← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 115

Sashe 110

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

uku tsakani sai ga Yaran har da Sanah da take kan keken marasa lafiya. Wannan abin bai wa Maina dadi ba, amma ya saka a ranshi haka Allah ya nufa ya kuma kaddara rayuwarshi zata fuskanci haka.. Tunda suka zo Haeda take hidima dasu, Yaran dake sauran suna da hankali babu matsala, Sanah ce Layla ta tsaya akanta ta fara mata jinya wanda ya saka a cikin sati guda ta fara warwarewa. Amma haka bai tab'a saka yarinyar nan ta duba Layla a matsayin wacce take kula da ita ba, sai ma kara mata kallon reni take, ita Layla bata damu da iskancinta ba, kwanakin su arba'in daidai aka kirata zuwa Fadar Baihak a ranar ta shirya ganin Queen Hamidah domin ta rantse sai ta saka matar tayi kaskantacciyar rayuwa, tunda Maina yaji sakon kiran Layla ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya shigo dakin ya kai sau goma yana tambayarta me zata fada a fadar me take tunanin zai faru. Kai Baki aya hankalinsa a tashe yake duk ya shiga damuwa, tana shiryawa ta riko hannunshi suka tafi dakinshi ta hada mishi ruwan wanka yana zaune ta zo ta riko hannunshi ta tura shi tana fa in. "Kayi wanka kaji!" Haka ya shiga ban daki tana jin shiru ta buga mishi kofa da sauri yayi wankar ya fito ita kuma ta taimaka mishi ya shirya baki aya ya zabge kallonshi take tana jin zafin abin da suka mishi. Murmushin mugunta tayi ta ce mishi. "Mai martaba da kanshi daga yau ni ce zan na shirya Mai martaba na." Jan hancinta yayi ya rungume ta ta baya yana fa in. "Kin sani ina jin kwarin gwiwa sosai kin sa ina jin kamar Ni cikakken namiji ne da zai iya tunkarar maza a filin ya Dariya tayi tana fa in. "Daren yau naka ne jarumin maza sannan kayi yadda ake so Allah yana tare da kai. Kafin na shiga addinin Allah zan yi kuskure daya ban sani ba ko Allah zai kama ni da laifin amma don kawo karshen miyagun cikin al'umma nake son nayi wannan kasadar." ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/14, 8:08 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________77 D'ago kanta yayi ya ce mata. "Indai a kaina ne zaki yi kuskure na yafe miki domin bana son hannunki ya kasance cikin jini na yarda da addarata amma ban yarda ni ba jinin Malik ba ne." Ya fada yana kallon kwayar idanunta. Janye hannunsa tayi tana fa in. "Ai fa kada mu makara domin akwai yiwuwar a samu cunkoson ababen hawa." Ta fada tare da barin gabanshi. "Layla!" "Na'am!" "Idan nace miki na fasa zuwa fadar Baihak ba zaki ji zafi ba?" Girgixa mishi kai tayi taki kallonshi. "Tow na hakura da zuwa fadar su yi yadda suke so!" Ya zauna yana alle botirin rigarshi. _Zaki yi hakuri sosai domin kuwa zai ta gudun addaranshi! Ki bi a hankali kome zai zo da sauki!_ fita tayi daga dakin tunda haka ya faru Malik ya fado mata a rai tana tafiya kalamanshi suna dawo mata. _Kiyi hakuri zai ta baki wahala saboda bai saba ba, asalima gudun kada idanun mahara ya fada kanshi na janye shi daga jikina_ hawayen da take dannewa ne ya zubo mata, har ta haura sama ta samu Sanah ta b'ata jikinta wani lokaci kuma gayya take b'ata jikinta yau da tayi dace mutanen na kusa wata irin tsawa ta buga mata sai da ta mike akan kafarta ta nuna mata ban daki tare da wheelchair din. Da sauri ta tura kenan ta wanke jikinta har lokacin jikinta bai daina rawa ba. Domin tsawar har cikin ranta ya shiga ya kuma cusa mata wani tsoron Layla. Tana fitowa ta samu Layla tana tsaye. "daga yau jinya ya kare aikin dakinku kula da kannenki ya koma kanki, sannan zamuna shiga kitchen dake idan kuma kika sake wani renin hankalin ya shiga tsakanin" tafa hannunta tayi sai gasu a daji me ban tsoro. "Anan zan barki har abada sai ki zab'a." Ashe da tsoron karya taji na yanzu ganinta a wani irin guri me ban tsoro yasa baki aya yarinyar nan kamar zata mutu, sake tafa hannunta tayi suka dawo dakin, jikinta yana rawa ta fara aikin dakin har Layla ta fita ta kawo mata abin turaren wuta ta bar dakin. Wurin Yaranta ta nufa ta samu Haeda tana kula da su. Sai lokacin kuka ya zo mata, Haeda bata damu ta tambaye ta ba, domin tasan tsakaninsu ne, haka tayi kukanta ta koshi sannan ya kalli Malika tana ta barci Malik ne yake ta yan kananun rikici. "Naana me ya same shi?" "Kawai yana ta rikici ne!" Kai hannu tayi zata dauke shi ta ga idanun yaron ya koma grey colour! Zungure goshinsa tayi tana fa in. "Oya wuce ki futa." A hankali hayaki ta fita ta hancin Yaron, daukar shi tayi ta rab'a a kafadarta, ta kuma dauki yar uwar ta fita da su. Wurin Maina ta kai su, yana inda ta barsu ta ajiye su tana fa in. "Ni ban iya kula da wasu abubuwan ba, idan nace zan yi zan sake aikata kuskure ko zaka taimaka kayi musu azkar wanda kake min da can baya!" Daukar Malik yayi ta mishi addu'ar sannan ya kuma aukar Malika yayi mata. "Nayi musu!" Daukarsu tayi zata fita ya ce mata. "Dawo dasu ki kwantar da su anan!" "Zanje nayi barci ne!" "Zo kiyi anan!" "A'a!" "Yaushe kika fara musu!" Kwantar da su tayi a hankali sannan ta koma gefenshi ta zauna. "Nasan ban kyauta ba, amma haka baya nufin ayi abandoned dina ba ne, nasan akwai dalilinki naso muje fada amma kuma ni bana da ra'ayin mulkin zan iya mutuwa idan na taka fadar Baihak, yanzu haka yadda nake kiran sunan ji nake kamar na yanke harshe a please i need your help!" Ya fada yana rike hannunta. Idanunta ne ya cika da kwalla. _Layla zasu yi me yiwa kada ya shigo gidan nasan sun waye a tare da ni, nasan dalilin zamansu a tare da ni, ki taimaka Maina ya tsaya da kanshi._ "Ki kwanta!" Girgiza kai tayi tana matsawa gefen shi. "Kwanta na ga kamar kana jin barci!" Kwanciya yayi ta shiga jikinshi ta kwanta numfashinsu.yana haduwa da juna kura mata idanun yayi kafin ya ce mata. "Tun ina Yaro bana son tashin hankali, sannan har girmana bana son tashin hankali, sun rike Ummimi a ciki da sauran Yan uwana, bana jin dadi sai nake jin kamar ni daya kawai aka halitta." Sake tura kanta tayi cikin rigarshi. "Ba kai ka ai kake cikin maraici da kewa ba, suma rayuwarka ake musu barazana da shi. Shi yasa naso muje su ganka ko ita Ummimi ce hankalinta ya kwanta kace a'a." "Layla ina jin tsoron kada wani abu ya same miki!" "Idan kuma yana cikin addarata babu yadda na iya don haka ka daina damun kanka da cewa kana gudun kada wani abu ya same ni!" Kwanciya suka cigaba da yi zuciyarsu tana bugawa da sauri da sauri. *** A gaban bishiyar adu'a take tana kallon kabarin Sanaya. Hawaye ke zuba mata domin bata kawo a ranta saboda tayi niyyar cutar da Layla Sanayah zata mutu ba, don haka cikin zafin rai ta karya wani reshe me karfi ta shiga gyarawa tana fa in. "Tunda kika kashe min jikata, sai na rama abin da kika min sai na tabbatar da cewa kema kin mutu." Ta fada tana gyara itaccen. "Me yasa ba zaki bar zuciyarki ta huta da hassada ba!" Inji wani mutum da yazo wucewa. Juyawa tayi tana kokarin fadar magana ta ga tsohon bokon da ya cire mata takunkumin da aka saka na wagaduwada. "Shugaba!" Ta fada da sauri tana kuka. "Ki hakura da yarinyar nan domin mutuwarki ce ita idan kika dage zata shafe Tarihinki!" Dariya tayi tana fa in "shugaba koda nayi rauni ban rasa zuciyata ba , sai na rama." "Zaki rame domin yarinyar tana da masu kula da ita kowa yana zagaye da ita." Kuka ta saka tana ihu sai ta rama ba zata yafe ba haka ya tafi ya barta nan tana ihu da birgima. Kafin ta mike tana murmushi. "Sanayah tayi miki rantsuwa da kakannina sai na kawo miki kan Layla na ajiye miki saman kabarinki!" Sannan ta wuce ta bar wurin. A hankali ta bu e idanunta tana kallon yadda yake barci, sake kwantar da kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya yau tana jin kamar tafi shi kewa. Sannan gumurzun da suka sha ba na wasa ba ne, shafa kumatunshi tayi tana jin shi har cikin ranta, Maina nata ne ita aya no matter how ba zata tab'a barin shi ba zata tsaya koda haka zai saka ta biya farashinsa da rayuwarta zata yi domin ya zama nata har abada. Sumbatar bakinshi tayi tana kallon yadda ya sake murmushi. "Zaka yi barci ne ko sai na sake cinyeka!" Sake rungumar ta yayi tsam ya cigaba da sauke ajiyar zuciya. Itama barci yayi gaba da ita. Cikin bakinciki Maman Jasy take kallon Aliyyah, kafin tayi murmushi tana fa in. "Allah ya sauke ki lafiya!" "Kamar ya Maman Jasy? A wannan yanayin da Mijinta yake bukatar macen da zata tsaya mishi yarinyar nan ta kwaso kafa ta dawo gida? Haba don Allah me kike son zama ne Aliyyah? Shi kenan dama ita yarinyar da kike ihu akanta dama Allah yana bamu chance sai daya ne ita kuma Allah ya bata tun bata kai haka ba, a yanxu da takai Alhamdulillahi gara da jahilin kwakwalwarki ya dawo dake gida." Murmushin takaici Mamanta tayi sannan ta wuce basu kuma tanka mata ba, koda Jasy ta san tana gari amma bata yarda ta je gidan ba, lokacin da Ayrah ta ji labarin tana gari kamar zata yi kuka haka ta zo ta sakata a gaba da magana. "Ashe ke karamar jahila ce? Taya zaki bar Mijinki da da can da kike haihuwar a gaban Uban waye kike haihuwar, ke dai kin yi asara mara amfani. Kin barwa kishiya Mijinki da Yaranki kin dawo nan Allah ya baki sa'a ya sako ki sai kin yadda zaki yi." A karshe ita ko
Chapter 110 · 0% Book details