← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 115

Sashe 61

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya dauki rawa. "Kece kika tab'a hannun?" Girgza kai tayi, "tow waye? Kinsan idan aka gano ke Matsafiya ce ba zaki sha da dadi ba, da al'ummar Baihak? Sannan." "Ni ban ni ba ce!" Ta fa a tana Juya tea dinta. Zamewa kofin tea yayi ta ce mishi. "Ziyazul!" Cak ya tsaya ta dauke shi a iska ta maida shi saman table din. "Me kika yi kenan?" D'ago kai tayi suka yi ido hudu da Hilda domin tana zuwa kwayar idanun Layla ke koma light blue. "Ai ta gaya maka ba ita ba ce." Ta fada tana lashe bakinta. "Bana ce kada ki kara zuwa ba?" "Idan nazo me zaka yi? Ko ka fara jin haushina ne akanta?" Ha e rai yayi ya nufeta, zama tayi saman table din kitchen din, kafin ya iso tayi wani uban tsalle ta rungume shi."me yasa kike dawo?" "Dama mun yi al awarin cewa ba zan dawo ba ne?" Ta fada tana kai bakinta kunnenshi. "zan dawo kuma zan cigaba da dawowa, ga matarka da kanwarka!" Ta fada tana fashewa da dariya, yana jin takunsu da muryan Bahi tana magana da sun shigo kenan idanun...... *Ga masu bukatar tallata musu hajarsu kofa a bude take a tuntubi wannan number :08130269641* *Hilda ta ce fansarta kad'an ne, da gaske tono kiyayyar da yake tattare da kashin Rihanna zai dawo da kome? Me Hamidah take shirin aikatawa? Gaskiya book din nan da na kudi ne da naci kazar yahuza soya da Rufaida yoghurt saura na zo da paid book ku juya min back kuna d'add'aga min shoulder [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _______________34 Cak suka kafe a wurin kamar basu raye, "na gaya maka gaskiya ina son ta san gaskiyar lamarin nan amma na lura kai naka matsalar boye shi kake, ya kenan idan ta san boyayyen al'amarin nan!" Ta tsaya tana kallonshi kafin ta kyalkyale da dariya. "zan kyaleka amma ga sani, zan dagula maka lissafi har sai ka ji ka tsani kanka, sai na mai da ka mafadaci kamar yadda ba zata ba, ina gefe ina murmusa maka." Bai ce mata kalla ba, ya juya zai bar wurin ta sha gabanshi tana zaga tsakaninsu Aliyyah da Bahiyyah tana dariya. "Dube babu kome a ransu da kansu sun manta kome ko na bar musu abin da suka gani ne?" "Maina kana kwadayin jikin Layla ni ina kwadayinka ya kenan? Kawai ka rab'e ni sai nayi tafiyata." Banza yayi mata ta kara leko shi tana fa in." Da gasken gaske nake gaya maka fa" ta fa a tana dafa kafadarshi tana dariya. "Hilda!" Ya kira sunanta a hankali yana me rike hannunta, cikin murmushi kanta na hayaki ta zauna. "Zan so mu dawwama a tare da ke, amma maganar gaskiya sai dai ki daina zuwa a jikin Layla ni kuma zan ware mana lokaci sai mu raba dare muna shagali!" Shiru tayi tare da fisge hannunta tana kallon shi, "yaudara ta zaka yi kamar yadda ya yaudare ni." Mikewa yayi yana fa in. "duk ranar da kika shirya zamu yi magana yanzu ki fita a jikin ta!" Shiru tayi kafin ta ce mishi. "idan nayi nazarin abin da kace zan nime ka." "Kada ki damu ni zan bukaci ganinki!" Daga haka ta wuce akinta, tana barin wurin su Aliyyah suka farka kamar masu barci, "tafiya zamu yi fa, tow mu kan ,mu tafi " suka nufi hanya babu wanda ya tuna me ya faru. Sai da suka shiga motar da zata kai su, basu fita ba sai ga Mijin Bahi suka nufi airport. Abubuwa dayawa suna faruwa a lokacin nan, musamman da Maina ya kara macewa Aliyyah kamar zata maida shi ciki, sannan baki aya bai da wani nutsuwa sai nata, kamar wanda ta rufe mishi iyaka, domin ko asiri ya mishi sai haka, a haka Layla ta dawo hutu, sau biyu suka ha u. Shima ya kawo Sainah da Nuri darling, dariya Deenah da Radiyyah suke mata, musamman yadda take musu hidima. -Baihak duk inda ake tsammanin zasu ga kabarin Rihanna babu shi babu labarinsa, sannan abin da ya kai aka gayyato masu bincike da tono abubuwan da ke karkashin kasa, amma ba a samu ba. Shiru Queen Hamidah tayi tana kallon kasa, kafin ta ce mishi. "Ita din jininmu ce, don haka a saka idanu a cigaba da bincike." Bayan fitarsu Malik da Wazir Abu Ammar suka shigo zama suka yi sannan suka gaida ta d'aga musu hannu tayi tare da mikawa Malik ruwa. Amsa yayi yana kallonta. "Ruwan me?" "Ka sha!" Ba musu ya shafa, ko minti daya ba yi ba, ya yanki jikinshi ya fadi jikinshi yana rawa. "Ka auke shi zuwa angarenshi, yau ka zuba idanu akanshi." -A can Washington DC kuwa, Nuri tana wasa da tap dinsu, dukkansu a parlourn kawai suka ga Nuri ta fadi kasa. Tana wani irin girgiza. "Nuriyya!" Suka kira sunanta suka yi har Madam Helin ta zo suka dauke ta zuwa dakin Aliyyah da take waya tana ganinsu ta katse wayar suka fita baki aya, sai da suka nufi asibiti inda suka kira Maina, bai jima ba ya Isa asibitin, ya samu ana ta fama da ita. Shiru yayi na few seconds kafin ya tambayi dalilin ciwon aka gaya mishi, yaso ya gayawa Ummimi amma sai ya fasa, ya tattaro Yaran da Aliyyah suka dawo gida, sannan a bangaren guda tunani yake ya gayawa Layla ko yayi shiru, tow amma meye na nashi da zai gaya mata. Kawai sai ya share wasa wasa ciwon Nuri ya fara wuce tunaninshi, don haka ya kira Ummimi ya gaya mata. Kamar yadda ya gaya mata haka ta mishi bayani yadda Malik yake ciki, yana office ya nufi jikin Window yana kallon waje. Juyawa yayi ya kalli kujeranshi sannan ya taka har gaban kujeran ya dauki abin da zai dauka ya nufi waje, bai zarce ko ina ba sai makarantarsu Layla, bude kofar yayi ya shiga har office din principle dinsu ya mata magana aka kira Layla yasan zuwa wannan lokacin Aliyyah ta koma gida, yana zaune ta shigo cikin shigar makaranta skirt ne sai dogon legis da ya bayyana sililin siraran kafafunta fararre tass, a hankali ta gaishe su sannan ta koma gefe, "Yallab... Papa!" Tayi saurin sauya abin da zata fad'a saboda kallon da ya mata. "Gani!" "Thank you so, zan dawo da ita." Gyada kai matar tayi suka fita, har wurin Motarshi ya bu e ya shiga ya koma ta daya bangaren ta shiga. Ta zauna tana kallon waje, har suka bar makarantar bata yi magana ba shima kuma bai ce kome ba, sai da suka nufi asibitin gabanta ya fad'i ta juya tana kallonshi idanunta cike da kwalla. "Me ya samu Nuri darling!" Yadda ta furta darling din ya saka shi jin yarrrrr yaji tsigar jikinshi ya mike, juyawa yayi kalli bakinta da ya furta darling din, ashe ya sake kan motar da sauri ta kai hannunta kan motar tare da kallon hanyar. Ajiyar zuciya ya sauke don ma titin babu mutane sosai. Kallon hannunta da yake kan hannunshi, yayi sannan ya dubeta gabanshi yana wani irin bugawa, jikinta sanyi kamar ba cikakken bil adama ba, Ganin yadda jikinta yake rawa ya ce mata. "Nutsu!" Juyawa tayi tana kallon fuskarshi. "Ya isa babu abin da ya faru!" Ya fadi haka Idanunshi yana kan hanya, janye hannunta tayi da yake jikin sanyin ya mishi yawa, bai san ya aka yi ba ya tsinci kanshi da furta haka. "Jikinki da sanyi ba ki da lafiya ne?" Dunkule hannunta tayi tana kallon asa, har lokacin bata bashi amsa ba. "It's ok!" Ya fa a tare da niman wuri yayi parking a cikin asibitin, kallonta yayi ya ce mata. "Nur ce bata da lafiya!" Bata yarda ta kalle shi ba, asalima kallon waje take, tana gyad'a kai. Har cikin asibitin suka shiga tana bin bayanshi. Tun kafin su shiga dakin ta ce mishi. "Dakata!" Juyawa yayi ya kalleta. "Bari na shiga ko" bata hanya yayi tana shiga cikin dakin Nur tana bu e idanu. "Nuriyya!" Ta fada tare da nufar gadon, ta dafa hannunta. Lumshe idanun tayi tare da dafe hannun Nur din, a hankali wani bakin hayaki yake fita daga jikin yarinyar yana fita sama, sai da ta zuke gubar sannan ta koma kujeran da yake dakin ta zauna tare da niman faduwa. Jin karar kujeran yasa shi ya leko, ganin halin da take ciki ya sa shi matsawa wurinta da sauri. "Kiranye suka mata, sun san ba zaka zo don kanka ba, shine suka yi amfani da Nur. Amma na raba tsakaninsu da Nur in. Amma dole wata rana ka koma Baihak, akwai wata gaskiyar da zaka iya samu." Daga haka ta mike tana tangal-tangal, kamar zata fadi ya tare ta, ta fa a kirjinshi. Dumin da yaji a kirjinsa ya sashi lekawa. Jini ne bakinkirin da yake fita ta hancinta. Bai yi wata wata ba, ya fitar da ita daga asibitin baki aya. Tafiya yayi me dan nisa kafin ya isa wani apartment. Anan yayi parking sannan ya fito ya zaga ta inda take ya fitar da ita, ya rungumeta har cikin elevator, sai da aka kai su har hawa na biyar sannan ya riko hannunta har zuwa kofar dakin da yake dauke da rubutun room 567, ya saka katin kofar ya bude a hankali ya shiga da ita, sai da ya kunna wutar dakin, sanan ya kwantar da ita a saman sofar din da yake parlourn. Ya nufi kitchen din da yake a ha e da parlourn ya ha a mata maganin da Hafsatul ikram ta tab'a gaya masa. Sannan ya zo ya d'aga ya saka matasai ya jinginata, ya fara dura mata. maganin na shiga cikinta tana bu e idanu. Juya kai tayi tana mika ta ce mishi. "Gidan nan yayi min! Duk da nasan ala arku dole a nime mafita." "Hilda kike?" Juya idanu tayi kafin ta ce mishi. "Duk abinda ya maka." Gyara zama yayi sannan ya ce mata. "Look meye ala arku da Layla?" Wani shu'uman kallo ta mishi sannan ta ce mishi. "A dake ni a hanani kuka, jikin Layla ba iya ni nake bukatar shi ba, hatta kasusuwan da Hamidah ta saka a tono tana
Chapter 61 · 0% Book details