Sashe 12
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
domin ganin zaman xai mata yawa, yasa ta koma makaranta, tana zaune Ummimi ta kirata a waya. "Bahi idan kin gama ki tawo gobe, Malik yazo da Lady Ayrah.!" "Tow me zan mishi? Mutumin da bai damu da kowa ba sai akanshi." Ta fa a tana tura baki. "Idan kin gama abin da kike dai ki dawo." Daga haka suka ajiye wayar, wurin karfe shida na yamma sai ga Bahi, tun falon baki aya ta fahimci Malik yazo kamshin turaren Malik daban ne, kara had'e rai tayi tana dauke kanta. Sannan ta shige falon Aliyah, yaran suka mike tare da nufarta. "Aunty Welcome!" "Yawwa My princess kuce kuna zaune anan kenan..." Bata rufe baki ba, Lady Ayrah ta fito Aliyah tana bin bayanta kamar zata kwanta a.kasa tabi kanta. "Yaranki zaki saka ko kece zaki wanke min?" Rike kugu Bahi tayi tana mata wani irin kallo me tattare da rashin kunya da rashin mutunci. "Matar Yaya me zaki wanke mata?" "Innerwear dina!" Inji Lady Ayrah. "Ai ko Ubanki bai isa ba, balle ke mayyar ku i. Matar Yaya wuce abinki watan cin Ubanta ne ya kama." Dake Bahiyyah yar bala'i ce da Balaja'u, kamar ba jinin sarauta ba haka yasa ta shiga yayyafawa Lady Ayrah rashin mutunci. Abin da ya sa lokaci guda gidan yayi tsit. Sannan baka jin kome sai muryan Bahiyyah. Ai kuwa simin-simin Lady Ayrah ta wuce dakin da take, domin ai Malik ya ce kada ta sake ya samu wani abu mara da i, kuma a cikin furuncin Bahiyyah ta ce bari ta kira Malik ya dauke Matarshi ai bata ajiye bawanta ba, amma a bangaren Aliyah tayi farincikin dawowar Bahiyyah domin kuwa ta kwace ta, asalima itama Bahiyyah ita ce ta kasa ta tsare, sai da Lady Ayrah ta koma BQ. Rashin mutuncin sai da ta godewa Allah,ga Uban sanyin da ake yi kamar zai fasa bargo. A rana na uku Maina ya ajiye aikinsa anan Scotland duk da basu so haka ba, ya musu al awarin matukar ya kara samun dama haka zai dawo gare su,. Shugaban Bakin daukar takardan yayi ya saka a kwandon shara. "Ka dauki lokacinka daga nan har shekaru goma zamu jiraka." Godiya Maina yayi tare da mishi al awarin amincewa da haka. A ranar ya musu sallama, sannan ya dawo gida, yana shigowa ya samu Malik zaune yana kallon yadda suke rufe kayan gidan da manyan mayafai. "Haisam ban gane ba, ba zaku sayar da kayan gidan ba ne?" Ya tambaye shi, "A'a gidan ai mallakar Yaya Maina ne." Tun daga nan Malik ya harbo jirgin Maina, wato ba zai yiwu ya koma Baihak ba, ya koma bai da inda zai kasance na shi. Wayar hannu Maina ne yayi tsiwa, ya wuce yana din. "Na gani ta E-mail sai dai bana son gida cikin cunkoso ai" Daga haka Malik ya zubawa Ummimi idanu da take bawa Nuriyya abinci. "Khamilah d'anki ba zai zauna a fada ba ne?" Girgiza kai tayi tana fa in. "Tunda ja bukaci ya dawo Baihak bai maka musu ba, inda zai zauna ai mai sauki ne, Malik." Ta fa a cikin sanyin murya, mikewa yayi tare da nufar Nuriyya. "Ina son Yaran nan, amma rashin Yara maza yasa basu min ba." Maina yana jin shi domin ya fito da stuff din shi yana kaiwa waje. "A haifeka a fada, a masarautar da tafi kowani masarauta karfin izza. Kazo kana daukar kaya da hannunka. Wannan wacce irin kaskanci ne haka?" "Bai auki kanshi da zafi ba, yana son kasancewa mai cikakken yanci ne ba, jinin sarauta ba." Ummimi ta bashi amsa. "Ai shi kenan, duk Abin da ya so yayi amma tabbas sai ya bini Baihak." Ummimi bata kuma magana ba, domin Ayrah ta fito, haka suka fito waje, har aka gama shirya kayansu. Bahiyyah bata gidan tace su hadu a airport. Kiranta Haisam yayi yana fa in. "Amma kinsan da wancan mutumin.muke ko? Kuma kin san zai iya cewa a tafi a barki." "Yanzu na shiga taxi!" Ta fa a tana kashe wayar, rufe gidan Maina yayi yana kallon gidan, about shekara goma yana raye cikin gidan babu abin da ya sauya sai fasalin gidan, Mr Drick Patrick yazo yana gaisa su. Mika mishi key yayi yana fa in. "A saka ido a gidan!" "Yes Sir!" Daga haka ya nufi motar, Mr Drick ya nufe shi, ya ce mishi. "Sir na gode sosai, Sir ban san me zan saka maka da shi ba, thank you sir idan da hali ka samu wani aikin Y'ata Teemi tana nan zata zo aiki a ashinka." Gyada kai yayi yana fa in. "Ina zuba idanu!" Daga haka ya shiga motar da Haisam ya bude mishi. Ummimi tana baya da Yara, shi kuma Haisam ya koma wurin kaya, suka bar gidan. Suna isa Airport suka samu Bahi tana tsaye da wani dan Pakistan, sai hira suke cikin so da kauna. Kallo daya Malik yayi mata ta shiga hankalinta, "Ga Iyayena!" Ta nuna mishi, su Ummimi, wucewa yayi ya gaida Malik , d'aga mishi hannu yayi ya kuma gaida Ummimi, cikin sakewa ta amsa. "Ga Babban Yayanmu!" Ya gaida Maina, sannan ta nuna mishi Haisam ta ce mishi. "Wannan katon shi nake bi!" Cikin mutuntawa suka gaisa, Haisam ne ya tambaye shi aikinsa da asarshi. Dan babban gida ne a Pakistan din, sai dai kuma Malik bai yi na'am da shi ba, domin baya cikin zubin tsarinsa. A haka suka bar asar. Suna isa Baihak, Halifa Abu Ammar ya isa tare da tawagar tarban Malik, yayinda Ammar dan shi da Salahudeen suka zo tarban Maina da tawagarsu. "Halifa me yasa baka gaya min sarakuna biyu ne a Baihak ba?" Sunkuyar da kai yayi yana fa in. "Tuba nake!" Wucewa motarshi yayi tare da Lady Ayrah da Ummimi dake saukar dare suka, Bahi da sauran team Maina suka bi bayanshi, zuwa Fin era estate. A can suka sauka ga kayan abinci kala-kala, kai everything so Masha Allah. Tunda ya iso ya fahimci, Malik ya gama mishi shirin talala. Domin kwanan biyu ya shiga fa a, wani ikon Allah yadda ya shiga fadar ya samu Malik bai shiga chamber ba, haka yasa shi nufar parlour Malik in da yake tare da Lady Hidayah da Abraham. "Barka da safiya!" Ya fa a yana zama, a kasa. Yana daga cikin abin da yake kara mishi kaunar Yaran Khamilah sai dai ba zai nuna musu ba, domin yasan sai su zama abin farauta, suna da tarbiyya a ko ina zai fada, idan ya hada rigimar su da Malik, tow a wurin girmamawa Malik yana kokarin bashi girman, yanzu haka ya shigo ya samu Abraham yana saman kujera yadda Lady Hidayah take zaune, amma ya zabi zama a kasa, sannan ya gaida shi cikin girmamawa. "Hmm!" Malik ya ajiye numfashi ya juya tare da dauko takardu na aiki ne da aka bawa Maina din ya ajiye mishi. "Dauka!" Ba musu ya dauka ya shiga dubawa, yana ajiyewa har ya isa kan na Baitul Malin kasar wacce take asalin garin Baihak. Yadda ya tara sauran a gefe, sannan ya rike wannan a hannunshi yasa Malik murmushi. "Wannan aikin zaka yi?" "Ih!" Ya fa a kai a kasa. "ka dawo fada!" Wani irin murmushi yayi me sanyi kafin ya ce mishi. "Yarana mata ne." Kura mishi idanu yayi, kafin ya ce mishi. "Ok kenan ba zaka dawo fadar ba?" "Ban ce haka ba, kawai bana son a cusa musu hatred ne" "waye zai cusa musu kiyayya?" "Zan tafi lokacin ya tafi!" Ya kalli agogon bangon dakin. Ya dauki takardan ya nufi waje. Yadda ya kurawa bayanshi idanu yana jin kamar ya janyo shi su yi magana irin na d'a da mahaifi. Amma ina yasan tuntuni ya rasa wannan matsayin, kallon da Maina yake mishi tun yana Yaro shi yake mishi har girmanshi. "Haka kawai kana wani bin shi da idanu, salon kurwan shi ta fada jinyar Allah ya sawwaka." Inji Abraham da yake cika yana batsewa. Kurawa Abraham din idanu yayi kafin ya ce mishi. "Me yasa ka rena ni?" "Ni kuma? Yaushe? Taya xan rena mutum irinka" ya fada yana Mikewa zai bar parlour. "Hidayah Tarbiyyar d'anki kenan!" Ai bai ji me Malik zai ce ba ya saka kai ya fita abin shi, yana fita daga angaren ya nufi inda Bike din yake ya zauna a akai ya kunna sigari ya fara Banka hayaki. Yau gidan casu zai tafi domin ya rage dare. ** Haka Maina ya amshi aikin kamar yadda Malik ya bashi har tsawon lokacin da Aliyah ta fara b'ari tun ana tsammanin ko infection ne, har aka dawo ko mahaifarta ce tayi sanyi, kai abubuwa dayawa sun ta faruwa, a barin da tayi kafin wanda Maina ya bar kasar ne Bahiyyah ta ce musu. "Ina ga ku ka fito ko zata samu cikin da zai zauna." "Ku dai da canfe-canfe kuke!!' inji Ummimi, haka kawai Maina ya sha jinin jikinshi, don haka ya tsannanta Addu'a da barwa Allah ikonsa daga wannan barin sai da ta shekara daya da rabi kafin ta samu wannan Cikin, a lokacin ne Maina ya fara mafarkin Queen Hamidah tazo tana cewa Sai Aliyah ta bata cikin jikinta, yayi mafarkin sau biyu ana uku ranar Aliyah tayi barin, tun fil azal ya san akwai wani mugun abu a cikin masarautar amma bai kawo kome a ranshi ba, sai akan wannan babyn da suka rasa. Shi yasa ya tattara iyalinsa, gashi Saina itama an fara bibiyarta. Haka yasa yake ganin gara barin asar baki aya, tunda rabi da kwatan rayuwarshi yayi shi wajen masarautar ne haka ba wani abu ba ne. Wannan tafiyar Maina ya fusata Malik kamar ya daki Ummimi,domin sai da jininta yayi masifar hawa, don ta zata abin ya kare a'a wani irin cin mutumci yake mata kamar zai hallakata. Mu dawo labari. Tunda Hamidah ta samu ganawa da bakuwar da aka ce tayi, kuma dama Falwa ya gaya mata wani dama yana nan tafe mata, idan tayi hakuri sai gashi nan damar yazo yadda bata zata ba. Zama tayi lokacin da Malik ya shigo yana kallonta. Mika mishi taswirar tayi tana kallon yadda yake kallon taswirar. "A ina kika samu?" Murmushi tayi ta ce. "Ka manta shekaru goma sha uku da uku da suka wuce ko?" "Taya xan