Sashe 71
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na hakura." Shafa kanta yayi yana jin babu dad'i. "Zan kai ki wata sati kin ji!" Kuka kawai take domin tasan yana gama abin da yake zai kuma mata abin ranar, sai dai kuma shima kamar ya fahimci kukanta yana ganawa ya zauna da ita har ma ya tsaya ta gyara jikinta bai kuma gwadawa ba, haka kwanaki bai kulata ba, kai har ta warke ta kuma manta da batun gida domin lokacin ya kashe kudi dayawan gaske domin ta kammala Secondry school. Haka yasa ta manta da wani abu ya faru, sai dai dake Mace ce bata rena namiji jikinta ya fara budewa kamar yadda kowacce mace take. Da zaran namiji na tab'a ta, tow lallai tana wasu irin sauyawa da kowa ya kalleta sai ya fahimci haka, kuma haka ne ya faru da Layla domin ta an fara rawan kai, sannan kirjinta da babu auki yanzun kan ba laifi ya fara cika gaban rigarta, rawan kai kan ba laifi idan su Sainah suka zo wurinta tayi ta musu abu kamar wata uwar mata, koda yake wani lokacin bata sanin tana yi, sai dai na kusa da ita yasan tana manyance. Idanunta sun d'an bude amma ba can ba, sannan tsakaninta da Maina ko wurin kwanciya bata yarda su ha a, amma duk lokacin da ya kamata sai yayi ta matseta yana lashe duk inda yake muradin, domin yasan tsoronshi take ji. Ranar da zasu gana makaranta Aliyyah tazo wani abin da ya bata mamaki ganin Ayrah itama tazo, sai abu na gama da ya kara gigita mata lissafin sarka da Maina ya saya musu ta gani a wuyar Layla, ga idanun Maina akanta.........(Aliyyah Mijinki munafiki ne Matarshi ce Layla Innalillahi bom) [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu __________43 Chakulkuli ya fara mata, ta fara dariya kamar zata shid'e sai dai ba'a yi nisa ba yaji tayi shiru. Bude bargon yayi ya ga yadda ta kafe kamar babu rai a tare da ita, tab'a ta yayi ta tawo kanshi baki aya. Da sauri ya janyota jikinshi yana kiran sunanta amma ina. "Ke Layla!" Ya jijjigata amma ina ba dai wannan lokacin ba, mikewa yayi zai fita da ita, ta fashe da dariya. "Ka zata zaka tsare min ne? Ko ance maka zan kyale ta ne?" Mika tayi tare da d'aga mishi gira. "Me ya dawo dake?" Juya shud'in idanunta tayi tana murmushin jin dadi ta ce. "Soyayyarka mana. " Fisgota yayi yana huci. "Ki fita kafin mu raba hali." "Ba zan fita ba, kai ko na fita ma dole ka bukaci alaka da ni." "Zaki fita ko sai na baki mamaki!" D'aga kafadarta tayi tana fa in. "Babu inda zan je, na gaya maka kuma a duk lokacin da na samu dama zan fita da ita muje daukar fansa Baihak!" Cak yayi da fadar shi yana kallonta, "baka dauki haske ba ne? Ita wannan yarinyar ita ce wacce kakarka da Babanka suka kashe mata kakarta. Ka hango abin da ka yi ai? Tow ai fansa ce ta shigo da ita duniyrka ba bauta ba, domin tafi arfin tayi maka bauta ruwanka ne ka saka idanu akanta ko kuma ka shafa ka ji bata nan!" Daga haka ta fice abin ta, tana murmushin mugunta, idan har ta haifar da zargi a tsakanin Layla da Maina, ta haka ne zata iya shiga rayuwar Maina idan basu shiri da Layla zata yi ta kawo masa ziyara ta jikin Layla. Sai dai hakarta bata cimma ruwa ba, domin Maina bai yarda da ita ba, lokacin da Layla ta dawo hankalinta barci ta kama yi ya gyara mata kwanciya ya bar gidan,ko a ranshi maganar HILDA bai dame shi ba, domin yasan sharrin Jinnin zasu yi abin da ya fi haka, bayan ta tashi sai da yazo ya dubata, ya samu tana kwance a parlour. "Layla!" Tashi tayi zaune tana kallonshi. "Papa ka dawo?" "Eh My girl!" Ya fa a yana tab'a goshinta yaji ko da zafi, "Bani da da lafiya ne?" "Eh dazun nan kin suma ne?" Kallonshi tayi iyakar tunaninta, tana son ta tuna abin da ya faru bata iya tunawa ba. Mikewa tayi ta nufi kitchen ta kawo ruwa da jagwalwalen da tayi ta nufe shi tana ajiye mishi ai tasan haka Aliyyah take mishi. Sannan ta wuce kitchen ta hada da mishi tea. Sai da ya tafasa sannan ta kawo mishi tana fa in. "Papa duba ka gani bai yi sugar ba?" Daukar tea din yayi yana me kai bakinshi zai kurba ta ce mishi. "Papa da zafi fa!" Cokali ya dauka ya juya tare da kaiwa bakinshi yaji sugar ba laifi bai yi zak'i sosai ba ya ce mata, "kin iya dafa shi kuwa!" "Kaci abinci mana!" Shiru yayi yana kallon yadda ta tsare shi da idanun, riko hannunta yayi ya zaunar da ita a gefenshi. "Zanci mana!" A hankali ya dauki cokalin cike da abinci ya kai baki, yana ci yana kallonta yasan zai mata kwana biyu. A hankali ya cigaba da cin abincin, yana kurban tea din. Har ya cinye sannan ya ce mata. "Had'a min ruwan wanka kin ji!" Gyada kai tayi, ta nufi dakinshi tana gama hada mishi ruwan,har zata juya ta ga ruwan yana juyawa kamar ana juya shi. A hankali ta kai idanunta cikin ruwan hango wata mace tayi me kama da ita kamar madubinta kuwa. Murmushi tayiwa Layla ta miko mata hannu, itama ta kai hannu zata bude kofar ban dakin Maina yayi yasa matar da take kama da ita, ta b'ace. "Me kike yi?" Da sauri ta juya tana kallonshi. "Kina jirana ne?" "A'a" ta fa a da sauri tana me kokarin fita daga ban dakin ya rikota tare da rungumarta. "Ina zaki? Taya ni wanka please!" Rasa yadda zata kwace a hannunshi yasa ta ce mishi. "Papa banci abinci ba!" Yadda ta rikice ya bashi dariya, "ki taya ni wanka kawai!" "Papa please!" Ta fada a dan shagwab'e, yadda tayi maganar yasa shi kyaleta, ta fita da sauri tun kafin ta bar dakin shi take hango inuwar mutum a kofar dakin amma haka ta nufi kofar tana saka hannu ta bude kofar ta ga babu kowa, parlour ta wuce ta zuba abinci har ta zauna zata fara ci ta ji motsi a dakinta, jin babu kome, yasa ta juya zata fita. "Layla!" Ta ji ana kiranta, juyawa ta fara yi bata ga kowa ba, ta kara nufar kofar zata fita aka kira dole ta dawo cikin dakin tana dube dube, bata ga kowa ba kamar an ce ta d'ago kai ta kalli Madubi ta hango Kaka Jamimah. Rike bakinta tayi tare da nufar madubin da sauri bude kofar da Maina yayi ya sakata tsayawa cak kaka Jami ta b'ace daga madubin. "Are you okay?" Ya tambaye ta, a rikice ta ce mishi. "Babu!" "Ok bari na leka Aliyyah da Yara ke kuma ki zo na ajiye ki gidan Mahnoor, yarinyarta bata da lafiya." "Tow!" Da wannan suka bar gidan, haushi ya kama Hilda da take hango Maina yana lalata mata shirinta, so take ta dauke Layla ta boye ta sannan ta rikide koma Layla, haka ta cigaba da zaman jiran Layla ta dawo domin tasan dole ita daya zata dawo, haka yasa ta gama shirinta sosai. Maina ya sauketa gidan Abbas ya wuce gidanshi anan ya samu Aliyyah ta cancand'a ado kamar wata dawisu. Haka ma Yaran sun ci kwalliyar kamar zasu biki. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ga ta karbe shi cikin girmamawa da kulawa, haka ya nufi kan table yadda ta jagorance shi ya ci abinci ka an ya sha tea, yasan bai isa ya ce ya koshi ba, domin yanzu zata ce don ya ci a gidan Layla zai ki cin nata, haka yasa shi ya ci sannan ya nufi dakinshi ya yi abinda zai yi sannan ya dawo parlour aka baza hira a parlour duk da bin su yake amma kuma akwai wani irin nutsuwa da iyalin suka samu, lokacinshi da ya basu da sauraron kowa yana fada mishi abin da yake so ko yake jin haka yake daidai ne. Sai dare Maina ya bar gidan bayan yayi Sallah Isha ya nufi gidan Abbas. Ya dauke ta suka nufi gidansu a hanya yayi ta musu sayayya, koda suka isa gida ya bar nasu Aliyyah a mota ya dauki nata suka shiga cikin gidan. Da sallama ya shiga Layla tana biye da shi. Sanyin da gidan yayi ya sa shi kashe ac in parlour sannan ya wuce dakinta ya ajiye mata kayan ganin yadda ta zauna a parlour. "Ki shiga kiyi wanka ko kuma zo kiyi a dakina!" "Papa ni kaina ciwo yake min!" Kallonta yayi na wani lokaci, sannan ya isa gare ta yana me tab'a kanta, yaji zafi rau." Me ya same ki?" "Ciwo kan yake min?" "Ok shiga zan baki magani a dakina!" Ya fa a yana shafa bayanta, dakyar ta wuce dakin shi ta kwanta shima ya shiga ban daki, lokacin da ya fito ya samu tana tsaye jikin closet in shi. "Kina son wani abu ne?" Ajiyar zuciya t sauke tana kallonshi. "Babu!" Kuma abin da ya kaita can jin ana kiranta ne yasa ta bu e closet in. "Muje kiyi wanka!" "A'a!" "Muje bana son musu!" Haka ta wuce kamar tayi kuka ta ce mishi. "Tow!" Suna shiga ban dakin ya ha a mata ruwa, ganin yadda take nokewa yasa shi mata kome da kanshi, yana kokarin tab'ata ta ji an ce. "Laylatuna! Kin manta kisar gilla da suka min ne?" Da sauri ta juya tana kallon inda taji muryan kaka Jami. "Kin manta da cin amanar da suka min ne? Laylatuna sun azabtar da ni!" Kawai ra fashe da kuka, kanta ne ya fara wani irin hayaki, da sauri ta ja da baya tana kokarin mai da kayanta. "Laylatuna kada ki bari yayi galaba akanki!" "Layla!" Ya kira sunanta ganin yadda take ja da baya. "Zo nan!" Da sauri ta juya zata fita ya rikota fashe mishi da kuka tayi tare da fisge hannunta ta fita da mugun gudu. "Layla!" Wani irin birki ta ci lokacin da ya kirata. "Zo nan!" Ficewa tayi daga dakin. Ta koma akinta tare da rufe kofar dakin, tana kuka.