Sashe 69
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce bata sani ba, sai dai ta duba hankalinta yana can kan bikin yar kawunta da za ayi. Ai kuwa lokacin da ta duba taga abin da yake faruwa dariya tayi ya daura da cewa. *Ikon Allah na kwance ya fadi yanzu fisabilillahi ko a zamanin Jahiliyya dai an bar wannan haukar balle a new era. Tow Allah ya kyauta Liyyah ina miki fatan alkhairi!* Tana ajiye posting din ta shiga kiran Aliyyah, wacce take can makale da miji ana ta cin uban sabada duk ruwan saman da ya kwaso wurin Layla nan yake watsa mata kamar an bude famfo. Abu aya ya kasa barin kanshi wani kuka da sautin Layla ya kasa barin kan shi, An dauki lokaci me tsawon gaske kafin ya kyaleta yana sauke ajiyar zuciya, ya hakura ne don gajiyar da ya hango tayi ba wai ya gaji ba ne saboda kanshi. Wanka yana tsaye abin ya faru yau ya dawo mishi, murmushi yayi har ya gama wanka ta ha a da alola, sannan ya fito daga ban dakin Jallabiya ya saka ya nufi hanyar waje, dakin Yaranshi ya nufa ya gyara musu kwanciya sannan ya musu addu'a ya dawo dakin ya samu Aliyyah tana ban daki. Gyara zama yayi yana kallon wayarshi,past one Layla kawai yake tunawa maganar gaskiya gidan ya mata girma. Shafa kanshi yayi yana nazarin abin yi. "Hot chocolate baka yi barci ba?" Kashe wayar yayi yana fa in. "Eh my heart,banyi barci ba so nake na kwanta!" Ya gyara kwanciyar shi da jan bargo. "Nazo na kwanta kusa da kai?" "Baki da matsala!" Da sauri ta saka rigar barci ta dawo gefenshi ta kwanta. Hira suka shiga yi a hankali har barci yayi gaba da shi don ita ke maganar shi kan zuciyarshi tana ga Layla. Har barci yayi gaba da shi. Itama barcin tayi. ----Baihak kura musu idanu Hamidah tayi tana jin duk abinda yake faruwa kamar har da rashin nasarar Falwa ta juya tana jin mutumin da yake mata bayanin, "Babu wata yarinyar da take tare da Maina, sannan yarinyar nanda kika ce a nimo miki ita, har yau babu labarinta. " Ajiye cup din hannunta tayi tana fa in. "Karya kenan! Ace lokaci guda a nima min abubuwa uku ta gagara! So kuke Malik ya mutu ne?" Ta fada da karfi domin zuwa yanzu jikin Malik ya fara bata tsoro. Duk wani abin da zai d'aga kafadar Malik abin ya ci tura,asalima tsoro da tashin hankali ta kara baibaye zuciyarta. Duk matan da Malik ya tara Hamidah bata yarda da kowa ba, sai Ummimi domin tasan ita daya ce bq zata iya cutar da shi ba, amma duk sauran tsoro suke bata, sau uku Abraham ya e shiga dakin Malik zai gauza sata, ana kama shi haka yasa tashin hankali da niman Mafita yasa Hamidah karaya. Sannan duk masarautar faman aikin tonon kabarin Rihanna ake tayi amma ba a samu ba,.haka yasa taji kamar rashin sa'a ya aureta. ---Washington. Shashekar kukan da yake ji yasa shi bude ido, haske ya hango a bakin kofar dakin ya mike a tsaye take tana rike da kofar kayan jikinta da yake hango yana zubar da jini yasa shi mikewa zubur ya bi bayanta da sauri. Tana tafiya yana bin ta sai da suka yi tafiya me nisa kafin suka isa bakin wani kofa a cikin masarautar Baihak. Bude kofar tayi sai ga Malik takure a wuri guda, kamar an daure shi. "Malik!" Ya furta kenan, ya bude Idanunshi. Tunda aka gaya mishi Malik bai da lafiya sai yau yaji tsoron kada Malik in ya mutu ne fa yayi, adaren yayi ta kiran Ammar amma bai same shi ba, don haka ya hakura gari na.wayewa daidai da agogon Baihak karfe biyu na asuba, ya kara kira basu dauka ba, idan hankalinsa yayi dubu ya tashi, duk da rashin jituwa da yake tsakaninsu amma Malik mahaifinsa ne bai.da ce ya watsar da shi haka ba, don haka bai bata lokaci ba gari na wayewa ya nufi office daga can,.ya kira Aliyyah ta shirya mishi kaya zai tafi Baihak. Daga office wurin Layla ya wuce ya samu ta tafi makaranta. Ya so bin ta can, sai ya ajiye mata duk abin da ya kawo mata, sannan ya rubuta mata short not ya tafi Baihak. Haka ya tafi, basu hadu ba. A can Airport Aliyyah da Yaranta biyu suka rakota, sai da ta ga tafiyarshi sannan suka dawo gidan. Wayarta ya fara ara, tana dauka Jasy ta dura mata zagi, murmushi tayi suka gama fadarsu, kafin ta gaya mata abin da yake faruwa wai dariya Aliyyah tayi daga nan ta hau IG, anan ta ga tashin hankali da ake yi abin har yaso ya bata dariya. Dariya ta saka tace *Ikon Allah! Mijina yana sona! Ina son shi Yana son Yarana yana sonmu baki aya laifine don na saka my lifeline! Maina Mijin Aliyyah ce ita daya kowa ma idan zai yi ihunsa ya gama Lafiya mijin Aliyyah Baban Hassanah da Husaina! Uban Nur da Banafsha! Muaaaaa My Man!* Aikuwa sai ga ruwan comments da likes ana ta turawa Aliyyah. Lokacin da Ayrah ta ga sakon kuka ta saka tare da kiran Hamidah da take can tana fama da nata damuwar, kafin wani lokaci ta hautsinawa Hamidah lissafi. A ranar Hamidah ta kira Ummimi ta gaya mata abin da Aliyyah take yi maza ta kira Ayrah ta bata hakuri sannan ta dauke handling social media inta. Murmushi Ummimi tayi tana fa in. "Ki kira Mijinta ki gaya mishi, zai fini iko da Matarshi tunda shi ya saya mata wayar ba ni ba."ai kamar ta jefe Ummimi a wuta domin bata zaci haka daga Ummimi ba. Haka tayi ta kiran Maina amma wayar taki shiga. Har bayan la'asar kafin taji labarin Maina ya iso shi tunda ya iso ya tafi wurin Ummimi bai kuma fita ba, domin da kwararrun likitocin Baihak ya ha a tafiyar suka zo aka rufa mishi. Har dare babu wani labari, dole haka suka tafi ba tare da an cimma abin da ake bukata ba. Washi gari a bangaren ya kwana, tun daren jiya ya yi mafarkin yadda zai fito da shi daga wannan karamin dakin, don haka ya nufi angaren Queen Hamidah. Tana zaune ta ci Uban kwalliya tana zuba izza. Zama yayi tare da daura kafa daya akan daya, yana kallonta. "Muhammad Maina!" "Hamidah!" Cike da takaici tare da mamaki take kallonshi. Juyawa tayi tana point din kanta bakinta ya gaza furta kalma ko aya. "Na zo na ga Jikin Malik ne, ki sake shi ya rayu lafiya, idan kika sake har na bar garin nan babu labarin Malik zan fasa kwai, sannan ki dakatar da yan iskan da kika saka suna bibiyar rayuwata idan ba haka ba zan fadawa mutanen Masarautar nan su san abinda kuke aikatawa!" Yana fa in haka ya mike ya kalli agogon hannunshi ya ce mata. "Awa biyu suka rage miki domin karfe hudu zan bar garin nan yanzu kuwa karfe daya ne!" Sake baki tayi tana kallon Maina da ya kashe ta da mamaki haka ta bar parlourn, kai duk Jarabar da taso mishi kasawa tayi har ya bar gidan, mikewa tayi ta fara Safa da Marwa, can ganin haka ba zai ficeta ba ta juya zuwa akinta. Bude wani kaje tayi sai ga wani katon zakara, a kwance kamar matacce, tana bu e shi ya tashi ya fita da gudu ya kuwa buga chara me karfin gaske sai da masarautar ya amsa. Maina yana isa wurin Ummimi Idanunshi yana kan Malik da yake kwance sai computer da yake aiki akanshi, "zan tafi an jima in sha Allah zai farka, sannan kina yawaita mishi alola, akwai kariya a haka." arar da computer din suka yi yasa Maina ya isa kanshi tare da kiran Nurse da take wajen aka fara duba shi. Sai wajen karfe uku ya koma sannan Maina yayiwa Ummimi sallama ta da uko abubuwan tab'awa da ta hada mishi ta ce mishi. "Ga na Aliyyah da Yaranta, wannan na Layla ce!" Sannan ta gaya masa abin da ya faru tsakanin Ayrah da Aliyyah. Murmushi yayi yana fa in. "basu gajiya da rigima ita tana can tana gantali ta bar Malik in anan!" Murmusa mishi Ummimi tayi, ya mata sallama ya tafi, bai gayawa Aliyyah ya taso ba, don zata iya zuwa aukar shi, shi kuma yayi kewar Layla so yake ya ganta. Haka suka bar Baihak. Jirginsu na barin Baihak Malik yana farkawa, yana kwance lumo kamar me nazari, kafin ya juya yana kallon Ummimi da take azkar. "Khamilah! Muhammad yazo ne?" Juyawa tayi tana kallonshi bakinta dauke da Alhamdulillahi ta ce mishi. "Dazun ya bar garin nan!" "Me yasa bai jira na farka ba!" "Tow kayi hakuri zai zo idan yara suka yi hutu." Shiru yayi yana kallon sama. A can kuwa Layla ta tara kawayenta suna ta shagali sai rawa ake anata cinye cinye, gidan yayi kaca-kaca, abinci kuwa an yi wasa da shi babu iyaka ga barna da aka yi wai anyi cake anyi chocolate, anyi candy. Babu barnan da ba ayi ba, pizza da chicken nuggets anyi barnan shi ko ina kaca-kaca, sai raye-raye suka abinsu. Har karfe shida na yamma suka wuce makaranta, ita daya aka bari a gidan shafa wuyarta tayi sai ga wasu yan mata ta kalle su tana fa in. "Gidan yayi kaca-kaca!" "An gama.ranki shi da e" daki ta dawo tayi wanka ta shiga zazzage kayan da Deenah ta saya mata,wai ya mata kyau ne ta saya mata. Dariya tayi pant ne da wasu abubuwan, hakq, wanka tayi ta fito tana saka kayan tana kallon kanta a madubi. Tana gamawa ta juya zuwa gado ta kwanta. Tun tana hiranta da yan wake-wake har barci yayi gaba da ita, karfe bakwai ya dira a gidan, tana ta barci lokacin da ya shiga dakin, mutuwar tsaye yayi yana mamakin Layla da yadda ta kwanta. [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _______________41 Tab'a goshinta yayi yaji ko zazza i nema jikinta sai dai kash, babu al'amar akwai ciwo a jikinta asalima lafiya lau. Sauke ajiyar zuciya yayi ya fito waje, yana kallon security din gidan ya ce musu."me ya faru?" "Babu kome yallabai