← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 115

Sashe 43

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* ______________________ __________________22 Barcin da bai ci karfinta ba, yasa ta bu e idanunta tana kallon Nuri darling da take ta haki hanci da baki, ta tashi zaune tana d'agota. "Nur!" Ta kira sunanta, ingijeta Sanah tayi tana watsa mata harara. "Banza yar kauye!" Ta nufi Nur din, tana me d'agota. Amma yarinyar da take ya in niman numfashinta ta sume baki aya, "Papa!" Ture hannunta Layla tayi ta auke ta, suka fitada ita. "Dalla bani kanwata!" Layla kamar zata yi kuka ta ce mata. "ki kyale ni!" Ta fita da gudu, da gudu ta bi Layla tare da jan rigarta ta baya, sai da suka fadi ita da Nuri darling. "I say hate you, bani kanwata mayya me witch eyes." Ta fada tare da lacce Layla da kafa, ta dauki Nuriyya ta nufi dakin part din Babansu da ita, "Sanah ki sakata a kafada!" Ya fada hawaye na zuba mata, juyawa Sanah tayi tana fa in. "Idan naki fa? Dole ki bar mana gidanmu naga lokacin da kike shake Nur din ai!" Wani irin abu ne ya taso daga sarkan Layla tayi maza ta rike sarkan, Sanah ta cigaba da tafiyarta, ita ta tsani Layla bata son zamanta a gidan. Layla ba alkhairi ba ce a gidansu gara ta bar gidan, duk da haka Layla bata sare ba, ta bita har kofar Maina yadda Sanah take buga kofar yasa duk iyayen suka fito, tana jin suna bude kofar ta tura kai da sauri, tana fa in. "Papa ky rufe kofar zata kashe mu!" Hango layla yadda da take rakube a can gefe, "Papan Twins duba don Allah!" Da sauri ya juya yaga Yarinyar bata numfashin, a daidai lokacin Layla ta leko, rufe kofar dakin Sanah tayi. Haka suka fito daga dakin baki aya suka nufi waje, karo na biyu da ya kalleta anan ya lura da gefen bakinta a fashe, haka ya tafi yana mamakin yadda aka yi bakinta ya fashe, koda suka isa asibitin a gaggauce aka amshi Nur din Sanah sai kuka take tana fa awa Aliyah. "Mum shaketa tayi fa!" Shiru Aliyah tayi domin ta ji bata gamsu da hakan ba, Layla da Nuri darling ko su yan uwanta basu nunawa Layla tattalin Nur din ba, wasa wasa tun karfe sha biyu na dare suke wurin har aka kira sallah asuba, kafin aka fito da Nur aka maida ta dakin da zata zauna, hancinta sakale da bututun zukar numfashi. "Sanah muje, Aliyyah zan dawo!" Haka suka tawo gida, dake gari bai gama sha ba, inda suka barta da zasu tafi tana tsaye a wurin, wani abu ne ya daki zuciyarshi, a karon farko da yaji haka akan abin da Layla tayi, Scotland tana cikin jerin kasashen da suke da bala'in sanyi, domin har da dusar ara suke dashi, don haka yayi mamaki da al'ajabin ganinta a wurin tun tafiyarsu. Fitowa Sanah tayi ta hangota ganin har lokacin tana wurin tana zuwa ta bangaje ta, sai da ta fadi kasa. "Kiyi hakuri, princess Sanah!" Tsaki tayi ta wuce ta, yana kallonsu bai ji dadi ba sam amma sai ya share kamar bai gani ba, ya tawo har lokacin tana wurin shi da zai wuce ta ce mishi. "Ranka ya da e, ya jikin Nuri darling!" "Da sauki!" A hankali ta sake wanu marayan kuka, wanda ya sashi dole ya tsaya shi bai wuce ba, sai koma ba yana tsaye yana jin yadda take kukan, haka ya saka kai ya wuce, bai tsaya ba domin zuciyarshi tana wani irin bugawa ne a duk dakika yana jin kamar numfashinsa zai bar kirjinsa, kamar me Ashma haka ya wuce cikin gidanshi. Koda ya shiga ciki bai tsaya ba ban daki ya shiga yayi Alola yana jan numfashi. Ya fito yayi sallah yasan Auta yana tare da Malik, gari na wayewa ya wuce ya gayawa Ummimi ita da Bahi suka shirya abin karyawa, anan Sainah take tambayarsu. "Papa me ya samu Didin Nuri darling? Bakinta ya fashe tana kwance wai bata da lafiya." Yana jin su amma bai ce kome ba, Ummimi da Bahiyyah ne suka fara mikewa suka shiga suka samu tana kwance rike da cikinta. "subhanalillahi Layla meke damunki?" Bude idanu tayi da kyar tana murmushi, ta ce musu. " Da sauki fa!" Tab'a kanta Ummimi tayi yayi zafi rau,"Ya Salam ke gayawa Maina a kaita asibitin itama!" "A'a na warke fa." "Dole a kai ki asibiti fa, idan baso kike Hajja ta cinye ni danye ba." Kasa mikewa tayi domin maranta da ya kulle, dole Bahiyyah ta d'agata, suka fita yana gyara wuyar rigarshi. Haka suka fita har da ita sai da ya ajiye su Sanah a makaranta, sannan aka wuce da ita asibitin, kafin su isa ta birkice musu, domin maranta ne ya kulle da mugun ciwo, suna shiga itama aka amsheta, few minutes sai ga wani likita ya zo ya wuce dakinta, a hoton da suka mata suka fahimci sukar da aka mata a cikinta, ya matso mata da hailarta. Wanda ba wani abu bane, don akwai yaran da basu kaita ba ma suna yi, sai da aka mata allura ta samu barci, shi kan sa tsaya ba dakin din Nur ya nufa, da basket zuwa yanzu ya gaji da dawainiyyar da yake wallahi. Ji yake kamar ya maida Iyalinshi bakidaya Baihak ya huta. Amma gubar da yake Baihak yafi wanda yake ciki illa. Sai da ya gama ganinsu, sannan ya fita ya nufi office din likitan da ya duba Nur din, yaji bayanin ciwon, sannan ya nufi na Layla yaji bayanin kome, kallon agogon hannunshi ya yi, sannan ya ciro wayarshi yayi sittings din calendar, sannan ya fita ya sauke wani mobil apps na My date, sannan ya tashi kamar yadda likitan ya shawarce shi ya saka idanu akanta, domin irin wannan yanayin tana gamawa zata shiga kwanakin da zata bukaci namiji, idan har akwai matsala dole ya bata freedom ta fita tayi zina don haka ne zai saka ta nutsuwa. Watsa mishi harara yayi ya ce mishi. "kai baka ji kunya yarinya yar shekaru sha hudu zan bawa Freedom bayan addinina da addinin Kirista sun haramta zina?" Sai mutumin ya shiga zare idanu. "haka ne kuma tow shi kenan!" Mikewa yayi ya fita ya sayo mata magungunan ya kai dakin, kafin ya wuce zai tafi office a bakin kofar ya hadu da Auta da ya zo shima."Yasu Nur din da jiki?" "Da sauki!" Ya fada a gaggauce ya bar asibitin. Haka ya wuce ya duba su, sannan ya koma dakin Layla da yaji labarin a bakin Bahi ita ce ma a tare da ita, tan barci. "Ya jikinta?" "Da sauki!" Bayan kamar minti ashirin aka shigo da wani kaya a box anyi refen dinsa, Pink ne mika musu me kawo kayan yayi ya mikawa Bahi, kallon Auta tayi ta saka hannu ta amsa, tayi sign. A saman ledar an rubuta *LAYLA* can asar rubutun ta ga rubutu bata maida hankali ba, ta bude ledar kwalin baki aya pant ne kala goma sha biyu pink and peach colour. Kwalin sanitary pads, shima ledarshi pink. Sai yamma likis ta farka lokacin har Ummimi ta kuma kawo musu abincin rana, tashin da zata yi ne jini ya gangaro mata, kallon Bahi tayi jikinta ya dauki wani irin rawa, "ke ba kome ba wani abu ne, tukun na ma waye ya buge ki a cikinki?" Ware idanu tayi tana son tambayarta wani abu ne, amma ta kasa tambayarta. "Da sauki da ace wani abu ne ya faru ai da." "Ciki na ne ya fashe?" Abin sai da yaso bawa Bahiyyah dariya ta ce mata. "A'a kawai ba kome ki kula da kyau!" Ya rakata ban daki tayi wanka ta gyara jikinta ta nuna mata yadda zata saka pant din da pad din. Haka kuwa tayi ta zo ta dan ci abincin, sai lokacin Aliyyah dasu Sainah suka zo. "Didi da Nuri darling ana ciwon kauna!" Inji Aliyyah tana murmushi, sunkuyar da kai tayi tana fa in. "Ranki shi da e ya jikinta?" "Da sauki!" Gyada kai, tana mata fatan sauki. Haka dai suka yi ta an riritatta kafin dare aka sallameta da tulin magani, a hanyar su ta komawa gida ne, Bahiyyah take bawa Maina shawarar saka Layla a makaranta, bai ce kome ba amma kuma yayi na'am da shawaran Bahi din, don haka ya ce mata dai duba. Haka suka dawo magani ta sha ta kwanta a dakin Bahi, domin tasan domin Nur take shiga akinsu, yanzu kuma bata nan don haka ta dawo akinsu ta cigaba da kwanciya, a kwanakin da tayi a gida Bahi ta masifar saka idanu akanta, domin ko Washi garin ranar da suke dawo ya gaya mata abin da likita ya fa a akanta, don haka Bahi itama tayi masa maganar ya nima mata kayan canza domin kayanta baki aya uniform ne, haka yasa shi bata kudi me yawa ta saya mata kayan sawa. Don a tare suka fita, da Bahi take gayawa mata girma da illar halin da take ciki,. Muslunce, sai da zuciyarta ya kad'a amma dake bata san kome ba a duniyarta tsafi ta sani da abin da yake cikin tsafin, sai bata ji wani sha'awar rayuwar addinin Musuluncin da take mata tayin shi a fakaice ba , burinta ta shiga jikin zuri'ar Malik ta rama abin da ake mata, a shirye take ta ga me kyau ko mara kyau, ta shirya ganin bakinciki ko farinciki ba zata tab'a gajiya ba, ko sarewa ba. Sati biyu da suka biyo bayan zata ce da sauki domin Nur itama an dawo da ita, yau ya kasance Monday, tun jiya Bahi ta ce ta shirya da wuri. Tunda ta je ta gyara wurin kwanciyar Nur ta mata wanka ta sa mata kaya, sannan ta bata abinci da magani har lokacin tana tare da abin numfashin. "Didi Papa yace yau zaki fara zuwa school!" Ware idanu tayi. "Me?" Murmusa mata Nur tayi tare da bude mata hannu
Chapter 43 · 0% Book details