← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 115

Sashe 10

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta fa a tare da zabura kamar zai mare ta. "Allah ya huci zuciyarka, ban isa nayi maka rashin kunya ba, nasan girma da darajar ka." "Tow me kike nufi?" "Malik dole ce na fadi gaskiya, Maina ya bar kasar nan don ya tsira da lafiyar Iyalinshi." "Kenan daga ke har Yaronki ba zaku min biyayya ba? Ba zaku taya ni rabuwa da Mother lafiya ba? Uwata ce Maina ya je yaci mutuncinta." A ranta ta ce mishi. *Ai nima kaci mutuncina* a zahiri kuma ta ce mishi. "Kayi hakuri!" Kwafa yayi ya ce mata. "Oya muje ki gayawa Mother domin ban san yadda zan gaya mata ba!" "Tow ranka shi da e!" Haka ya tasata a gaba har bangaren Queen Hamidah, wacce take zaune cikin kwanciyar hankali, yo labari ya jima da zuwa kunnenta Maina ya bar kasar, dan iskar yaro mara jin magana. Ta tsinewa Maina yakai baki dubu. "Kiyi hakuri Mother, da ." "Ka je ka duba Ayrah?" Girgiza kai yayi, cikin kulawa ta ce. "Ya kamata ka je, batun bani hakuri duk bai taso ba, tunda Allah ya bani kai a matsayin me biyayya bani da aufi duk inda dan iskan ya tafi dolen shi zai dawo ai." "Yes Ma!" Suka fa a, murmushi tayi tana fa in. "Jeka Allah ya maka albarka." Daga haka ta sallame su, a hanya kuwa kakkausar martini King AbdulMutallab yake mata, tare da cewa ya zare idanunshi a cikin lamarin Maina. Lokacin da ya isa part din Ayrah har an gama mata wankin ciki, ta koma barci kamar ba ita. Yana sonta sosai amma idan ya tuna abin da ya faru a baya sai yaga har da ita wurin nisanta shi da Maina, shafa kanta yayi tare da sumbarta goshinta. Sannan ya nufi angaren shi, yana nufar dakin shi ya samu kyakkyawar budurwa da ta sha lullube, dakin wanka ya shiga yayi wanka sannan ya fita, babu wani dogon jawabi, yana ganinta yasan abinda ya sa aka kawo ta, don haka ya kashe wayar dakin, cikin tsannanin bu ata ya far mata sai da ya mata kaca-kaca, domin yarinya ce sosai karama, sannan ya d'aga wayarshi ya kira Queen Hamidah ya ce a zo dauke ta, yana ajiye wayar ko minti biyar ba ayi ba, sai ga Bahira da wasu mazan. Suka zo aka dauke ta tare da fita da ita zuwa can cikin masarautar, Wata tsohuwar rijiya aka tafi aka wurgata, Sannan suka juya tare da barin wurin bayan an rufe, tunda aka jefata take arin tashi, don ta soke da kasusuwan da suke tsubiri guda, wani irin dariya take ji kamar ana kusantotta. "Nayi miki halacci, ni ce na baki shawaran a kashe yar uwarki ta haka zaki samu damar shiga cikin masarautar, bayan na hada miki kome kika hada dani kika me yasa baki kashe ni ba, kika mai dani dodanya, sai na dauki fansa!" Hannunta takai ta fasa cikin yarinyar ta zakulo zuciyarta."wannan shine dabban da ya sauya miki tunani, " haka tayi ta cakar gangan jikin yarinyar jini yana watsuwa a ko ina, kafin ta koma gefe tana ihu. "Ku cire ni, ku cire ni ku fitar dani. Sai na dauki fansa." *Afte 3weeks *Scotland* Tunda suka isa, yaran ya yi kokari shi da Prince Auta, aka maida su makaranta. Don dama anan suke, wurin aikinshi kuwa da ba ajiye aikin yayi ba, hannu bibbiyu suka karbe shi, cikin Aliyah kan ya zube bayan ta sha bakar azaba na jinya, a yanzu tana murmurewa. Kamar ba ita ba, Maina mutum ne da baya son hayaniya, duk yadda kake tsammanin waye shi ya wuce haka, wannan barin da tayi ya janyo likita ya basu hutu da tazara a tsakaninsu yadda zata huta, kuma shi da yake yana da adalci ya dauke kanshi daga gare ta, sai dai yanayin shi ba me yawan sabgogi ba ne, da zaka iya fahimtar yana son wani abu ko baya so, kuma tunda suka dawo ya lura da bata cikin nutsuwarta, ita bata so su dawo nan din ba. Don haka yasa auta ya nima mata ticker zuwa asarsu wurin iyayenta a Yemen. Ana gobe zata tafi ta shigo dakinshi, yana ta aiki tunda tayi sallama ta zube a gabanshi. Sau daya ya kalleta tare da amsa sallamar. "Barka da hutawa, My Prince!" "Hm!" Shiru tayi kafin ta ce mishi. "My Lord ina son na tafi da Nuriyya!" Sai da yayi kamar vai ji ba, ya d'ago yana kallonta."akan me?" "Saboda bani da" yadda ya tsare ta da shanyayyun idanunshi masu kama da me jin barci, "ina jinki!" " Naga bata fara zuwa Kindergarten ba" "Ai!" Ya fa a yana cigaba da aikinsa. Zame abayar jikinta tayi ya ce mata. "Kuje Allah ya tsare." Abin ya bata mamaki, ba dai fushi yake da ita ba? Amma har ana fushi da irin wannan abin? "Nazo maka bankwana ne!" "Ina aiki ne!!" Ya gyara zaman shi yana kallon Laptop in. Kamar zata yi kuka haka ta mike ta nufi gadon ta kashe wuyar dakin, sannan ya kwanta. ",Kinyi musu addu'a?" Mikewa tayi da sauri ta fita. "Ban yi ba,!" Wani munafikin murmushi yayi, a ranshi yarinya shi zata yiwa yaji? Har da kaurace mishi, ta je ta jika abinta idan kanwa ce, har da wani yatsina fuska kamar yaga mugun abu. Koda ta dawo yana nan a inda ta barshi. Kwanciya tayi tana me duba notification din wayarta. Zungurerren sakon Lady Ayrah ta gani na cin mutuncin, lumshe idanu tayi tana murmushin takaici, Yes bata yi tsammanin Maina a rayuwata ba, asalima Ayrah ita ta shigo mata da shi, bata tab'a tuninan shi a ranta ba, sai dai addara mace ce me ciki da ba a san me zata haifa gobe ba. Hango shi yayi idan bata yi karya ba, twins addaran su ce da Maina, domin da ta sake auren Maina a wannan ranar da ba ta san wacce zata same su ba, koda yake anyi auren daga shi har ita, kowa kanshi yana kallon wani bangare na daban, zaman da shi a USA yasa kome ya faru, sake kallon kasumbarshi tayi, wanda yake gyare irinta matasa, amma a yadda yake wurin a zaune bai kama da matashi ba, karfi da yaji ya manyatar da kanshi ya zama kamar ya shekara hamsin. A saninta da shi lokaci ba a haka yake, ba din da bai yawan hayaniya amma kuma yana da yawan sake fuska, sosai yake da sake. Domin a da idan yazo Yemen, har ya gama kwanakinshi yana daukar zuwa yawo duk abinda zasu ci ko zasu saya shi zai kashe musu.. *Baihak* Sati uku da barin Lady Ayrah, taji sauki sosai domin har jinin ya tsaya, sai dai kuma zuwa yanzu ta fara gajiya da zama babu d'a a tunaninta hakkin Maina ne yake bibiyarta, don haka ta kira kawarsu Jasrah cikin damuwa ta ce mata. "Jasy na kuma bari fa?" Dariya Jasy tayi tana fa in. "Baki ga kome ba, Lady Ayrah wallahi ko hakkin Maina ya ishe ki, kin ga yau nake jin labarin Aliyah zata zo ganin gida, ita da Beautiful Apples dinta. Ke kuma kin kare a jikin dagus!" "Bana son iskanci da wulakanci, ki gaya min meye illar zama concubines?" "Ai ke baki ga laifin cin amanar da kika yi ba? Ok fine lady Ayrah a cigaba samun ciki yana bin rariya, Yaran Princess Aliyah uku. Mijinta ina jin Darling yana gaya min zai samu babban promotion daga bankin Scotland zuwa.." "Bashi na kira ki gaya min, nima zan shigo Yemen din nan!" "Wow!" "Na gaya miki, ko ajiye a ranki Maina nawa ne, ni daya babu wacce ta isa raba ni da shi." "Amma ke akuya ce?" Inji Jasy. "Ba zaki tabbatar da haka ba, sai nazo sannan da kike kare Aliyah kina kiranta da Princess ta ina zata zama princess? Bayan ta kasa haihuwar da namiji da ake son ta haifa?" "Dakata Malama Ayrah kin manta kema kin kasa haihuwar ne? Balle ita da ta haifi Yara uku da Maina? Yara uku tagwaye da Gambonsu. Dalla kashe waya yar cin amana kawai." Duk wannan abin da suke King AbdulMutallab yana jin ta, yasan ya zalinci Maina, kuma har da kwadayin iyayen Ayrah amma bai kuma sanin cewa ya kunno wutar bala'i ba sai yanzu. Abu uku suka nisanta shi da Maina na farko Ayrah na biyu muzanta Mahaifiyar Maina, na Uku ......... (Meye abu na ukun nan ne?) #Mai_Dambu #Batrayer #Destined #selfishnesss [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s *MASU NIMA DAGA FARKO DON ALLAH GA LINK NAN SU SHIGA ZASU SAMU* ________________7 *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*
Chapter 10 · 0% Book details