← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 115

Sashe 111

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kula kowa bata yi ba, ita tasan dole Maina zai zo saboda Yaranshi dole zai zo ya bukaci ta koma dakinta anan ne zasu fahimci ashe gara da tazo tunda ta samawa kanka yanci. Duk da Mahaifinta bai fito ya nuna mata tayi kuskure ba, amma ko da wasa yaki yarda ya nuna mata fushi sai ma riritata yake yana nuna mata tayi kokari ma. Yadda aka saka musu takunkumin hana fita haka yasa Ummimi ta yanki jiki ta fadi, aka rasa wanda zai fito da ita dole suka kira Maina wanda yana ban daki, Layla ta dauka tare da sakawa a kunne. ",hello yana wanka!" "Ki gaya mishi don Allah yazo ya kai Ummimi asibiti ta fadi a ban daki!" "Tow!" Ta kashe wayar ta sauka a gadon ta wuce dakinta, wanka tayi ta sauya kaya, sannan ta dafa bangon dakin idanunta a rufe kafin kace me sai gata a parlour Ummimi ta samu duk Yaran sun zagayeta. "Salahudeen!" Yadda ta kira sunan don basu san da zuwanta ba, suka razana. "Rike Hannunta ka rufe idanunka!" "Tow!" Ya fa a yana kallon Matarshi. "Zan dawo!" Rufe idanu yayi sai gasu a parlour lokacin Maina ya fito nimanta. "Daga!" Da sauri ya sauko yana tambayar meke faruwa. Salahudeen yana gaya mishi a take suka fita da ita zuwa asibiti. Ita kuma ta sake juyawa ta koma Baihak. Parlour Hamidah ta nufa da take zaune ana mata fifita ta tsaya a gabanta. "Ke!" Tafa hannunta tayi kowa na cikin parlour ya tsaya cak sai ita da Hamidah ne suke motsi itama Hamidah an dankarar da ita wuri guda ne. "Meye matsalarki da Maina? Ai ho kina son a baki mulkin don ko bawa Haris wanda ya kasance d'anki da kika haifa da bawanki ko?" Wani irin razana ne ya cika zuciyarta. "Shi kika bawa Turaki domin ki ji dadin kadamar da harinki, ni kuma na shammace ki na saka an dauke Haris ban san me zai faru ba, zai dawo ne ko kuma ya tafi ne sannan abu na gaba akwai wani abu da zamu yi amma sai kin tabbatar da kin nemo d'anki ni kuma zan yi miki alfarmar ki rayu ko ki mutu! Baihak na ahalinmu ce da Maina da jinin ahalina aka gina shi don haka ke da duk wani me kokarin shiga Baihak sai ya zama tarihi, na rana daga yau ba zaki kara barci cikin kwanciyar hankali." Daga haka ta bar parlourn bayan ta sake su. Kamar wacce aka kuncota daga gidan mahaukata haka Hamidah ta fita tana ihun ina Haris. Haris boyayen dan Hamidah ne ta haife shi ne da bawan Sarki wanda kusan dalilin haka ta kashe tsohon sarki sannan ta saka aka fitar da Haris yadda za a ce Malik ta haifa, bayan Malik yana mulki Haris ya dawo Baihak inda tayi ruwa tayi tsaki aka bashi Sarautar Turaki wanda Malik da hannunshi ya bashi mu amin. A bangare guda Haris ya fi Hamidah hatsari, babu wanda yasan wannan abin sai Malik da Layla sannan ya tab'a rubutawa Abu Ammar sakon ya ajiye mishi, a lokacin da Malik yake tunanin barwa Maina kujerarsa shine suka mishi asirin da ya kwanta jinya, a ranar da zai rasu da Layla ta je duba shi ya gaya mata abin da yake faruwa, ita kuma tayi al awarin sai ta kure gudun Hamidah. Sannan ko rashin lafiyar Ummimi da yasa yau ta shiga fadar kange masarautar aka yi da tsari haka yasa ta karya tsafin ta shiga sannan ta kuma saka aka dauke mata Haris din aka fitar da shi a nahiyar yadda ba zai iya dawowa ba. Sannan babu tsafin ko aljanin da zai iya dawo da shi wani tsubiri aka kaishi aka ajiye shi ya rayu a wurin babu wanda ya mishi magana sannan idan yayi kokarin gudu duk tazarar gudun da zai yi ba zai tab'a barin inda yake ba yana tsaye a wurin guda. Tana barin wurin Hamidah wurin shi ta nufa. "Barka dai sarki me jiran gado!" Ta fada tana zama a kan iska. "Wai meye matsalarki da Baihak!" Wani kallonshi tai kafin ta ce mishi. "Baihak? Tow jinin ahalina aka gina masarautar da shi, gaya min dan bawa ni ban cancanci zama sarauniyar Baihak ba ne!" "Ki fitar da ni daga dajin nan!" "Anan zaka rayu har mutuwa xan na zuwa dubaka idan na tuna da kai amma ba zan tab'a barin ka ka fita ba domin wannan tsibirin shafafeen wuri ne da na kirkira maka iya ni da kai da wadanda suka kawo ka zamu ganshi." "Meye laifina?" "Kashe Matar da kuka yi a asibiti watannin baya, sai bawa Malik guba mara makari, ba zan kashe ka ba ina fatan kayi nisan kwana anan tsubirin..... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/15, 10:10 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________78 Hawaye ne ya zubo mata, "Hamidah zata cigaba da ganin bala'i da masifar rayuwa kamar yadda ta hana kowa barci sai na tabbatar ta zauce kamar ta mutu amma ba zan so haka ba, domin ta girbi abin da ta aikata!" Har ta juya ta kalle shi tana murmushi"na fasa barinka anan zanso ka rayu da ita kana me jin zafin abin da ta maka amma zauna kafin na dawo kanka." Ta fita tana share kwalla da yake bin kyakkyawar fuskantar. Ta kofar ban akinta ta fita tana kallon Yaran da suke ta barci cikin natsuwa ta zauna tana kallonsu kafin ta fashe da kuka, shima mahaifinta kamar bai damu da ita ba, wannan yasa take kara jin tausayin Yaranta. Idan wani abu ta same ta tow bata da wanda zata kira nata. Kawai haka zasu rayu cikin kunci da bakinciki don ma Ubansu yana tare da su. Batan san Haeda ta shigo dakin ba, sai da ta dafa kafarta tana fa in. "Me yasa kike kuka?" Juyawa tayi ta rike hannun Haeda. "Koda yau bana raye kada ki bar Yarana su yi maraici na hadaki da Ubangiji." Ta fada tana wani irin kuka. "Na amshi wannan nauyin har karshen rayuwata." Ta fada tana durkusawa a gaban Layla. Cikin shashekar kuka ta ce mata. "Na gode! Ta yiwu na rayu ko na mutu ni dai kada ki nisanci Yarana!" "Nayi miki wannan al awarin!" Ta fada tana sunkuyar da kanta. "Je ki!" Matsawa tayi a hankali, sannan ta rungume Layla wacce ta kara sake kukan a hankali, she feel alone, gyaran muryan Maina yasa suka kalli kofar, takawa yayi zuwa gaban Layla Haeda ta bar dakin, ya mika mata hannu. Saka nata tayi ya d'aga ta a hankali yana me janyota jikinshi. "Me kuma ya faru?" "Ina jin kewa ne!" Taya zai fahimtar da ita hakuri yana daga cikin addarar dan Adam. "Kiyi hakuri!" "Nayi Sultan!" "Promise me ba zaki sake kuka ba!" "Nayi maka wannan al awarin!" Ya rungume ta yana shafa bayanta. Da dare suka tafi da Yara duba Ummimi har da Annah, da ta ce zata zauna, haka suka barta a can suka dawo gida, sai da yara suka kwanta sannan ta nufi dakin Maina da yake zaune yana kallon wani hoton Malik. Rufe mishi idanun tayi tana fa in. "Canka waye a bayanka?" Janyota yayi ya daurata akan cinyarsa. "Ina bukatar wani a kusa dani! Yawwa inji Doctor Jafar ya ce na gaya miki zai zo duba Yaran!" "Bana bukata!" "Kiyi hakuri mana!" Jan hancinta yayi yana hararanta. "Sorry !" Murmushi tayi tana wasa da sajenshi. "Kiyi hakuri kinji!" "Ya wuce ai tunda ka bani hakuri!" Daga haka suka shiga labarin dare. Hauka ne kawai Hamidah bata yi ba, amma ta birkita Baihak, har sai da ta cire ranta zata kuma ganin shi domin sai da aka kwana aka wuni kafin aka samo shi a bakin ruwa, kawo mata shi kafin a same shi sai da Layla ta saka mishi tsanar Hamidah. "Zan kyale ka ka tafi amma ka sani har abada Baihak ba naka ba ne domin kuwa, kai shege ne baka da uba idan nayi karya ka tambayi Hamidah!" Daga haka ta saka a kawo shi wurin, lokacin da ya farka abin da ya fara tambaya shine. "Mamma waye Ubana?" A gaban jama'a, kunya yasa ta ce mishi. "Tsohon sarki mana!" "Waye Uzaifa? Ko bashi ba ne mahaifina? Gaya min waye Ubana!" Yadda yake ihu yana buge buge yasa ta tsorata domin da yaga ba zata bashi amsa ba, fita yayi ya dauko karfe ya zo ya same ta. "Gaya min waye ubana? Ni shege ne?" "Babu wani kai shege ne wanda ya gaya maka haka yayi haka ne don ya gurbata maka tunani!" Duk yadda taso masa bayanin yaki, haka tasa aka rufe shi domin yana ta hakika. Har kamar zai balla kofar, ya ce Mata. "Layla ba zata min karya ba, Layla ba zata boye min abin da kika yi ba, wallahi ki gaya min Ubana ko na fito na kashe ki." Wannan abin ya kara bata mata rai. Washi gari da sassafe ta isa fadar kafin wani yazo ta shiga har ta zauna akan kujeran fadar, koda emirates counciler suka iso Kowa yasha mamakin yadda ta zauna a kujeran kowa nason magana amma yana tsoron me zai dawo. Haka suka yi shiru suna kallonta. "Ba a tab'a samun wanda yayi wannan kuskuren ba sai ke! Hamidah." Inji Layla da ta shigo fadar cikin shigar Alfarma. "Dakaru." Dariyar Layla tayi tana fa in. "Ai Hamidah yadda kika karanta musu haka na musu bitar nawa karatun." A hankali ta isa gabanta. "Na zo miki da babban kyauta!" Matsara tayi gefe sai ga Haris. "Wa...wa....wa.. waye ta bu e ka?" "Sai kin gaya min waye Ubana? Sarkin Muhammad Hatim ba shi bane ubana zaki gaya min ko sai na kashe ki!" "Ko na gaya maka ba zai amfane ka ba, Ubanka shine bawan da Sarki Muhammad Hatim ya kama Ni da shi yasa aka kashe shi." Ta fada da karfi kowa na jinta, juyawa tayi tana kallon Layla. "Na fada haka ya miki? Amma ni kuma zan baki kyautar mutuwarki." "Layla!" Ammar ya fada da karfi daidai lokacin da Tirsila ta nufe ta da gudu zata suka mata wukar da ta yi da
Chapter 111 · 0% Book details