← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 115

Sashe 113

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bar wurin, Layla ta ce musu. "Ku dai wallahi anyi surukan zamani kawai. Ku ba zaku girma bane? Ba uban ba ba surukinsa ba. Kai zo nan Sultan kyale su mana ka ci zamaninka kuma kace zaka ci na wani ko kaima Hamidah ta koya maka hali ne?" Ta fa a tana jan hannunshi, "Layla kyale ni, na ci mutuncinsa bai da mutuncin!" Har da wani kai duka a iska. Shima Ammar wani zabura yayi Sainah ta ja rigarshi. "Yan mata sake ni na kai mishi duka kamar yadda ya naushe ni a iska." "Papa na ne fa, taya za ayi ace baku samu daidaito a tsakaninku ba, fisabiilillahi." "Yarinya laifi ne don na so ki?" "Amma shi yayi farin ciki don kaso yarshi, kuma ya amince ya yarda kai mutum ne me matukar muhimmanci a gare shi, ba iya nan ba kaf duniya babu abin da zaka nima a gare shi ya hanaka, saboda yana kaunarka fisabiilillahi." Juyawa yayi yana kallon yadda take magana. "na sani kaf duniya bani da kamar Maina, ni ma.ina alfahari a tsayuwar da yayi domin rike matsayinsa na uban kirki, ya kuma san waye zai auri yarshi wannan ba sabon abu bane fadarmu ko a fada ne zamu yi!" Ya fada yana me nuna mata hanya suka wuce suna tafiya suna hira ko ina suka wuce sai gaisuwa ake kai musu.. har cikin gidan ya rakata, ya samu Maina yana shan tea. "Barka da hutawa Bab... Kai wallahi ba xan iya kiranka Baba ba domin." "Uncle me kyau kace mishi Papa kawai mana!" Juyawa yayi ya kalle ta ya kuma gyada kai. Yayi bakin shi yana rawa ya ce mishi. "Barka dai Papa!" Dauke kai Maina yayi. Layla ta ce mishi. "Sultan ba ka ji ana gaida kai ba ne?" Yadda tayi maganar yasa shi juyawa ya ce mishi. "Barka dai Yaro!" Yana hararan Ammar wanda yake mishi wani abu can. Haka Layla ta ja hannun Sainah ta barsu suka cinye kansu daga karshe aka manta da wancan aka shiga tattaunawa akan abin da ya shafi mulkin Baihak wanda shine abin da yake gabansu. Kallon Maina Ammar yayi kafin ya ce mishi. "Jiya mijin Jasy ya kira ni akan Aliyyah!" "Manta kawai muyi!" "Ni Yarka nake son aura, sannan itama yarinyar tana sona, amma ta roke ni alfarman na baka hakuri ka dawo da mahaifiyarsu. An dauki lokaci sosai tana son ko yayya ne ta ga mahaifiyarta a tare da kai. Bata rena iyawar Layla ba amma uwa ce ko yayya ne ana sonta a wuri ko mi muninta!" "Zan yi nazari!" "Allah yasa nazarin ya zama na alkhairi." Tunda suka yi wannan maganar basu kuma maganar da ya shafi Aliyyah, sai da Ammar ya kuma yiwa Layla magana ta saka baki ta ce mishi. "Ko kwana biyu da suka wuce Sanah tayi min magana nace tayi hakuri yanzu Babansu ne ya zama sai a hankali. Amma xan yi mishi magana!" "Haka ne domin nayi mamakin da Ummimi ta ce tayi mishi magana amma bai ce kome ba, haka ma Anna!" Shiru tayi kafin ta ce mishi. "ba damuwa zan duba lamarin, sannan kin ga yaki yayi magana akan bikin nadin sarautar nan fa!" Dariya tayi tana fa in. "Kyale shi ka kuma bawa Salahudeen hakuri abin da za ayi shine zan uzura mishi a saka bikinku akan lokaci ranar daurin aure sai ayi nadin sarautar." Girgiza kai Ammar yayi babu wanda yayi wannan tunanin baki aya sai ita, haka suka rabu koda dare yayi Maina yazo ya kwanta tana kallon shi ya janyota taki matsawa gare shi. "Laifin me nayi za ayi min h ukuncin da haka?" "Me yasa ba zaka dawo da inuwar gidanka ba?" "Inuwar da ta gujewa mai bukatarta inuwa ce a lokacin da mabukaci ya dibo rana da zafi kamata yayi ta zauna a tare da shi, me yasa Malik ya daura yardan shi akanki? Saboda bai ta a jin kin yi fada ko hayagagga akaina ba, macen da ta isa bata fada akan namiji sai dai namiji yayi fadar shi akanta domin kada wani ya ganta yace yana so. Ke rayuwata ce idan babu ke babu ni." Hawaye ne ya zubo mata. "Ka dawo da ita ina son shiga addinin Allah! Idan har zaka amshe ni a matsayin yar uwa a musulunci, ka dawo da ita don Allah!" Murmushi yayi kafin ya janyo ta yana shafa bayanta ya ce mata. "Na amshe ki na kuma amince ta dawo ai bani na kore ta ba ita ta kori kanta." "Na gode sosai!" Tai ta mishi godiya Wayyo wannan daren anyi shagali kamar me, kafin washi gari suka yi sallah asuba a tare, tana zaune a wurin tana addu'a har rana ta fito . Ya kalleta yana mamakin yadda take iya addu'a.."yaushe kika koya?" Kwantar da kanta tayi a kafadarshi, ta fara karanto Suratu fatiha zuwa nasi, sannan yayi mamakin yadda take karatu babu gargada. "Kina nufin duk lokacin da nake sallah kina saurarona!" Lumshe idanun yayi ya ce mata. "Me kike so?" "Islamiyya zaka bude mana ana karatu domin.har da jahilci yake damun matan Masarautar nan!" Ware idanu yayi yana zungure goshinta. "An gama Sultanah!" Bayan sun karya ya fita ta kira Ammar ta gaya mishi yadda suka yi, shi kuma ya gayawa Salahudeen, Salahudeen ya saka Ibrahim ya shirya a ranar ya tafi dauko Aliyyah. Duk da basu gayawa Maina abin da ta haifa ba, amma Ayrah ta turo mishi hoton yaron, shima sai ya share kamar bai wani sani ba. Kwanan Ibrahim biyu ya dawo da ita, bangaren Maman Ibrahim ta sauka Lady Hidaya wacce ta masifar sanyi kamar ba ita ba haka tayi ta hidima dasu, kwananta uku Lady Hidaya tace mata. "Tunda nake da Khamila ban tab'a jin tayi fada akanmu ba, duk da mun yi mata abubuwa dayawa, Yarinyar nan da kike fada akanta ta sauyawa mutane dayawa Rayuwa kada ki sake mu fahimci baki son zaman lafiya don Allah ki zauna lafiya da ita." "In sha Allah zan zauna lafiya!" "Ki kula sosai tana da mutunci da sanin ya kamata!" "Na gode Mamana!" Bayan sallah isha ta kaita bangaren Maina don ta ki kaita wurin Ummimi ta ce zata samu Ummimin, bayan ta musu nasiha sannan ta wuce bangaren Anna ta gaya mata yadda aka yi, ai kuwa tasha addu'a da godiya wurin Anna. Sannan ta wuce bangaren Ummimi sun tattauna karshe har dare yayi lokacin da mazan gidan suka shigo suka rakata bangarenta. "Mama ina Ibrahim ne?" "Yana can daki ya rufe kofa ina ga har yau yana tare da aljanar nan!" "Gara yayi hakuri don mu ba Malik ba ne da ya mishi alkawarin aurenta!" Dariya abin ya basu suka mata sallama. A can dakin Ibrahim, Rufaida ce zaune tana kuka. "Kayi hakuri babu alakar auren da zamu yi nasan haka Allah ya nufa ka ji ina sonka zan maka fatan alheri." Daga haka ta b'ace, har asuba bai fito ba, Maina yayi notice Bai ganshi ba, yayi magana duk suka nufi gidan. Anan suka samu Lady Hidaya tana ta buga kofar ya i budewa, bangaje kofar Maina yayi ya same shi zaune akan abin sallah yana kuka.."Me nene kuma?" "Yaya ina sonta! Amma tace mu hakura da juna babu aure a tsakaninmu!" Shafa kanshi yayi ya ce mishi. "za a fara akanta amma ka gaya mata su biyu zasu zauna da kai." Ya juya yana kallon Auta. "Wannan ya zama sirri a tsakaninmu, sannan Layla zata shiga maganar, domin ita tafi musu kusanci da su." Haka kuwa aka yi Layla ta shiga lamarin aka kai ruwa rana, sannan aka bar lamarin tsakaninsu, tow yace yana sonta iyayenta suka ja mata kunne ban da zalunci duk ta dauki kome nasu ne. A bangaren Aliyyah ta ga sauyin akan Yaranta, domin idan ka cire Sainah hatta sanah tana manne da Layla wani lokaci Layla take cewa su tafi wurin Mum su mata hira, ko tace a dauko mata Ammar domin sunan yaron kenan, ta goya shi duk da Aliyyah ta kasa sakewa amma rashin dawowan Yaranta ya dame ta, haka ta kira Jasy tana kuka Yaran sun ki sakewa da ita ta bata hakuri...... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/16, 10:12 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu _______80 Ba karamin damuwa ta sakawa ranta ba, domin Maina ya nuna mata wannan karon babu macen da zata raba mishi kan Yara, sannan ta kasa daina fitinar kanta akan Layla domin gani take kamar Layla ce ta hana Maina kulata, bata san Layla nata damuwar daban ba. Satin da biyu ta same shi a parlour shi da Layla. "Nazo wurinka ne!" Mikewa Layla tayi da Ammar da yayi barci zata fita ta ce mata. "Wadancan basu ishe ki ba ne sai kin hada da wanda ya rage min!" Sarai Layla ta fahimci rigima take nima cikin raha ta ce mata. "Ai ni burina ki ta haifawa Sultan Yara ina renonsu. Duk nawa ne " cikin fushi ta nufeta."Idan kin gama haukarki zaki iya tafiya don naga shi ya kawo ki!" Ya fada mata yana kallonta. Juyawa Layla tayi tana mamakin Aliyyah ba zata sauya ba wato. Haka ta wuce bangarenta, duk maganar da take yana jinta tana gamawa ya mike yana fa in. "Idan kin gama ki rufe kofar zan kwanta " ya bar ta nan, A hankali Aliyyah ta sakawa akanta fitinar Layla ta kwace mata Yara. Babu wanda ya bi ta kanta, karshe haka ta kange Sainah da kowa ga bikin da aka saka yana ta matsowa. Tunda aka fara rigimar Layla ko sau daya bata tab'a d'aga kai tayi magana ba. Wani bin kamar ta bata Yaranta wani bin ta tuna tana bar mata Yaran tarbiyyarsu sai a hankali,.haka suka ci gaba da rayuwa har bikin ya tawo saura kwanaki kamar ashirin, Layla ta fara wasu irin mafarki mara dadi, a hankali ta shiga ramewa. Tana jin wani abu yana damunta amma tarasa meye shi, ranar Haka ta shirya Yaran baki aya suka tafi wurin Jafar suka wuni bayan kwana biyu suka.tafi wagaduwada nan suka kwana sannan ta dawo dasu, Maina yayi tambayar duniyar nan ta kasa bashi amsa.
Chapter 113 · 0% Book details