← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 115

Sashe 103

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

je da suka kawowa Kalfana hari? Ka ji tsoro ka gudu ka bar yarinyar da ta zabe ka sama.da iyayenta? Ka gudu ka bar yarinyar da ka rabata da kowa nata. Yau gani a jikin Yarka da Zafir ya kare ya kuma boye ta. Malik Zafir ya gaya maka zata zo, ba ita aya ba tare da rundunarta. Kasan su waye rundunar? Ni da sauran dangi gamu nan jikin Layla zata biya bashi a bisa laifin da wasu suka aikata. Gaya min akwai kuskure anan." "Tabbas akwai kuskure, kun yi kuskure, mafi girma da kuskuren da kuka aikata shine na saka Layla cikin abin da bata san mafarinsa ba, Layla bata yi kome ba, Layla bata da laifi idan akwai wanda ya cancanci hukunci nan ne!" Inji Malik ya tako har gabanta. "Ni ne mai laifi ni nayi kuskure ku bar jikin Layla ku dauki jikina na amince!" "A'a koda wasa ba zamu koma jikin ka ba, nan dai ya fi dacewa da mu, nan yafi arfi da samar mana nutsuwa nan zamu zauna har karshen rayuwarta muna nan!" "Ku yi mata adalci!" Maina ya fa a. Amma ina gyara kwanciya tayi tana tauna wani abu kafin ta furza. "Ni bana yafiya, bana mantuwa kuma bana yafe duk wanda ya min laifi. Hukuncin daya ne kawai " daga haka tayi shiru bata kuma magana ba, hankalin kowa ya tashi musamman yadda Layla take dadda komawa akwai tashin hankali lamarin, haka aka sallame Sanah wacce itama ta komawa Uwarta aiki kamar me bata iya kome sai an mata. Sannan tun wannan ranar da suka yi magana basu kara tari ba, A can asibiti kuwa da aka Queen Hamidah azabar da take sha, yasa da kafarta ta gudo daga asibitin ta dawo gida a gidan ma can cikin wardrobe dinta, ta shige domin masifar da take gani ya wuce tunaninta kuma bakinta baya iya furta ko kalma daya sai dai tace "a rufe ni zasu kashe ni." Duk wanda yasan Masarautar a shekaru arba'in baya yau ya ga masarautar Baihak a halin da take ciki yasan haske ya fara bayanan a bayan duhun da ya lullube ta. Duk yadda Tirsila taso ganin ta kare kanta, haka bai faru ba domin kuwa Layla ta dirka mata lokacin Sanaya bata nan, murmushi tayi mata sannan ta ce mata. "Na ce ko gudu amma kinki ji." "Ke Layla ki fita min a gida.!" "Kece kika kira ni zatonki sai naki zuwa?" "Gaya min gani nan!" "Ki tafi ke ba Layla ba ce!" "Tabbas ni ba ita bace dama na gaya maku zan zo amma ban gaya muku yadda zan zo ba,. nice ba Layla ba ita tana can da jikina. Ni kuma nazo nan da wani jikin." Dauko sandar tsafi tayi tana nunawa Layla. Yatsa Layla ta nuna mata. "Ba zan kashe ki ba, sai dai zan barki ne domin bakin ciki ya kashe ki don haka shi wukar da kika ajiye zai miki amfani nan gaba ka an kuma ba zan miki wani abu ba amma nasan shirina ba zai tab'a wargajewa ba kina da sauran lokaci imma ki gudu nace kin ji tsorona, imma ki tsaya na cigaba da ganinki cikin fargaba da abin zai faru wanda baki san shi ba. Ni daya ce na sanshi na kuma san makomarki!" Daga haka ta b'ace ajiyar zuciya Tirsila ta sauke tana fa in. "Ya wuce ta ce zata mai dani wagaduwada, tunda ba xata kashe ni ba." Tana wannan surutun Sanaya ta shigo. Shakar iska tayi ta ce mata. "Layla tazo ne?" Fashewa da kuka Tirsila tayi tana fa in. "Ta zo kai, ta ce sai ta ga bayana." Girgiza kai Sanaya tayi tana fa in. "Ba laifi tunda fansa zata dauka akan abin da aka mata ba laifi ai!" "Kina bayanta ne?" "Eh mana ina bayanta lokacin da nace kada ki biye musu ai baki ji ba." "Sanaya ni fa kakarki ce." "Haka kika kashe mata kakarta, sannan kika cusa mata bakinciki kina tsammanin hakki zai kyale ki ne? Don haka ki fuskanci ukubar da kika tanadawa kanki!" "Haka ma zaki ce!" "Me zance bayan haka? Tunda abu ne da kece silar faruwarsa! Tun da kika iya cefanar da Al'ummarki na gano baki bukatar wani a gefenki kiyi yadda kike so." Daga haka ta barta a wurin baki sake. Abu kamar wasa ciwon Layla ya ara arfi, yayinda Queen Hamidah take kara firgicewa da razana, haka yasa baki aya kome ya tsayawa Maina da Malik, ga Auta da babu labarin su shi da Ibrahim. Sai da aka samu shudewan sati uku kafin, Allah ya dawo dasu cikin aminci da salama, tunda Malik ya gansu yaji sauran damuwarshi ya ragu, cikin masifa da zafin kai Abraham ya cewa Malik. "Wannan yaron irinsu ne saboda mugun nufinsa ko ya shiga Aljanna sai an koro shi, Malik kaga yan mata tsala-tsala amma yaron nan ya saka ni a gaba wai sai an dawo damu!" "Ka kasa fahimta, Yan matan da kake gani aljanu." "Yo ina ruwana? Kawai son Rufaida nake!" "Allah ya shirya ka!" "Kai na rantse sai ka mai dani duniyar nan domin fa bar abina a can!" "Babu abun da ka bari!" "Wallahi na bar rayuwata na barwa Rufaida." "Abraham baka da hankali!" Murmushi Malik yake yana kallon yadda suke fada, a da can ko ga maciji basu yi amma a yau wani irin shakuwa da kaunar juna suke murmushi yayi hawaye na zuba musu ya cewa Auta. "Ita Rufaidar yar waye?" "Jikar Sarkin Malaman kisra ce, Abba aljana ce fa!" "Yana sonta ne kuma tunda ya fadi haka tabbas zai zauna da ita, Allah Sarki Halifa!" Ya fada hawaye na zuba mishi, kafin ya basu labarin rashin lafiyar Layla. Mikewa Auta yayi yana fa in. "Kuma tana cikin gidan nan?" "Eh tana nan a bangarensu." "Taso muje Abraham!" Tashi yayi suka nufi bangaren, lokacin da suka isa sun samu an saka mata na'ura ne sai daure ta da aka yi. "Me yasa aka daure ta." "Saboda tana kokarin cutar da Malik da Maina ne. Inji Doctor Jafar. Riko hannun Maina Auta yayi ya shigar da shi cikin dakin ya ce ya zauna a bakin gadon shi kuma ya durkusa yana kallonta. Kunce hannunta yayi yana me riko hannunta ya daura kan na Maina. Juyawa tayi ta kalle shi. "Kin tuna shi?" Ya tambaye ta. "Muhammad Hatim inki ne! Wanda kike tare dashi kodayaushe, kada ki tafi da nisa yana tare dake, tun fil azal bai cutar dake ba, Layla nasan kina jina kada ki sake kiyi wani abu Muhammad Hatim yana sonki gashi a tare dake kuma zai yi kome domin ki, shi din mallakanki ne ki dawo gare shi. " Yana gama fadar haka ya mike ya bar dakin. Ya tsaya a bakin kofar yana kallonsu. Hannunta cikin nashi abubuwan da suka faru a Scotland ya dawo mata, a hankali ta ce mishi. "Papa, Sultan dina!" Tana furta haka jikinta ya kuma rikicewa tare da kai hannu ta shake wuyar Maina. "Me yasa aka haife ka da fuskarshi? Sai na kashe ka" ta fada da karfi. "Kada ka damu ka tsaya ba zata iya kashe ka ba, ai Layla tana sonka! Ba zaki iya kome ba, shi din rayuwarsa ta Layla ce. Ba zaki kuskuren Salahudeen ba shi zai shafi miliyoyin zuri'a ba, kun kashe iya sarakunan da suka muku, Muhammad Hatim ba zai kasu ba ai shi ba sarki bane!" Sake wuyar Maina tayi tana murmushi kafin ta ce mishi. "Tawo nan dan baiwa!" Tana dariya domin tasan kanta a hankali ta ce mishi. "Har yau kana son Laylan ce......... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/5, 5:27 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________71 "Ki zo ga jikina ko shiga," Malik ya fada mata yana son ta bar tuhumar Auta, zuwa yanzu yafi son zaman lafiyar Yaransa da juna sama da kome, girgiza kai tayi tana fa in. "Me zan yi da gangan jikinka Malik? Ni fa ko da nake nan ba zan iya zama cikin zunubi ba, jikin Layla shine daidai da lissafina, domin tazo a lokacin da na rasa kome na a daren bakar addara! Don haka ba kowa yake da sa'a irin nata ba! Sai yar baiwa me tare da ruhin Ruhainai!" Ta fada tana mikewa zaune, yana rike da hannunta cikin kulawa yana shafawa. "Nasan tunda kika bukaci Layla tabbas laifinmu babba ne, ba ina yi don ki fita ba." D'ago kai tayi tana kallon shi da mamaki. Murmushi yayi kafin ya ce mata. "Ni nafi son ki cigaba da zama a anan. Sama da ki fita ki bar Layla zamanki jikin Layla shine xai samar mata da kariya!" Daga haka ya mike zai fita ta ce mishi. "Maganarka bai yi tasiri a kaina ba na gaya maka, ba zai tab'a lalata min lissafina ba!" Ta fada tana murmushi ta tashi zaune tana kallonsu baki aya. "Duk akan Layla kuke jin tashin hankali! Tow ya kenan idan na kashe ta? Zan fita na wani lokaci kuyi bankwana da ita sannan ka sani ba ta shigo rayuwarku ba ne don zama matarka ta zo ne rufe tarihin Baihak." Murmushi tayi sannan ta sauke Ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta, barci yayi gaba da ita. Fita suka yi a dakin ya rage daga Layla sai Maina, yana zaune yayi jugum yana kallon yadda take barci. A hankali yake matsa hannunta yana jin kamar ya fashe da kuka har idanunshi tara kwalla. Baki aya rayuwarsu ta baya yake zuwa mishi kome daki-daki. Hawayen da bai zaci saukar su ba sune suka zuba daga manya idanunshi. Ya lumshe idanu yana me kara matsa hannunta. "Please kada ki nisanta kanki daga gare ni kin ji Layla!" Barci take sosai domin kwanakin da Ruhin Rihanna yayi bai barta ta runtsa ba, haka lokacin sallah yayi ya tashi ya tafi yayi sallah sannan ya dawo, anan ne yaga wani tashin hankalin da yaji kamar ya mutu kwanan shi bai kare ba. Domin kuwa an tsinke sarkan da yake hannunta,sannan an dauke ta daga gadon an yasar da ita can, a fahimtar shi kamar fada suka yi don kwatar kanta. "Layla!" D'ago kai
Chapter 103 · 0% Book details