← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 115

Sashe 22

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa sai kinzo* ___________________ Yadda ta kurawa kofar idanu kamar tana iya hango abinda yake faruwa a waje, nan kuwa ba haka ba ne, "wallahi na gaya maku babu kowa a dakin zan muku karya ne da tsofana, shi kenan ku duba ai." Ya fa a yana kokarin bude musu kofar, yarinyar ta kuma rufe bakinta, har ya bu e zai turo kofar dakarun suka ce mishi. "Shi kenan, idan aka kuma kawo mana gulmar kana da mace a cikin gidan nan, harbe ka zamu yi tunda babu abinda zaka kara yi." "Na amince!" Ya fa a muryan shi yana rawa."Na yarda!" Sauke ajiyar zuciya yarinyar tayi tana share hawayenta a sannan ta kalli Layla slowing. "Bakya tsoro ne?" "Su waye su?" "Dakarun Malik ne" lumshe idanu tayi kafin ta bude shi akan yarinyar ta ce mata. "Me suke yi?" Sai da yarinyar ta sauke ajiyar zuciya kafin ya ce mata. "daukar yan mata ake da karfin tsiya a kaisu cikin Baihak babu wanda yasan me ake masu, domin idan suka shiga basu kuma dawowa!" Gyada kai Layla tayi hawaye na cika mata idanu. "Wani abu ake da su?" Cikin shashekar kuka yarinyar ta ce mata. "Yayuna mata biyu tunda suka tafi basu dawo ba, sai kannena maza biyu, kaka shine kome na mu, mahaifinmu ya gudu saboda wahala da talauci, mahaifiyarmu ma haka." "Duk saboda me?" Cikin kuka sosai yarinyar ta ce mata. "bamu san meke faruwa a cikin Baihak ba, amma mata da yan mata basu tsira a bala'in Baihak ba, mahaifiyarmu ma garin gudu ta tsira ta fada wata tsohuwar rijiya, ko gawarta bamu gani ba. Shi yasa kaka da Kaka Hajar zasu kawo miki kayan maza kina sakawa." Hawayen da take dannewa ne suka zubo mata shar wannan na koran wannan. Ita tausayin yarinyar take ji domin matukar ta cigaba da kasancewa mace za a shiga dasu baihak amma da ta tuna da kanta, sai ta ji kuka ya zo mata, shigowar tsoho Salis ya shigo da kaya a hannun shi ya mika musu, sannan ya fito ya dauko musu kwanon soyayyen kifi da ruwa. "Sajida ki kula da ita, ya sunanta?" Ya tambayi Layla cikin kulawa. "Layla!" Ta fa a cikin kuka tana kallon kasa, "Bar kuka hala kema sato ki suka yi ko?" Cikin wani irin yanayi ta girgiza kai ta ce. "Ina son zan koma gida ne?" Kallonta suke kafin suka ce mata. "Taya zaki koma gidan? A ina kuke?" "Wagaduwada!" Shiru suka yi domin daga tsoho Salis, har Sajida basu tab'a jin sunan garin ba, tashi yayi ya fita zai je gidan Hajar, a bakin kofar gidan suka hadu. "Yawwa wurinki zan je, mu shiga ciki." Suka shiga a tare ya ce mata. "Kin tab'a jin sunan wani wurin wai ya ma sunan garin?" "Wagaduwada!" A razane Hajar ta rufe bakin Layla. "kul ki kuma kiran sunan garin nan, domin yanzu haka an kamo daya daga cikin manyan matsafar dausayin za a yanke mata hukuncin kisa!" "Kin gane garinmu ne fa? Kuma taya za a kamo cikin manyan matsafar bayan bamu cutar da kowa ba." "Tsafi shine makiyin Baihak. Nima na samu labari ne kasancewar ina kai magani cikin bangaren bayi." Mikewa Layla tayi. "Ina zaki?" "Idan har manya cikin matsafar Wagaduwada ne Kakata ce." Kamar kiftu da Bismillah sun cure wuri guda, ai yadda aka daura musu tsoron tsafi, yafi yadda suke tsoron Malik da azabarshi, ganin yadda suka cure wuri guda ta ce musu. "Ni ban iya tsafi ba, asalima ba a haife da shi ba. Nima mutum ce kamar ku bani da kome bani da baiwa kada ku guje ni!" Cikin dari-dari Hajar ta kamo hannunta ta ri e, taji babu wani abu na daban ta ce musu. "Kimanin shekaru dari uku da wani abu ana son a shiga Wagaduwada, na samu labarin garin a wurin kakata da na gaji bada magani a wurinta, tace itama ta samu labarin ne awurin kawunta wanda shima ya tab'a zama da mutanen da suka fito daga dausayin Wagaduwada, sai dai daga lokacin da aka gane su ne, ake kashe su domin a shekaru goma sha da suka wuce, nan tudun sarakuna sunan unguwar kenan, an tab'a kashe iyalin wani dattijo saboda an gano cewa Matsafine shima a lokacin aka.kone gawarshi da na Iyalinshi har da yara anana." Wani irin dummmm kan Layla yayi ta dafe kanta, tare da kallon tsoho Salis ta ce mishi. "Ni daya ka samu a lokacin da ka ceto ni baka ga wata a tare da ni ba?" Girgiza mata kai yayi, ta cigaba da dafe kanta. Ita kuwa Hajar sai labarin irin kisan kiyashin da ake wa matsafa. Kuka Layla ta saka tana rike hannunta. "Ku taimaka min na ga kakata!" Rike baki Hajar tayi ta ce mata. "Ke rufa min asiri, masifar da take cikin baihak ai gara a shafe kwarin masunta!" Wato unguwar kenan. Kukan Layla ya tsannanta. "ki ci abinci, koyi hakuri idan muka ce zamu kai ki ya makomar rayuwarmu? Ina da jikoki yanzu zasu dawo ma, don Allah kada ki jefa mu cikin bala'i, idan kin warware zaki iya tafiya, ga wannan dukiyarki ce da muka samu a jikinki ." Ya mai da mata zinarinta, sannan suka bar dakin, idan ta bar nan ina zata? Waye zai taimaka mata kamar yadda suka taimaka mata? Haka ta ci kuka tana jin suna hira a waje, can sajida ta shigo cikin shigar maza, ta ce mata. "Zan tafi kasuwa talla, idan na dawo da wuri zamu tafi bakin ruwa su." Gyada mata kai kawai tayi amma tabbas zuciyarta babu dad'i. Haka ta zaune har dare koda Sajida da kannenta suka dawo kasuwa, da bakin ruwa sun same ta a kwance, tana kuka abincin da aka bata na rana yana nan haka na dare gashi nan, baki aya vata tab'a irin wannan rayuwar ba, haka kwanaki suka cigaba da tafiya, a bangarensu Queen Hamidah, azabar da suke ganawa Kaka Jami yasa ta fita hayacinta,. Sannan abin tashin hankalin yadda suke tsiyaye mata ruwan idanunta dukka biyu,, bata gani wannan shawaran Tirsila ce wacce yanzu ta zama babbar aminiya ga Queen Hamidah, duk wani abinda Hamidah take so tana mata, a cikinsu har da mallake mata Khamilah, sannan aka jefawa Bahiyyah bakin jini saboda kawai tayi magana akan Mahaifiyarsu. Dama can ta saka Falwa ya hanata aure, zuwa yanzu kuma ta kara munana al'amarin kamar yadda take jin zuciyarta zata yi sanyi. Tsaye Falwa yake a gabanta yana kallon yadda jini yake zuba daga idanunta, "Jamimah, ki fada min inda Layla take, nayi miki alkawarin zan bata kariya domin nima ina da nawa burin." Dariya Kaka Jami tayi tana me d'aga kai tana kallon inda yake ta ce mishi. "Layla kake nima? Ai tuni tana nan kai ne baka ganta ba, amma ga layla nan a gabana!" Daukar jar karfen wuta yayi ya mari fuskarta da shi, sai da ta fa i. "Ka zata ban san alakarka da Tirsila ba ne? Ko ka zata ban san cewa kai ne ka janyo Zafir garin nan ba? Duk wannan yana kunshe a cikin abin wuyar sa na bawa Layla daga ranar da ta gano wacece ita, Baihak tayi muku kad'an dama nasan haka zai faru yasa na bata abin wuyar da zai dawo da ita kan hanya, daga ranar da wannan abin wuyar ya fita daga wuyarta haskenta zai mamaye Baihak duhun da kuka jefa mutane a cikin zai washe ko ina Layla ka ai zata zama jarumai arni, Lallai ka gaggauta barin Baihak domin ga zakanyar Wagaduwada tana nan tafe, ita kadai take amma bayanta zuga ne. Na rantse da Uwargijiya wada, ba zata bani kunya ba ko mutuwa nayi ruhina ba zai.kwnta ba sai naga karshen ku ." "Ke karya kike?" Dariya tayi tana fa in, "Na karanta littafin da Uwargijiya Yalna ta rubuta, inda ta ce hassadan mutum ita ce Ajalinsa. A shafi na dubu goma da dari tara babi na hudu tace zamani zai zo cin amana xata zama ruwan dare. Cuta da zalinci zai yad'o a duniya, a lokacin za a haifi wakiliyar Wagaduwada domin kawo karshen kukan marayu baka tunanin wannan karni ne? Baka fahimci wani ba, a sakin layi na biyar ta ce daga cikin al'ummar mu mafiya yawansu azzalumai ne, domin zasu watsawa wasunmu zinari su janyo su ga Mahallaka, kasan me ta ce akan irinku.? Kaskanci da mutuwar kaico ya tabbatar ga haddamammu maha'inta mugaye azzalumai." Dariya ya saka yana fa in. "Baki isa yin kome ba, babu abin da zaki iya kuma wannan maganar taki ba zai tasirantu a kaina ba, ina nan ina jiran mara kunyar jikar Zafir." Wannan rigimar ba karamin abu ba ne, domin shi aganin shi matukar Kaka Jami ta gaya mishi inda Layla take, zai san yadda zai yi ya janyota fadar. Yadda ba zata iya kwacewa ba, yaki gayawa Hamidah gaskiya ne domin karfin mulkin Malik zai iya nunkuwa idan da za a nimo mishi Layla ya kwana da ita, d'igon mabiyansa ya shiga jikinta ya zama ya had'e da jininta, idan aka kashe ta aka mishi wanka da jininta ya cinye mahaifarta, babu wnada ya isa ya mulke Baihak sai shi, shi burin shi ne ya samu damar da zai samu amma matar nan taki magana, kamar daga sama ta ce mishi. "Layla ba zata tab'a bayyana muku ba, ka bar tunanin Layla zata bayyana har kake tunanin boye lamarin ga Hamidah,kasan me? Tirsila tana binciko haka kai zaka zama abin hari na gaba, kafin Tirsila ta d'ago sirrin dawamman Malik kai ka fara gayawa Hamidah satar amsa ce sai ku shiga niman Layla ruwa ajalo" ta fa a tana fashewa da dariya, domin ba zasu tab'a haduwa da Layla ba, don tun kafin haka ya faru tasha binciken yanayin Baihak, kuma abin da take fahimta matar Baihak basu da matsirata sai sun yi shigar maza, da wannan shigar mazan Layla zata fado fadar. Ta sani
Chapter 22 · 0% Book details