Sashe 15
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan abin ya razana shi, Shahida sun haihu lokaci da da Hidayah, Khamilah tana da cikin Bahiyyah, anyi anyi Hidayah ta shayar da shi amma taki, haka yasa aka bawa Khamilah ita ta rene shi, yana da wata uku ta haifi Bahiyyah,haka yasa ta ha a su baki aya ta rena, duk da tana gidan sarautar ita kan bata san dadin sarautar ba, sai hidimar miji da Yara. Shekarun Maina goma ya koma wurin kakanshi yayi karatu tare da Ammar har zuwa degree. Tun yana matashi ya fara zaman shago, ya ha a degree dinsa yana zuwa gida ya ga yan uwanshi da Mamanshi. Ya sha gaya mata ta ajiye yaran ta dawo wurin Danginta ta ce a'a ba zata iya barin yaran ba,zata zauna dominsu. Haka suka gama degree shi ya koma master amma Ammar ya ce shi gaskiya aure zai yi, ya gama hakuri na rike zariyar wandon shi, idan ya kara wasu shekarun ba mace, tabbas idan ya ga mace sai ya biita ya danneta. Sai ya dawo Baihak ya bar Maina ya wuce USA, amma har zuwa lokacin suna tare, sannan a lokacin ne ya hadu da Ayrah, a kasar Amurka a garin Texas, da farko yana yawan jin ana labarinta, saboda kyanta a lokacin da ya ganta sai bata wani burge shi ba, kawai abu daya ya sani tana da kokarin kulawa da mutane, musamman gajiyayyun da mabukata, sai halinsu ya zo daya, wasa wasa sai hankalinshi ya tafi gare ta,haka yasa shi fara bibiyarta. Amma a zahiri ba zaka tab'a cewa ya damu da ita ba, duk da tunawa da yake Kingdom dinsu babu soyayya asalima an tsine mata, amma yana ji a ranshi babu wanda ya isa dakatar da shi, da kanshi ya kirkiro kungiyar agaji da sakai,na yan uwa musulmai, baki aya sai ya ja hankalin yda dalibai, aka cika da kudinshi ya yi ta daukar nauyin kowa da kome, ga alkhairi kamar bai san ciwon nima ba, sannan idan ya bar makarantar yana tafiya pertime job, Ganinshi Kyakyawa ga salo ga haduwa yasa Ayrah ta makance akanshi,bata da aiki sai turawa kawayenta labarinshi musamman Aliyah, da bata kaita haduwa ba, domin iyayenta basu da halin kaita kasar Amurka karatu. Haka yasa ita da Jasrah suke matukar sha'awar rayuwar Ayrah, koda yake kusan tare suka yi duk wani karatu musamman daga primary school zuwa Secondry school. Don haka sai ya kasance kusan duk shekara idan Ayrah tazo hutu babu abinda ya sauya daga ala arsu, su ukun nan babu wanda ya tab'a jin kansu, sannan suna da rufa asiri. Duk ta ishi kowa da Maina. Kowa yasan Iyayen Ayrah da masifar son abin duniya, gasu wasu irin mutane masu iya shiga rigar aro, Ayrah yar karya ce da son lallai a gane ita wata ce, haka yasa suke yawan fa a da Jasy domin dukkansu basu dauki kansu kamar yadda suke dauka ba, musamman Aliyah da bata da wani buri, har gara Jasy kawunta Yayan Mamanta yana kasar Saudiya yana da katon kanti, duk wani kaya sabon yayi yana mata, ita kuma Aliyah Mahaifiyarta tana da kokarin cire yarta kunya kuma abin burgewa Mahaifinta dan kasuwa ne, banbancinsu da Jasy wacce mahaifinta ya jima da rasuwa, yan mata uku nan sun taso da kaunar juna, da taya juna tattaunawa akan matsalolin juna, Ayrah tana da gab da kammala jami'a Maina ya nuna mata alamar yana son kasancewa da ita har karshen rayuwarsu, abin bai zo mata da sauki ba, domin bata kawo zai kawo kanshi har haka ba, sai gashi kafin wani lokaci sun zama tsuntsayen kauna, kashe mata kudi da suturu da yake har ya wuce misali, sannan bai yi wasa da damar shi ba, haka ya kira Ammar akan lallai yazo, lokaci da yazo ya ga Ayrah abin da ya fara fa a shi ne. "Abokina yarinyar tayi, amma bana jin zata aure ka." Kallon shi yayi kafin ya dauke kanshi. "Kana mamaki ne? Hmm idan ta samu wanda ya fika zata yi tsalle ta barka." Saboda Ammar ya karanci ilmin hallayar dan adam ne, a ganin shi da ita na farko ya fahimci haka domin kuwa ganin yadda take kallonshi ta kalli Maina, yasa shi gane cewa irin yan matan nan ne masu masifar son abin duniya. Karshe rabuwar dutse a hannun riga Ammar suka yi da Maina, domin Maina yana ganin Ammar bai sakawa soyayyarshi albarka ba. Lokacin da Ayrah ta gama makaranta, shi saura wata tara ya gama, da zata koma gida da kanshi ya kaita har gida, ya kuma gabatar da kanshi. Bai fito ya gaya musu waye shi ba, sannan ganin yadda yake barar mata da dukiya yasa ta zama abin sha'awa ga kowa. Bayan ya koma ta tafi har wurin Dangin Ummimi yasa kakanshi lallai yazo ya nima mishi auren Ayrah. Kakan ya kira King AbdulMutallab ya gaya mishi. Bai yi mamaki ba domin yasan Maina zai aikata kome. Don haka da kanshi ya tafi har Yemen da rakiyar Halifa Abu Ammar, suka isa har gidansu Ayrah. Tunda farko zuwan hukumar masarautar Yemen suka tabbatar musu zasu yi baki Sarkin Baihak. Haka yasa suka shiga rud'ani, lokacin da suka karaso, King AbdulMutallab yayi tozali da Ayrah iyayenta suka ga King AbdulMutallab, sai suke ganin like anya Yarsu bata yi kuskuren soyayya da maina ba, yo ina ake zancen crown Prince ga King AbdulMutallab da kanshi, don haka a take iyayenta suka nuna basu da ra'ayin Maina, domin kuwa bai gama kuruciya ba idan aka bashi auren Ayrah kullum za a ta jin kansu, idan King AbdulMutallab zai aure ta sun amince amma idan Maina ne gaskiya ba zasu bashi Yarsu ba. Kai tsaye King AbdulMutallab ya ce musu. "Gaskiya sai dai tazo a concubine, domin ina da matata kuma mahaifiyar Maina ce, amma kada ta damu domin babu abinda zata rasa na rayuwa." Saboda kwadayi irin na iyayenta da son abin duniya, suka amince aka kulla kome. Lokacin da iyayen suka gaya mata, kamar zata yi hauka, amma da suka gaya mata reason insu, sai ta ga meye a ciki. A hankali labarin ya fita waje, inda kawayenta suka nuna mata kuskuren abin da tayi, amma ta shafawa idanunta toka ta ce batai kome ba. A haka maina ya kuma zuwa ya musu hidimar kamar ba gobe, amma basu gaya masa ba, sai da zai tafi take kukan munafunci. Duk ya damu bata gaya mishi ba har ya bar garin. Maman Jasy me suna Sakina, ita ce tayi breaking silent da gulmar da ake a cikin unguwar ta zo har gidansu Ayrah. Ta samu Maman Ayrah ta ce mata. "Yar uwa abin da kuka aikata Allah ai tambaye ku, domin kuwa babu adalci a cikin wannan lamari,. Kusan san kun bawa Ubanshi aurenta ya zo ya muku hidima!" Cikin masifa da bala'i . "Don Allah ya bawa yata mijin kece reni shine zaku fara mata hassada, waye bai son cigaba? Tow anyi din idan kinyi zuciya ki bashi yarki." Da wasu kalamai marasa dadi har da mata gorin arziki, wannan abin ya mata ciwo, tasan Jasy tana da wanda zata aura dan kawunta. Aliyah ce ta fado mata a rai. "Idan ina numfashi sai na tabbatar miki da cewa Maina ba zai yi rashin mace ba, in sha Allah." Haka kuwa ta bar gidan, bata yi shawara da ko iyayen Aliyah ba, sai da ta bari anzo tafiya da Ayrah ta samu wakilin masarautar Baihak tare da niman alfarman iyayen Aliyah, kasancewar mutane ne masu mutuncin da sanin ya kamata, sannan yadda takewa Aliyah hidima kamar ita ta haife ta, yasa tana gaya musu bukatarta, basu ji dadi ba amma saboda karanci irin na larabawa, suka ce sun bata wannan damar tayi yadfa take so da Aliyah. Don haka ba tare da ta bari Maganar ta futa ba, aka daura auren Aliyah da Maina, tare da goyan bayan Halifa Abu Ammar. Shi kuma ya kira King AbdulMutallab ya gaya masa, ya ce ayi kome. A can masarautar dama an tsara haka, tunda har Maina ya so yarinyar dole a raba su, domin ana mishi kallon Future King don haka Dowager ta gayawa Uban matukar ya isa Yemen ya lalata niman Maina, domin ceto rayuwarshi. Koda suka zo sai suka samu faduwa tayi daidai da zama, domin kuwa iyayenta makwadaita ne. Haka aka kawo ta Kingdom din, Queen Hamidah ta jata a jiki kamar me, haka yasa take jin matukar kaunar Queen Hamidah. Sai dai alqawarin da Hamidah tayi Ayrah zata zo taci kwadayinta amma ba zata tab'a samun damar haihuwar jinin gidan ba, domin idan ta haifa zata iya yunkurin kashe King dalilin da yasa a tsawon shekaru goma sha daya ake watsar mata da yara kenan. Aliyah da aka kawo ta,wurin Ummimi aka kaita wannan shine rabon da ta kuma saka Ayrah a idanunta ya dauki kusan dogon lokaci. Ammar shi ya dauki Aliyah har Texas ya kaiwa Maina ita, ya zauna ya warware mishi kome, ai kuwa tsallake ta yayi ya diro Baihak a daren da ya zame mafi munin dare, ana tsakiyar ruwan sama ya shigo masarautar. Yasan tunda ya ga fadawa a ko ina Sarki yana fada. Yana shiga fadar ya ga wasu mutane a durkushe. "King AbdulMutallab mun kasance masu maka hidima, ka sani kashe mu abu me sauki ne, sai dai abin da zai dawo tabbas ba zai zo maka da sauki ba, kamar yadda kuka boye nufinku da sharrinku zata zo ta watsar da kome ka.." yanke mishi wuya aka yi, ya zube yana shure-shure. Akan idanun Maina King ya kashe mutane goma a daren, wannan abinda ya gani ya fahimci Babanshi yayi nisa. Mutumin karshen da aka kashe ya jyya yana kallon Maina dariya a fuskarshi ya ce mishi. " Na hango gobe me kyau, dauke da dambarwan zubda jini, jikata zata zo.har nan ta kashe kowa soyayyar da kuka kashe zata farka daga ranar da ta saka kafarta kiyayyar da kika jinginawa kanku zata mutu, na rantse da abin da nayi imani da shi Uwargijiya ta kare ta a ko ina zata zo zata rusa daular. ...." Shi kan fille mishi kai aka yi, ya fadi can yana kyalkyalewa da dariya sannan ya daina motsi, rud'ani tashin hankali wanda bai tab'a gani ba, haka yasa