← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 115

Sashe 102

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi amfani da damarshi kafin wayewan garin washi gari, ya saka an dawo da Malik, wanda yana cikin halin koshin lafiya. Sannan ya tura Salahudeen ya dauko masa su Ummimi da Annah da kuma Sainah. Kwana biyu gidan da masarautar ya koma kamar baya, sai dai yawan gulmacce-gulmacce da ake yi a tsakanin bayi da sauransu, sannan Malik kai tsaye ya dakatar da wasu mutanen fada, ya kuma nad'a Ammar a matsayin babanshi. Ummimi ta koma zaman asibiti saboda Aliyyah da take fama da cikinta. Kwana biyar a tsakanin aka sallame Hamidah, wacce babu wanda ya gaya mata abun da yake faruwa kawai tana dawowa ta ga Anna wacce dayawan mutane basu san tazo ba, ranar kasa barci hamidah tayi zuwa dare ta wuce wurin Falwa. Lokacin da ta shiga ta ga gawan Gorunfa, Layla tana tsaye akan Falwa da yake ja da ciki. "Ni fa ba xan maka kome, kai da hannunka zaka yi kome kamar yadda ka saka hannun ka kashe min iyayena haka zaka yi kome da kanka! Barka da zuwa Hamidah." Ta juya baya tana kallon Queen Hamidah. Ja da baya tayi tana nuna ta da yatsa. "Waye ya kawo ki nan!" Farcenta take kallo tana hurewa. "Waye ya gaya miki ana niman izinin zuwa irin wannan wurare..." "Kwammmm!" Ta ji a tsakiyar kanta, zubewa tayi akan gwiwarta tana juya kanta. "Kasan abin da kayi? Zuburarr!" Makashi da kasa aka yi. Ya sune ta kai minti ashirin a wurin tana ganin bibiyu, wani irin guguwa ta ji yana tashi kafin ta ji dariyar Hamidah. "Je ki can akanta aka kashe miki rayuwa je ki." Yunkurawa Kalfana tai tana me tashi sama kamar tsuntsuwa, ta dirko gaban Layla. Kafin ta shake mata wuya. " Kashe ta ki dauki gangan jikinta." A fusace ta juya ga Queen Hamidah tana dalla mata harara, "Bana kisa haka kawai, sai da dalili sannan na gaji da zama a mataccen gangan jiki. Ina son ma rayu a rayayyen gangan jiki. Duk yadda aka yi yarinyar nan tana da nasaba da Wada!" Ta shake bakin Layla hayaki ya fito daga bakinta ya shige bakin Layla ta zube a kasa, gawan Kalfana ya fadi tare da kamawa da wuta. Yadda ruhin yake gudu a jikin Layla da jininta yasa ta kara fahimtar wacece Layla, ganin haka Queen Hamidah ta saka mata karfen da ake daure Kalfana hannunta da wuyarta tana me watsa mata wani farin hoda. Sannan ta nufi wurin falwa ta tashe shi, tana nuna mishi abin da tayi. Murmushi yayi mata sannan ya ce mata. "Kin kyauta sosai sauran aikin zamu barwa Tirsila mu ga zata iya ko ba zata iya ba!" "Wannan shine magana kuma naji dadin haka!" **** Maina tun da ya dawo yake niman Layla,amma babu labarinta. "Ya kina gidan nan baki san lokacin da ta fita ba? Aliyyah!" "Ka ajiye ni gadinta ne? Ko sandar kiwonta ka bani na saka mata idanun!" "Amma!" "Look bana son tashin hankali ina fama da kaina!" Ta wuce shi tana dingishi. Wannan abin ya mishi ciwo ba ka an ba, haka yasa shi nufar bangaren su Anna babu Layla duk inda ake tsammanin tana nan babu ita. Kiran Ammar yayi ya gaya masa halin da ake ciki shima yazo ana ta nimanta. Wasa gaske aka nime Layla aka rasa har gari ya waye ana nimanta. Queen Hamidah tana sane da kome tayi fuska kamar bata san meke faruwa ba. Bude idanu tayi tana kallon Falwa da yake tsaye kanta zigidir. Murmushi yayi yana me jan kafarta, "me zaka aikata?" "Nima ina son naji abin da kowa yaje ji ne. Haka nayiwa Jamimah, aka kashe ta." Lumshe idanu tayi tana fa in. "Tabbas ba kai ba zuriarka ma zasu sama tabb'abu!" Kai hannunshi yayi gaban rigarta "me zaka yi?" "Na gaya miki!" Murmushi tayi kafin ya furta wani kalma an yanke mishi hannun an cilla can ai kuwa ya fasa wata irin ara. Mikewa tayi tana me jan sarkan da suka saka.mata a hankali suka yi ta narkewa kamar ara akan wuta. Baki aya sarkan ya tsinke. Nuna mishi hannu tayi juya take aka sake maka shi da bango. Kafin ta nuna sarkan nan ya daure shi aka.ja shi har gabanta. Mikawa tayi tana wata irin mika baki aya kasusuwan jikinta suka amsa, murmushi tayi wani kas da hannunta, kafin ta sauke hannun an kwashe mishi gabanshi baki aya ihun da ya saka wanda ya saka shi suma baki aya, sannan ta nunawa sarkan hanya. "Ina baka umarni da kalamai na ka kai shi har bangaren Hamidah wannan shine kalamai na." Daga haka ta kalli ilahirin cave in. "Kome na cikin nan ya kone ya zama kamar baa taba amfana da wurin ba, sannan a shafe min kofar shiga yadda wani bil adam ba zai yi tunanin aikata laifin da aka yi ba." Kafin ta dafa bango ta b'ace ai kuwa tana barin wurin wuta yana kamawa gadan-gadan. Ana cikin jimamin rashin ganin Layla sai ga wulakantaccen jikin Falwa ya nufi bangaren Queen Hamidah sarka na jan shi a guje kamar zai tashi sama. Wannan al'amarin ya girgiza kowa domin sun san matsayin shi a wurin Queen Hamidah, haka yasa aka fara kus-kus abin ka da masarauta da bata rena gulma. "Queen! Queen!!!" Bahira ta kwala mata kira fitowa tayi ganin Falwa a wannan halin yasa ta zubewa tare da cewa. "Ku fita min da shi waje!" Yadda tayi maganar da karfi yasa Falwa ya farka yana jin tana ihun a fitar da shi. "Guduna kike Hamidah?" Ya fada da karfi ai kuwa ta koma ciki ta rufe kofar tana cewa a fitar mata da shi. "Har kece xaki guji abokin cin mushenki?" Inji Layla da take zaune a tsakiyar parlour akan iska....... (Me kuke tunani? Layla ce ko Ruhin Rihanna? Sunan wani labari wai Ruwa biyu ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/4, 10:48 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________70 Murmushi dauke a fuskarta ta ce mata. "Yanzu meye laifin Falwa ko shima amanarshi kika ci?" Da wani irin zafin Nama Queen Hamidah ta fara arin bude kofar amma kofar ya i bata ha in kai, "zan tafi amma ki sani daga yau babu ke babu zaman lafiya, zan ta bibiyarki ina fito miki daga ko'ina na duniya, xan buwaye ki har sai kin bayyanawa duniya kalarki zan sakawa raina salama!" Daga haka ta b'ace. A firgice Hamidah ta bude kofar ta zuba da gudu. Ganin tana gudu yasa aka fara kokarin tare ta, amma ina sai da aka yi da gaske aka rikota. A can kuwa Maina suna ta niman Layla. An kira shi an gaya mishi abin da yake faruwa da Hamidah ya ce shima yana niman matarshi ce bai da lokacinta. Lokacin da ta bayyana a dakinta, kwanciya tayi, Domin bata jin jikinta yana mata dad'i, wani irin yanayi take jin ta kamar ba ita ba haka yasa tunda ta dawo ta kwanta bata kuma farkawa ba. Aliyyah da Yaranta suna parlour amma basu san tana gidan ba, sai da Maina ya shigo ya zuba musu idanu. "Papa har yanzu ba a same ta ba?" Inji Sainah. Jinjina kai yayi yana fa in. "Eh Sweetheart!" Ya nufi hanyar dakin, "Allah ya bayyanata a duk inda take!" "Allahummah Amin!" Daga haka ya shige, yana kuwa barin parlour Aliyyah ta mari Sainah sai da medical glass dinta ya fadi. "Ina wasa dake ne?" Girgiza kai tayi tana daukar glass dinta, domin har yau dishi-dishi take gani, bata wani gani sosai, shure glass din Aliyyah tayi Nuri tayi maza ta dauka tana fa in. "Mum kin manta bata gani ne? Idan da Mamee Layla ce ba zata yi mana haka ba." Mamaki ya cika ran Aliyyah, tana kallon Yaranta da suke yabon yarinyar me take basu ne kai ko asiri tayi musu? Rike hannun Sainah Nuri tayi suka bar parlourn, cikin sanyi jiki ya zube akan kujera. A can dakin Maina yana shiga ya zuba mata idanun. "Layla!" Bude idanunta tayi ta zuba mishi kafin ta koma ta rufe su, ita aya tasan yadda take ji domin jikinta har wani turiri ya e, kiraye-kirayen waya yake har zuwa wani lokaci, takawa yayi ya zauna tare da tab'a goshinta, yayi zafi rau. Cikin gaggawa ya fara bata taimakon da ya dace, sai dai tunda yake bai tab'a ganin abin da yake gani akan Layla ba, domin kuwa fatarta ne yake duhu daga farar fata zuwa baka wuluk. Sannan gashin kanta yana jemewa daga baki zuwa fari sol. Duk wani abu na jikin Layla sai da halittarshi ta sauya, fuskarta kuwa ta koma kamar ta tsofin da suka shafe shekaru sama da ari. Kwayar idanunta kawai zaka kalla ka san cewa yarinya ce amma kome nata ya koma na tsofi. Wayarshi ce tayi ara ya dauka, "ka shigo dakina kawai dashi!" Ya kashe wayar yana kallonta da dukkan zuciyarshi. Shigowa Doctor Jafar yayi yana kallonta ya ce. "Innalillahi wainnalihir rajouna! Layla Aisha!. Kece haka?" Hannu Jafar ya kai ya tab'a jikinta yaji zafi rau, hawayen da yake dannewa ne ya zubo mishi. Tunda yazo yake arin niman jijiyar da zai saka mata ruwa amma babu, wani irin tsoro ne ya cika ranshi. "Yarima ko zaka bari na tafi da ita ne?" "A'a kayi hakuri ba zan iya nisa da ita ba!" Ya fada yana kara rike hannunta. Kiran Malik ya shigo mishi anan yake gaya mishi halin da ake ciki, babu bata lokaci sai gashi tare da Anna. Lokacin da ta ga Layla fashewa da kuka tayi tana tausayawa halin da take ciki. "Yanzu me za ayi?" "A ganina a kaita asibiti!" "Wannan ba ciwon asibiti bane Ammar, wannan ciwon aljanu ne da aka yi imani da su!" "Mtseew! Waye ya gaya muku ciwon aljanu ne? Yadda kuka.ga na bayyana a wannan gangan jikin babu inda zani domin na samu jiki me dad'i da kyau, an haife ta a daren addara an kashe ni a daren addara taya kuke tsammanin ba zan dawo mazaunina ba. Labarina ya shafe daga lokacin da na kawo dauki Baihak, sabuwar ni na fara sabon rayuwa a daren da aka kashe Zafir da ahalinsa, Jafar ina ka
Chapter 102 · 0% Book details