Sashe 109
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
binti Sheikh Imran Kisra. "Babu inda zani yarona zata bani!" "Dakaru ku wuce da ita Kisra. " take aka saka mata sarka aka yi sama da ita, Hafsatul ikram ta isa gaban Layla. "sannu da gwagwarmaya Sarauniyar karshe ta Baihak sannu da ya in da aka sha, sai dai muna son.mu gaya miki babban yaki ya taso miki dole kiyi amfani da damarki domin wanke Mijinki....... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/13, 9:44 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________76 "Tabbas yaki yana gabanki! Sakon da Malik ya baki ya kamata kiyi tsaye akanshi. Domin kowa ya fahimci Malik ya bar miki sako, Allah zai baki kariya sannan muma zamu tsaye a gefenki domin ba zaki iya kare kanki ba, kiyi rauni sosai bayan haka shu'uman cikinmu zasu bibiye ku ke da Yaranki!" Daga haka suka b'ace. Ita kuma aka saka mata ruwa. Yaran da suka samu kulawa tuni aka saka su a gadonsu. A can fada kuwa a zahirin gaskiya mutuwar Malik ta bar baya da kura domin kuwa an ga wasiyyar shi da ya bari na karshe akan wanda zai gaje shi bai yarda ya rubuta sunan kowa ba, sannan ya rubuta dai abawa Layla damar zabar Sarkin da ya dace. Tsawon kwana biyu ana rigima da tashin hankali babu wanda ya isa ya tunkari Layla domin kana fara tunanin haka zaka fara shiga damuwa da tashin hankali. Abin tambaya anan me yasa suke tashin hankalin? Kowa ya san Maina ne zai zama sarki amma me yasa suka damu domin sun ci kasuwarsu da dukiyar al'umma wanda Malik ya kyale su domin suna da goyan bayan Hamidah. Haka yasa Malik ya roketa ta tsayawa Maina a kowani yanayi. Abun da ya fara saka Maina a tashin hankali inda aka yi ta wasu rubutu akanshi wai shi ba jinin Malik ba ne, wannan aikin Hamidah ne tasa jarida su buga labarin karya akanshi. Baki aya yan uwan Maina sai da suka tausaya mishi domin ko taron suna da ya hadu da ranar bakwan malik ba ayi ba, karshe Maina boye kanshi yayi yana me jin kunyar fitar da kanshi. Tana zaune abin duniya ya dame ta, Haeda ta ce mata. "Ki tafi wurinshi kadaicin yayi mishi yawa!" Shiru tayi kafin ta mike tare da gyara jikinta ta nufi bangaren shi babu kowa a parlour dakinshi ta nufa ta same shi yana karatun Alqur'ani. Zama tayi gefenshi tana shafa kanshi. Murmushi yayi ya ce mata. "Layla kiyi hakuri ban gaya miki sunan Yara ba ko?" "Hmm bashi ya kawo ni ba, sakon Malik nazo na gaya maka." "Bar maganar nan bai da fa'ida!" "Yana da shi Malik ya roke ni akan abu biyu ne daya na tabbatar ya cika sannan daya sai bayan ya cika zan gaya maka yanzu abin da zai yi ni da kai zamu je Fada in sha Allah." Sumbatar shi tayi ya rungume ta jikinshi yana rawa. "kayi hakuri zan dawo gare ka yanxu ina cikin yanayin jinya ne!" Ta fada tana murmushi, sai dai sumbatar da suka yiwa juna kamar zasu cinye kansu. Lokacin da ya cafki madaran Yaranshi ne ya kara haukace mata sai da ta kwace tana dariya. Yana ajiyar zuciya ya ce mata. "sunan Yaran namijin Abdulmutallab Malik kenan, mace kuma Kalfana Malika!" "Sunan ya dace da su!" Dake an sallame su daga uwar har Yaran suna cikin koshin lafiya a gida aka kawo nurse suna kula da su, washi garin suna Aliyyah tazo da Yaranta uku ta bar Sanah a gida wurin Ummimi, ganin Layla a gidan yasa jikinta ne yayi bala'in sanyi, tasan Layla bata cikin rayuwar Maina ita ce sanadin shigowarta, sannan tasan Maina bai da ra'ayin tara mata ita ce tayi sanadin haka, har ila yau bata yarda akan Layla kishiyarta ba ne gani take kamar kwace tayi mata. Tana ji kamar fashin mijin tayi mata, "Sannu da zuwa. Nuri sai yau zaki zo ganin kannenki!" Inji Haeda. "Kuyi hakuri ina zuwa school ne!" "Maminki tana sama je ki wurinta!" Da gudu ta haura sama, sai da tayi Knocking aka ce ta shiga ta tura kofar. "Mamina!" "Na'am Daughter like no other." Inji Layla tana me bude mata hannu, shiga tayi tana dariya. "I miss you Mami!" "Me too my love, kin ga su Malik da Malika sun yi fushi baki zo wurinsu ba" ta fita jikin Layla tana me haurawa gadon. "Mamina then look so cute!" "Da gaske!" "Eh mana wannan tana kama da Papa wannan kuma da ke!" "A'a kalla da kyau Dukansu suna kama Sanah ce." Tura baki tayi tana fa in. "Na daina wasa da su, tunda basu yi kama da ni ba sai wata can da bata da lafiya!" Ta fa a tana wasa da Malika. Turo kofar Haeda tayi tare dasu Aliyyah. Layla ta d'ago kai tana murmushi. Gaban Aliyyah ne ya fadi yarinyar nan bata da matsala ne? Aliyyah ta fada a ranta. Shigowa tayi ta zauna a kujeran dakin. "Sannunku da zuwa Mum ya Sanah da jiki!" Sannan ta juya ga Sainah da take dari-dari domin kada Uwar ta kamata da laifin kula Layla. "Sainah ba magana ne?" "Sannu Mami yasu Namcy!" Murmushi Layla tayi me sanyi ta ce mata. "Gasu nan ga takwaranki!" Shigowa Haeda tayi da kayan ciye-ciye, sannan ta juya ta fita. "Ya hakurin da Malik kuma?" Inji Aliyyah wacce ta rasa abin fa a. "Alhamdulillahi!" Daga haka suka yi shiru baki ayansu. "Ashe an saka musu suna a wurin Ummimi na ji!" "Eh nima ranar sunan ya gaya min." "Hmm! Shine ba ayi miki taron suna ba!" Murmushi Layla tayi sannan ta ce mata. "Rasuwa aka musu fa, taya za ayi taron suna? Ai ko wani ne ya ce min ayi taron suna sai na sab'a mishi balle uba suka rasa ba wani cikin yan uwansu ba, ina girmama lamarin Papa domin matsalarshi nawa ne!" "Eh haka ne amma da ko yar walima da kunyi ai!" Zata yi magana Bahi ta shigo tana fa in. "Maina jego bana jin kamshin abin dad'i." "Barka da zuwa Ummin Na'im, Mum ba zan iya murnan suna ba, domin Malik kamar Uba ne a gare ni, Mahaifin Maina mahaifina ne, kin ga kenan ba shi ba wani na kusa da Malik ya rasu zan hakura da wani taron suna mu bar maganar nan kawai tunda kome ya wuce Allah ya bamu lafiya ni da Yaran baki aya tunda gasu nan ba wani kuzari ne dasu ba tunda ba wata tara aka haife su ba." "Haka ne amma ni zan koma gida na haihu, Yaran zasu dawo nan ne." Sai lokacin Bahi ta gyara zamanta da kyau ta ce mata. "Ki ce saboda abin da ya faru zaki tafi ita Sanah waye zaki barwa?" "Kina da gurguwar fahimta ni fa haihuwa zan tafi nayi." "Shi kenan ai Allah ya kai mu ba shi kenan ba, nan gidan Maina ne yana da ikon Yaranshi su rayu a duk inda suke so kin fahimta Ummin Na'im!" Buge mata hannu Bahi tayi tare da barin dakin a fusace. Bangaren Maina ta nufa ta same shi yana nazarin wasu littattafan addini. "Yanzu haka zaka kyale Aliyyah?" "Tow me kike so nayi mata?" "Amma fisabiilillahi Layla bata san kome ba!" "Itace kuwa ta sani domin ita Malik ya gayawa kome!" "Aliyyah fa!" " addara ce ta ha a mu ba laifi idan ta zabi yadda zata rayu." Wato abin da yake faruwa a Baihak abu daya zuwa biyu ne, na farko shine manya da suke tare da Hamidah sunce basu yarda Maina jinin Malik ne ba, na biyu sun ce an samo wani labarin da ya shafi Maina ba mutumin kirki ba ne. Da wannan suka kafa hujja an haramtawa Maina shiga Masarautar ko ganinshi aka yi sai an hukutanshi. Kuma dama Malik kamar yasan da haka ya ce mata. _"Layla bana son kina amfani da sihirinki! Don Allah ki daina haramun ne amma kafin nan ina niman alfarma ki tsayawa Maina a bashi kujerana domin bayan bana nan zasu yi me yiwa a ga bayan Maina kada ya hau sannan idan ya samu dama.ya janyo Auta da Ibrahim jikinshi domin Ammar da Salahudeen ba zasu iya tsayawa akanshi kamar yadda Haisam da Ibrahim zasu kasance akanshi ba, zasu bashi kariya da dukkansu arfinsu. Amma kece babban garkuwarshi kada ki juya mishi baya ki tabbatar ya zama cikakken sarki kuma namiji! Makiya zasu lullube shi ta ko ina amma ke ki tabbatar kin kare harin da za a kawo mishi don Allah Layla"_ Sannan a bangaren Aliyyah tana son tafiya garinsu ne saboda tasan yanxu Maina bai da wani abu da zai iya zama a cikin masarautar tunda an haramta mishi shiga, idan da bata da ciki zata hakura amma yanzu tasan yana tare da Layla gara ta koma gaban Iyayenta. Haka zai saka ta samu natsuwa, wannan shine tunaninta sannan zata kwaso Yaran baki aya ta dawowa da Layla su. Shine tazo ta gayawa Maina. "Layla ina Papa yake?" "Yana dakinshi da yake kasa." "Tow!" Ta mike ta fita, haka ta nufi dakin, tunda ya shiga ta ga Bahi, ta mike itama ta bar dakin. Bayan fitarta ta gaya mishi abin da ya kawo ta. Shiru yayi kafin ya ce mata. "Haka ya miki?" "Eh haihuwa zan yi idan nayi arba'in zan dawo." "Allah ya kai mu yaushe ne tafiyar?" "Ina jiran abin da zaka yanke akai!" "Shi kenan Allah ya nuna mana!" Ya fada tare cigaba da karatun shi. "Yaran zan barsu anan ne fa." "Ba kome ai!" Ya fada yana cigaba da karatun. Haka ta fita Bahi ta dawo tana mita. "Kiyi hakuri haihuwa zata fa!" " wannan yanayin? Da baka da mai tsaya maka sai Allah!" "Amma ai ba wani abu ba ne!" "Kana kare ta kenan?" "Ko daya bana kareta ina son na gaya miki wani abu shi rayuwar aure ya gaji." "Ka gujewa abokin zamanka don ya fada matsala!" "No ita haihuwa zata fa!" Duk yadda Bahi taso tayi magana amma yaki asalima kare Aliyyah yayi ta yi, da ta koma bangaren Layla itama taki yarda ta ga laifin Aliyyah. Haka yasa tayi fushi ta bar gidan, kwanaki