Sashe 28
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* __________________ Gyara dakin aka yi, Haeda tana buga bayanta, har tayi shiru amma ba wai ta daina kananun kukan ba ne, haka suka kwana cikin rigima da rikici wanda ya ha a da zazza i me zafi ya rufeta, haka suka yi ta fama da ita gari da ya waye ta suma ya kai sau uku. Saboda zazza in suma mutanen garin ba aramin damuwa suka shiga ba, domin yadda take suma tana farkawa kamar ba zata tashi ba, magani sosai suke bata. Almost five days Layla bata san waye a kanta ba, domin zazzabin yayi zafin da ya tab'a brain inta, koda yake ba zazza in ba ne kawai asali firgici da abin da ya faru kaka Jami yafi kome bata tsoro da tsayawa a rai, haka ta kwashe sama da sati hu u, kafin ta ji sauki sai dai zuwa yanzu Layla me kiriniya da aka sani ta zama Layla shiru shiru, idan ta zauna a wuri guda zata iya awa biyar bata motsa ba, kawai kome ya tsaya mata cak, ganin yadda ake damuwa da halin da take ciki don wani lokaci sai Haeda ta bata abinci a baki, amma Layla ta zama kamar ba ita ba. Dafa kafadarta Haeda tayi tana fa in. "Abincin ya huce Laylatu na!" D'ago kai tayi tana karantar fuskar Haeda. "Yaushe damu bar garin nan?" Cike da mamaki Haeda ta kalleta. "kina son mu bar garin ne?" "Eh!" Ta fa a tana wasa da yatsunta. "Akan me?" "Ina jin tsoron kada wani abu ya faru da su ne, domin ina jin kamshin wani abu na daban." "Ina zuwa to!" Haeda ta fita can sai gata tare da wasu mutane biyu, "Layla kika ce kina jin kamshin wani abu?" "Eh mu bar nan, sannan idan da hali ku yi kaura kafin faduwar rana, don suna gab da cimmana!" Daga haka tayi shiru tana kallon kasa, "Shi kenan zamu yi yadda kika ce, kema ai samu tafi dake ne?" "A'a tafiyarmu daban da ku." "Muje dai kawai." "Nace a'a tafiyarmu daban da ku, ban shirya ganin tashin hankali akan mutanen da suka bani damar sake rayuwa, Bana son na rasa kowa a cikinku. Ku tafi nima zan tafi ne." Mamaki dankare a fuskarsu, bata shirya ganin tashin hankali ba? Layla ta dauke su kamar rayuwarta ne, fita dattawan suka yi yaron da ya kawo ta ya shigo. "Me kika ce?" Bata kalle shi ba ta juya kanta, haka ya gama tsayuwarsa ta fita, Ravi ya shigo yana me kallonta ya ce mata. "Zan biki, kuma zan zama me biyayya a gare ki har karshen rayuwata." "Ki dauki duk abin da yake naki, mu tafi zamu koma Baihak ne!" "Layla!" Haeda ta kira sunanta a firgice. Murmushi tayi tana fa in. "Zan koma baihak ki zauna anan din, Ravi muje!" Ta mike itama, tana fita itama Haeda ta biyota, kallon mutanen garin tai ta ce musu. "Idan kun gama had'a kayanku, ku bi bayan wannan dutsen, babu wanda ya isa ya cimmaku, kada na rasa koda mutum daya a cikinku na roke ku" mun miki al awarin haka. Daga haka ta nufi wurin shugaban kauyen ta ce mishi. "Ka kula da al'ummarka." Daga haka suka bar wurin, tafiya suke basu juya ba, Haeda kan kuka take domin ya saba da mutanen garin, haka suka yi ta tafi tun sha biyun rana, -Tunda Falwa ya gayawa Queen Hamidah Layla tana raye, har da kauyen da aka kaita, ta saka aka shirya farmakar garin tsakiyar dare, sai dai basu san cewa duk shirinsu ita Layla din ta sani ba, a yadda suka tsara har da Tirsila domin ita ce kawai ta san Layla, don haka bata sake Sanaya ta san inda zata ba, tayi futarta daga gidan. Sai dai duk shirinsu ita Layla ta shinshino haka, koda suka isa sun samu garin babu kowa, wannan abin ya basu mamaki domin garin kamar an yi ruwan sama an auke, babu al'amar mutane sun tab'a koda rayuwa ne a wurin, haka yasa suka juya da bakinciki, suka ajiye Tirsila a gida tana shiga Sanaya ta ce mata. "Ina kika je? Kin samo Layla ce?" Domin buge kanta da dutse da Yara suka yi, yasa mata wani irin dimuwa haka yasa take wani abu kamar shashasha, can tayi abin masu hankali can tayi na wawaye. Wannan abin yana matukar yiwa Tirsila ciwo, domin kuwa ta saka buri a kan Sanaya, haka yasa take bata magani a hankali yadda babu wanda zai fahimci ciwonta. -Labarin da ya isa kunnen Queen Hamidah, abin ya bata mamaki amma sai ta shanye mamakin ta yadda ba za a fahimci haka ba, ta nuna ai ba kome. Tunda aka sallame Malik ya dawo, taki mishi maganar iskancin da Maina yayi mata, asalima sai ta fahimci shima kamar Maina ya tsula mishi hali ne, don yazo faka-faka da zancen Suhana Queen Hamidah taki amsar maganar yarinyar haka kawai take jin kamar yarinyar ba don Allah take tare da Malik ba, don haka ta ce bazai maida ita cunconbine din shi ba. Wucewa akinta tayi, ta zauna tana tunanin me zatayi. Ga Khamilah tana gidan Salahudeen haka yana nufin babu wanda yake tare da ita har shi Malik din, shiru tayi kafin can dare da ya raba, ta nufi can cave din, tare da bukatar a dawo mata da ikonta da danta, sai da aka auki lokaci, kafin gorunfa ya fito, "ki yanki jikinki, jinin zaki bawa gorunfa sauran aikin ki saka idanu!" Haka ta yanki hannunta, jinin na d'aga dodon ya shiga lashewa yana wani irin gurnani, yaji dadin haka. "Ki tafi gobe Khamilah zata dawo, abubuwan da kike ganin Malik ya daina zai yi sama da wanda yake yi a baya, mulkinku da yake tangal-tangal zai dawo daidai ki saka idanu zaki sha mamaki!" Murmushin mugunta tayi tana jin like karfin mulkinsu zai ninka na da can baya, haka yasa take murmushi bata damu da jinin da take zubarwa ba. Ta bar ashin asan. Washi gari, da sassafe sai ga Ummimi ta dawo, gidan Malik yana ganinta ya shiga balbaleta da masifa.-Daga nan Layla suka ci gaba da tafiya har na tsawon kwanaki masu yawa, kafin suka isa masarautarsu Ummimi, kafin su isa suka fa a tarkon masu sayar da bayi, haka yasa aka wuce da su cikin masarautarsu Ummimi, a lokacin da aka kaisu kai tsaye ita Layla aka wuce da ita bangaren Matar Yayan Ummimi wato King Khamil, domin shine sarki a yanzu, mahaifinsu ya rasu tun bayan haihuwar Yan biyu, sai aka bawa Yayan Ummimi. Haeda kuma ka wuce da ita wurin Maman Ummimi Sultanah Dilshah Khatoon, mace ce mai kirki da adalci, a lokacin da aka kai Haeda tana kuka domin tana tsoron kada a rabata da Layla, cikin kulawa ta ji bayaninta don haka ta kira Jakadiyarta Amimah ta ce ta je ta saka Bazlah ta dawo da yarinyar nan, Allah ya ke da ikon raba d'a da mahaifi ba mutum ba. Dake ana mulki na adalci da tausayi, babu musu ita kanta Bazlah ta zo har wurin Sultanah Dilshah Khatoon, tayi ta bata hakuri. "Umma wallahi ban san yarinyar tare da mahaifiyarta, take ba don Allah kiyi hakuri da ba zan raba su ba." "Na sani haka da ba zai faru ba, kin kyauta da kika dawo mata da ita, ta ce daya saurayin an tafi da shi, ki tabbatar ba ayi nisa da shi ba, ya zauna da su Arab." "In Sha Allah, Ummana!" Daga haka tayi mata sallama ta bar parlour. Tun ganin Layla Sultanah Dilshah Khatoon taji kaunar yarinyar ya cika ranta. "ya sunanku?" "Layla sunanta, ni kuma Hardah!" "Masha Allah, Ummu Layla, Jakadiya ki kai su bangarenku,gyaran daki da wasu abubuwan zaku na min, Layla ke zaki na zuwa wurin Bazlah kina mata nata aikin amma ki tabbatar kin zo nan na ganki saboda mahaifiyarki!" Gyada kai tayi sannan suka fita, ana kaisu bangaren bayi. Saboda yanayin kyan fuskar Layla yasa Haeda shafa fuskar, take wasu irin kananun kurajr suka feso. "Me yasa?" "Tunda kika kawo mu nan, babu bayani akwai shirinki, sai dai bana son wani ya kalli fuskarki yayi tunanin kina da muhalli a nan ne " murmushi tayi sannan suka shiga har babban dakin da aka basu da wurin kwanciya, da kome da kome. Haka suka cigaba da rayuwa, sai dai dake Layla yarinya ce akwai matar jikan gidan, Ubaidullah, ta haihu sai aka tura musu Layla tana renon Babyn, haka yasa Layla ta shiga cikin zuciyarsu, musamman iyayen Yaren da ita kanta Matar sarkin Bazlah, cikin wani irin kauna suke mata hidima, domin Ubaidullah ya jima bai haihu ba, kusan shekara goma kenan, Allah ya kawo musu Yaron, satinsu Layla biyu matar ta haihu, karewa ma nurse din da masu kula da me jego daga kasar waje aka kawo su, sannan ana haihuwar Yaron wani dan banzan Aljani ya shafe shi, kullum kuka gashi yaki haiba irin na jarirai, ranar da Sultanah Dilshah Khatoon zata barka ta dauki Layla ta rakata, suna tafe tana mata hiran kuruciyarta. Tun kafin su isa gidan Layla ta hango aljanin yadda ta zabga mishi harara, yasa shi b'acewa babu shiri ya gudu, suna shiga cikin gidan suka samu za a kai yaron asibiti. "Ubaidullah me ke damun yaron ne?" "Granny wallahi bamu sani ba, tun haihuwarshi yake wannan kukan da zabura." Ya mika mata Yaron har zuwa lokacin ihu yake yana zabura, "tow Allah yasa lafiya dai! Layla dauke shi kema." Ta mikawa Layla Yaron, tana amsar shi idanunta suka koma purple, haka ma na Yaron ai kuwa ya shiga jujjuya shi tana murmushi, sai ga Yaro yayi shiru, shi kuma aljanin ya kama da wuta garin gudun ceton ranshi. Ajiyar zuciya yaron ya fara a hankali barci ya kwashe shi. "Kun ga ikon Allah ba? Tow ai kuwa baku da me kula da Yaron nan sai Layla!" Sanadin da layla ta dawo gidan da zama kenan,