← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 115

Sashe 32

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* __________________ "Mace!!!" Ya furta sau uku, irin bai kawo haka a ranshi ba, a tunaninshi zata samu sauyi d'a namiji, da zai yi hakuri da sssautawa tunda namiji aka haifa, a fusace yayo kan Ummimi da take tsaye kamar statue, ita kanta bata ta a kawowa malik zai iya fusatar da zata kai yace zai mangareta ba sai yau, baya tayi cikin sanyin murya ta ce. "haihuwa ta Allah ce, shi yake da ikon bada abin da yaso ya kuma hana abin da yaso, ni ban isa inja da ikon Allah ba, domin duk rayuwa tana kan addara, kayi hakuri nima ban san tana dauke da juna biyu ba, da na gaya maka." A yadda tayi maganar tana me sunkuyar da kai, ya kalleta a tsanake kafin ya ce mata. "Ka da na kuma ganinki a turakata, sai ranar da aka gaya min Maina ya haifi d'a namiji, kada na kuma sake saka ki a idanun sai ranar da Maina ya dawo masarautar nan, idan kin ji muryata ki boya donon xan saka a azzabarta min dake babu tausayi babu imani ficce min a gaba lusara da bata iya kula da Yaranta ba." Maganar Malik yayi mata tsauri da girma, amma cin mutuncin yayi mata ciwo, don haka ta juya tana fa in. "Allah ya baka hakuri, ya huci zuciyarka." Daga haka ta fito, a bakin kofar ta hadu da Ayrah tana murmushi, danne b'acin ranta tayi sannan ta ce mata. "Sannu ya kike?" A lalace Ayrah ta kalleta tana fa in. "Dalla bani hanya, tsohuwar guzuma!" A kunnen Court lady Ayrah ta fa awa Ummu wannan maganar, har zata shiga ta ce mata. "ki daina zuwa wurin Malik domin baki da wani amfani, kin haifi manyan yara gotai-gotai amma kike wani zuwa ko uban me zaki iya mishi oho, bayan kome ya tamushe!" Girguza kai Ummimi tayi tana fa in."Eh kome ya tamushe kam, amma ki tambaye shi duk macen da zai kwanta da ita saura na ta samu, domin nice na bare shi a leda, kin ga kenan Babu amfanin nayi kishinsa da yawa, domin duk inda aka je aka dawo. Ni zaa yi pointing da sunan Matar Abdulmutallab Hatim, Uwar Sadaukai. Dadin abin duk wanda za a haifa a cikin masarautar nan, kannen Maina ne sa'o'in jikokina." Ta fa a tana wuce Ayrat har zasu bar.kofar ta ce mata. "Ke da kika same shi yana shan maganin karfin maza, ni na aure shi ne da karfinshi da lafiyarshi. Ki shiga ki ga abin da yake sha, na shanye kome na bar muku tsufa majina!" Daga haka suka bar bangaren Malik, sai taji duk haushin Malik da take ji ya kare, domin bai isa yayi kome va, Haihuwa ce an yi ta bai da ikon maida Babyn a haifi wanda yake ba, Lady Ayrah tana shiga ta ga Malik ya zazzage ledar Men super powers, gwalalo idanu tayi wato maganar Khamilah dai gaskiya ne, saka hannu tayi ta make kofin sai da kome ya zube, dama a fusace yake kiris yake kira ya fashe, sai ga Lady Ayrah ta karasa gawar da ba nata ba, ai kuwa bai san lokacin da ya kifa mata mari ba, sai da ta fa i. "Guard ku zo ku tafi da ita, a rufe yar iska sai na nime ta." A duniya waye ya isa mishi wannan iskancin ya kyale yar banza da ita, ya daka musu tsawa a fita da ita kafin ya had'a dasu, jin haka suka fita da ita, cikin b'acin rai ta ce. "Sai ka biya abin da ka aikata." "Dakata!" Ya nufe ta, ganin yadda idanunshi yayi jajjur, dama haushin kaza ne, huce kan dami. Kallonta yayi na wani lokaci sannan ya tsinka mata mari, sai da ta zauna dirshan kafin ya ce mata. "Ku kaita airport bana bu atarta a maida ta kasarta." "Malik ka rufa min asiri ina da ciki!." Ta furta a razane domin bata ta a kawowa Malik zai mata irin wannan hukuncin ba. "na sani cikin wata guda da kwanaki, a maida ki gaban iyayenki domin zan iya sakawa a sare min kanki!" Fashewa tayi da kuka me yasa ta biyewa zuciyarta, cikin takaici ta ce mishi. "Naji amma a bar ni na dauki kayana!" "Kada ta wuce awa ashirin da hudu a cikin gidan nan, domin zan hukunta har ku." Ayrah tana ji tana gani aka tarkata shirginta zuwa Airport suka watsar da ita, sannan suka dawo, ita kuma a take ta nemi taimakon Maina tana kuka, kamar ranta zai fita tana gaya mishi abin da ya faru, ga ta da ciki don Allah ta ci albarkacin cikin jikinta tazo ta haihu a wurinsa, bata san me zata gayawa iyayenta ba ita ta manta iskancin da tayiwa Ummimi kawai burinta ta samu abin da zai kusantotta da Malik. -A lokacin da ta kira shi, yana rungume da Banafsha Prince Haisam ya saka mishi wayar a kunnenshi, duk yadda yake jin haushinta amma yaga kuskuren Malik da ya kore ta da ciki tow amma yadda Malik yake masifar ji da ita, iya abin da ya ce mata, "shi kenan" kallonshi Aliyyah da Bahiyyah suka yi, had'e rai yayi tare da cigaba da yiwa yarinyar Addu'a. Ganin yadda yayi yasa baki aya suka shiga hankalinsu. A can kuwa Malik a fusace ya wuce parlour Queen Hamidah da take rike da mug din tea, ya zauna yana huci. "Kai da waye?" Ta kai kofin tea din bakinta. "Matar Maina ce ta haihu." Ya fa a daidai ta kurbi ruwan zafin da yake da shegen zafi, ai bata san lokacin da ta buntsuro shi ba, tare da sake kofin a kasa tana zare idanu, hannunta daya na manne da bakinta da ya kone. "Sannu " ya fa a mata bayan ya mika mata ruwan sanyi, ta kurba tare da rintsa idanunta. "Garin ya haka ya faru? Khamilah da take bamu labarin cikin bata sani ba ne? Ko ta boye ne don d'anta?" "Itama bata sani ba, yanzun take gaya min wato ya boye abin ne." Kallonshi tayi cikin yanayinta me.kara birkita mishi lissafi domin baya kaunar irin wannan yanayin, cikin sanyi da murya ta ce mishi. "Allah ya raya me aka samu?" "Mace!" "Tabdijam, mace ta kuma haifar mana?" Lumshe idanu tayi abin yana dukan ranta, mikewa tayi ya ce mata. "Don Allah kiyi hakuri, wallahi nima ban san kome ba." Murmusa mishi tayi ta ce mishi. "Allah ya raya." Daga haka ta bar parlourn, tunda ta shiga dakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai safa da marwa take, zuwa yanzu ta kara tabbatar da Maina yasan cikinshi ake bawa dodon masarautar, kuma tasan Falwa ya saka masu bibiyar Aliyyah, amma taya haka ya faru. Yadda ta kagu dare yayi ta isa fadar Falwa Allah ka ai ya sani, tunda ta ji labarin ko ruwa jin shi take yana mata d'aci, dare na rabawa ita dayarta ta nufi wurin Falwa tana zuwa ta fashe da kuka. "Falwa ya haka ta faru? Matar Maina ta haihu kuma." Fyeduwa yayi ya kira Gorunfa, ya isa gabanshi yana shafa shi. "Ya aka yi dakarunka basu kawo mana labarin cikin da aka haifa ba." Gurnani yayi kafin ya kwanta yana nishi. Juyawa Falwa yayi ya ce mata. "Ban san yadda haka ta faru ba!" Dariyar Gorunfa suka ji ya ce musu. "Matukar Maina yana cikin Baihak ko da mata dubu ya kwanta ya tashi aka samu ciki zamu iya ganowa, ta hanyar Uwarshi da take tare da shi, amma matukar tazarar da yake tsakaninmu da shi ya kai tazarar da yake tsakaninshi da Uwarshi. Har abada ba zamu ji labarin kome ba. Maina yayi nisa da Baihak." "Ya zamu yi tow." Amai Gorunfa yayi yana fa in. "A hada a kayan barka a bawa Uwarshi a tura inda yake, kamar yadda aka saba." "An gama!" "Ba gamawa bane, aikin kada ya hadu da tangarda. Maina zai dawo niman taimakon mu,.a sannan zamu karasa aikinmu." Daga haka ta bar cave din, ta dawo tana murmushi. Washi gari ta saka aka hada kayan Barka, da kanta ta nufi angaren Khamilah, tana zuwa ta zaune Ummimi ta mike cikin girmamawa ta zauna a kasa. "Ashe Aliyyah ta haihu, Masha Allah ga shi a kai musu, nawa kayan barkan waye ma zai je?" "Jakadiya ce zata!" "Ke fa?" "A'a sai bayan an kwana biyu zan je na duba su." "Allah ya kaimu, nima naso zuwa sai dai ban san yadda Maina zai karbi bakuntatta ba, ba damuwa zamu je kafin su yada wanka." "Allah ya nufa!" Haka ta dama iyayinta da makircinta, sannan ta bar bangaren Ummimi, ai kuwa cikin kwanaki biyar, Court lady ta bar Baihak ta nufi Scotland. Anan ta ga abin mamaki domin ta samu Ayrah tana buga mulkinta son ranta ga Maina ya ce a kyaleta don ciki ne da ita, abin da Maina bai sani ba Ayrah ba karamar munafuka ba ce, cikin babu laulayi amma haka zata yi ta kwanciya ta amai, baki aya ta birgita gidan da sirfa, don hauka ranar cewa tayi ita maina ya cire kayanshi ya bata, cikin yana son turaren shi, sanin yadda Aliyah take shan wuya da ciki yasa shi cirewa ya bata, Washi gari ta ce, ita girkin da yakewa Yaranshi zata ci, haka ya zuba mata taci ta lashe, dake ba ayi suna ba, sai da suka kwana goma, aka dan yi walima. Haka ba aramin burge Ayrah yayi ba musamman yadda Maina yake gabatar da Aliyah ga manyan mutane, sai taji ina ma da hannun agogo zai juya da ta dawo da alakarta da Maina. Don sai da ta zubda hawayen bakinciki da kishin Maina. Kyaututtukan da suka samu, Washi gari aka baza a falon Aliyah, tana rike da Banafsha ana ta budewa, suna kashe kudadden ciki, har aka iso kayan Queen Hamidah, a hankali aka bude aka ciro wani White gold na yara me masifar kyau, ta amsa ta
Chapter 32 · 0% Book details