Sashe 90
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya wuce wurin Layla da ya samu tana shan chocolate ice cream, tana sha tana jan hanci daga ita sai hafvest, kallonshi tayi tana fa in. "Baka kwanta ba ne?" "Eh tea nake so baby doll!" Gyada kai tayi ta sauka a gadon ta dauki doguwar riga ta yafa mayafi tafita. Tana gamawa ta koma dakin ta samu yana shan ice cream. "Toh nabaka ne?" "Allah ya baki hakuri kadan nasha naga yana narkewa ne!" Ya amshi tea din. "Ka tafi kafin ka kunno min wutar rikici!" "Da waye?" "Gasu nan tafe!" Ta cigaba da shan Ice cream dinta. "Allah ya kawo su." Yana zaune a wurin yaji hayaniya yana tashi. Kallon Layla yayi wacce ko a jikinta, buga kofar aka yi ta ce mishi. "Ya rage naka, kasan yadda zaka wanke kanka don ni ba zan rasa mafita ba!" Bata rufe baki ba ta saka yatsar hannunta a wuyarta ta fara kwara amai sosai. Sake baki yayi yana kallonta domin kakarin aman nata har waje kana jin shi. Kafin kace me sun cika dakin. Suna shigowa dakin tana sume musu a wurin. Kuma ba kome bane sai kafce kawai da ta iya. Abin bai bawa Maina mamaki ba amma yadda aka yi yarinyar nan ta iya wanke kanta yana zaune. "Ayya ashe bata da lafiya ne sannu dauke ta ku Kaita asibiti!" Shi kan ya rasa bakin magana domin shan tea yake haka Ummimi suka fita da ita ana ta mata fifita. "Sannu!" Daga Queen Hamidah da Aliyyah fita suka yi tana kuka me ban tausayi. Iyayenta ma abin ya dame su. "ranki shi dade, ina ga zamu tafi da ita gida yanxu yana dokin amarya ne, ba zai kula da ita ba kada wani abu ya sanya mune da asara ba Maina ba." "Ku je gobe zan muku magana kuma zan yi magana da iyayensa." Haka suka tafi da Aliyyah tana kuka. Layla ta kai minti goma tana kwance kafin ta farka, a lokacin yana tsaye a kansu. Shi mamaki yadda ta iya wannan drama yake lokacin da ta farka kwanciya tayi jikin Ummimi domin daga barcin wasa Sai ga na gaske ya tafi da ita, yana ganin haka ya maida ita daki yayi musu sai da safe, lokacin da ya isa ya samu Aliyyah tana had'a kayanta, kallo daya yayi mata sannan ya juya dakinsa ya kwanta. Da asuba bayan ya dawo masallaci aka turo kiranshi har da Aliyyah da Layla da take tsaka da barci, haka suka isa har bangaren Queen Hamidah da ta gama hada sharrinta. Ga iyayen Maina da yan uwansa, Queen Hamidah ta fara warware abin da yake faruwa tare da gayawa Malik, sai da ta gama kafin ta nuna Layla ta ce musu. "Maina da Matarshi suna zaune lafiya, shigowar wannan matsafiyar ya lalata kome ga Aliyyah ta tab'a yin tsafi a gabanki ko?" Sai da Aliyyah ta kalli Maina kafin ta gyad'a kai ta ce. "Eh Queen da ma tsafin ne da sauki Arniya ce, bata sallah balle salati." Yadda tayi ta fadar magana son ranta ya sosa ran Maina Layla kuwa kamar bata wurin. Ita ta rasa me tayi da ake wannan surutun. "Tow me kuke son Maina yayi da ake wannan maganar?" Inji Malik da ranshi ya gama aukar zafi. "Ka saka Maina ya sake ta, ya bar masarautar nan ko kuma a hukuntatta!" Inji Queen Hamidah. Matsawa jikin Maina Layla tayi tana kallonshi kamar zata yi kuka, "Kwantar da hankalinki, Haskena!" "Sultan rabamu zasu yi?" Girgiza mata kai yayi yana . "Babu wanda ya isa wannan hukuncin." Shiru Malik.yayi sannan ya kalli Maina da yake rungume da Layla. A karon farko a rayuwarsa da yaji matukar tausayin Babban dan nashi, sannan ya juya ga Iyayen Aliyyah ya ce musu. "Kuna fahimci bukatar Mother da yarku haka ya muku daidai?" Babanta ya cewa Malik. "Eh tow idan har rabuwarsu shine xai samar musu zaman lafiya, ai ya kamata ayi mata adalci!" "Shi kenan ku tafi zuwa yamma zan bukaci dukkansu, har daku." Daga haka ya mike ya bar parlour. Haka bai wa Queen Hamidah dad'i da su Aliyyah dad'i ba, abin tausayi idan ka ga Layla da Maina. "Ki shirya kizo mu fita" "tow Sultan!" Haka ta shiga bangaren Ummimi ta shirya sannan ta nufi bangaren shi. Tun daga kofar shiga da fadawa da masu tsaron kofar take jin muryan Aliyyah. Bata shiga ba, ta kira Maina a waya. "Na shirya!" Ta furta a hankali can sai gashi ya fito tare da riko hannunta suka fita daga angaren suka nufi inda mota take ajiye. Sun shiga kenan sai ga Aliyyah. Yadda take ihu da fada yasa Maina jan motar da gudu, ko kallo bata ishe shi ba suka bar masarautar, kifa kanta Layla tayi ta rasa me zata yi wani gidan cin abinci ya kaita suka karya ya mata guzirin wasu. Ba tare da ya gaya mata ba, ya dauki hanyar wagaduwada. Tun tana kallon hanya har barci yayi gaba da ita, wajen karfe daya na rana suka shiga garin har lokacin bata farka ba. Yara da yan matan suka hango mota ya shigo garin abin ya basu mamaki domin sun san an kara rufe garin. Ganin motar Maina ya wuce har majami'an su yasa suka fara firfitowa. Parking yai ya kalli Layla da take barci. "Haskena!" Bude idanu tayi ya shafa kumatunta. "Tashi ki ga inda na kawo ki!" Ya fada mata, a hankali ta mike zaune tana me kallon garin kafin ya sauke glass din ta shaki iskar garin. "Laaa Layla ce!" Duk suka fada da karfi. Da sauri ta balle kofar motar ta fita tana murmushi da farin ciki. "Layla!" Haka aka yi ta ihun ganinta da murna daga nan cikin gari suka nufa ya ravi da Malamin majami'an suka gaishe shi. "Ravi ya gaya min zaka zo, ban dauka yau ba ne." Ya kalli hanyar da Layla tabi. Sannan ya kalli Maina kafin ya dasa da cewa. "Yarinyar nan rayuwarta cikin maraici ta fara, amma dake tai imani da Uwargijiya gashi ta kawo mata kai a cikin rayuwarka." Suka isa kofar majami'an suka zauna. "Yallabai mun kullaci masarautar Baihak sosai, domin abin da suke kashe mu akai shima suke aikatawa. Kafin yau ita kanta Sarauniyar Baihak jinin wagaduwada ce, amma ta butulce mana, Ravi ya gaya min ya baka labarin masarautar Baihak da ita kanta Sarauniyar Baihak, wacce ba ita bace Uwa ga Sarki Malik." Gyada kai Maina yayi. Madara da apple da ayaba da sauran kayan dangin ittace. Ya fara ci yana jinjina qarfin halin Queen Hamidah tare da yadda ta kifar da kome ta kuma shafawa Malik kashin kaji, hango Layla Maina yayi ya maida hankalinsa kanta. Tana isowa ta ce mishi. "Oya bude baki Sultan! Ka zauna Malamin majami'an ba ciyar da kai zai yi ba,har na zauna zan fara cin abinci na tuna da Yaron Ummimi bai ci kome ba! Oya open your mouth!" Bude baki yayi ta zuba mishi abincin da ya ji ganye da kayan kamshi irin na mutanen kauye wa anda basu damu wayewar rayuwa ba, haka tayi ta bashi yana ci tana me mika mishi kofin madara ya sha. Wasa -wasa sai gashi ta bashi ya ci sosai. "Malamin majami'a kyale min shi ya ga gari." Ta riko hannun Maina suka nufi wurin motar shi ya dauki abin sallah, sannan suka shiga garin lokacin Sallah yana yi ya tsaya yayi sannan ta dauki abin sallah tana nuna mishi wuraren tarihin garin. Karshe suka yada zango a bakin ruwan garin. "Are you happy!" Gyada kai tayi tana fa in. "Sosai kai."daga haka suka sha hira kafin wurin karfe uku ya mike yana fa in. "Kin san zamu gana da Malik da dare!" "Ka tafi ka bar ni anan nasan ko na bika wulakanta ni Queen Hamidah zata yi nan ne dole na, can ba dole na ba ne." Kamar ya kurma ihu ya ce mata. "Ina nan tare da ke, sai dai idan Ifraz zaki gani." Ya fada da wani irin U a'amurya mara amo. Tashi tayi ta rungume shi tare da tsalle wai zata sumbaci goshinsa. cak yayi sama da ita. Ta sumbaci goshinsa. Sannan ta rike fuskarshi. "Na bar wasu abubuwan saboda kai na sadaukar sabida kai, kayi min al awarin idan muka tafi ba zaka bar ni alone ba, zaka tsaya min a kowani kusurwa!" Rungume ta yayi na wani lokaci, ya ce mata. "Na rantse da Ubangijin talikai na zan barki ba, ba zan bari kiyo kuka ba, ba zan kuma bari wani ya shiga tsakaninmu sai mutuwa! Itama a tare zamu tafi kin ji!" Bakinshi ta kama tana tsotsa hawaye na zuba mata. Ita ta san me take akan Maina zuwa yanzu ya shayar da ita abubuwa masu yawan gaske. A hankali ta sake bakinshi tana fa in "muje kada mu makara gashi nan ga Ifraz ba!" Matse mata hannu yayi tana murmushi ta ce mishi. "Wash Babynbaby!" "I'm I hurt you?" "A'a kawai yadda na san zan ga Ifraz ne." Jan hannunta yayi suka wuce wurin motar su, ya je yayiwa Malamin majami'a sallama sannan suka wuce gidan magajin garin wagaduwada, suka mishi sallama. Kallon Maina yake cikin kauna da tausayi. Ya rako su, "ban sani ba ko a wata rayuwar zaku sake zama ma'aurata amma tabbas addararku tabbatacce ne, Layla bayan barinki nan mahaifin ki yazo ga sakon da ya bar miki!" "Abbana!" Ta fada tana kallon Maina, "Eh Layla gashi ya ce yana Baihak ne yana aikin jinya, amma ya ce ma gaya miki ki nemi shi!" Kamar zata yi kuka ta ce ma mishi. "Nagode sosai, shugaba." Ta amsa tana kallon Maina. Shi kanshi shugaban tausayi suka bashi, yar suka fita malamin majami'a ya ce. "shugaba wani taimakon zan musu, bai kyamace ta ba bayan yasan wacece ita, shugaba dole Tirsila da Hamidah su mutu, amma masoyan nan idan dayansu ya mutu dayansu zai tagayyara." Ya fada yana kuka,"Malamin majami'a kai Sarkin addu'a ka taya musu da addu'a. Muma ba zamu barsu ba." A ranar suka baza ko wani kusurwa na garin da addu'a. _A hanya kuwa kowa jigun ya zauna Maina ne yayi kokarin janta da hira har suka iso Baihak ana kiran Magariba. "Ban yi la'asar ba!" "Kayi mana sai mu koma gida!" A Baihak kuwa Malik