Sashe 59
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masu zafi na yabo da godiya tare da fatan alkhairi. Ware idanu tayi ta nufi shafin Aliyyah ta ga abin da ta rubuta mine Ubangiji ya karo shekaru masu albarka, kayi karko kamar bishiyar dabino, ka kasance da ni a matsayin matarka sauran matan su kasance kwarkwarorri ne da kunyangi. Wannan kalaman yayiwa Aliyyah ciwo domin gani take kamar habaici Aliyyah tayi mata, tare da Bibiyar hotonsu dana Yaransu. Can kuma ta sake murmushi da ta tuna yadda ta jefawa Aliyyah gefen titi tasan Maina bai damu da Layla ba, bai damu ya tsaya ya kalli wacce ita ba, amma daga lokacin da ta Bahira ta ce mata. Murmushi tayi kafin kuma ta ga kamar hankalin Maina bai bar kan Aliyyah tunda gashi da alamun bikin murnan karin shekarun aurenshi yake haka yasa wani kunci ya ziyarci zuciyar Ayrah don ba haka ta so ba, taso taji labarin Maina yayi aure. Duk da ta shirya mata gadar zare amma wani ikon Allah bai yi tasiri ba. Kashe datar zata yi sai ta ga wata yar unguwar ta ce. _Gaskiya Aliyyah tayi sa'ar rayuwa da ta samu miji irin Crown Prince Maina, koda yake garin kwadayi irin na kuda yake fadawa wuta, Aliyyah Allah ya kashe ya ba i jajirtaccen namiji tare da kyawawan Yaranki masu kyau._ wannan kalaman yayiwa Ayrah zafi kashe datar tayi tare da kallon sama tana jin hawaye na zuba mata, ta haifi yaro wanda shi ne yarima na shida me jiran gado, ga Malik yanzu baya ta kanta duk gyaran da tayi asalima kamar ya gama yayinta ne,sannan Suhana ma taji labarin an ce ta gudu abin da ya kara harzuka Malik kenan, ya shiru yayi mata amma zuciyarshi sam bata amince da batun ya hakura da yarinyar da yake hango idan tafi haka zai sha lagwada. Haka yasa shi sakawa kada a kuma barin Ummimi shiga bangaren shi. Cirko-cirko suka yi suna kallon Falwa da ya nutsu domin bai ji a ranshi Layla tana raye ba, sai dai da ya cigaba da bincike kawai ruwan wutan da yake cikin wutar yayi ta kumfa a hankali sai da ya cika bakin tukunyar ya wani tarwatsa tukunyar har sai da ya watsu musu a jiki da fuskarsu dariya aka fara, Gorunfa da ta fito da sauri ya koma raminsa. Hilda ce ta fito ta cikin ruwan wutar tana kyalkyalewa da dariya tana fa in. "Kunyi kuskure kuma kuna kokarin hada wani kuskuren!" Ta watsar da wutar da a jikinsu zo ku ga gudu tsakanin Queen Hamidah da Falwa, tirsila ce bata yarda ta taka ba, ta b'ace. Tsabar gudu da tashin hankali babu takalmi da mayafi Hamidah. A firgice ta shiga angarenta, tana haki bata son Ayrah tana parlourn ba, sai da ta dawo hayacinta. "Wayyo Allah!" Ta fada da karfi tana zare idanu kafin ta ha e rai, tana fa in. "Uwar me kika zo yi min anan?" "Wai na kawo miki magajin Baihak na gobe ne, ya gaida ke ya miki sallama zamu ganin gida!" "Allah ya tsare!" Ta wuce dakinta tana tsaki, tab'e baki Ayrah tayi sannan ta wuce ta fita a bangaren tana mamakin me ya sami fuskar Queen Hamidah da yayi ja-ja-ja. - A hankali suka fito daga babbar Mall tare da Bahiyyah, wacce take bata labarin yadda suka yi da auta da ya ce yana hanya, amma har yanzu shiru. "Hmm! Maybe aiki ya sha kanshi tunda naji." Ha iye maganar tayi sakamakon Maina da tayi sanye da kananun kaya, tare da Aliyyah da su Sainah da Sanah sai Nuri. Tura baki Bahi tayi tana fa in. "Don Allah sai ku biyo mu mall baku gaya min zaku zo ba?" Kamar tayi kuka take kallon Maina da ko a jikinshi sai wani ha e rai yake kamar yaga mugun abu. "Muna isa gidanku muka ga kin fita shine muka biyo ku." Inji Aliyyah. Tana kallon Layla da take gaishe ta. "Lafiya!" Sannan suka juya zasu shiga Motar da ta kawo su, Nuri ta ce bata san wannan zancen ba. "Ni Papa ba zan bi ka ba, wurin Didina zan je!" Sauketa yayi Aliyya ta ce mata. "C'mon my friend wuce ai duk wuri daya zamu!" Wucewa motarsu Layla tayi tunda taga kallon da Aliyya tayi mata da Nuri darling tace zata wurinta. A mota Bahi ta ce mata. "Kin mata rashin kunya ne?" Girgiza kai tayi tana fa in. "A'a!" Duk yadda Bahi tason jin me ya faru bata gaya mata kome ba, sai da suka isa gidan aka fara shirya musu abinci ashe mijin Bahi yasan da zuwansu, sai dariya yake mata, ai kuwa ta fara mita yana binta yana mata dariya. Duk an hadu har da iyayenshi aka ci abinci idan ka cire Layla da bata parlour din, domin tun da ta gasu Aliyyah ta rufawa kanta asiri ta koma daki, bai ji da in rashin ganinta ba, amma kuma sai yaga haka da tayi shine masalaha domin indai tana kusa babu dalilin da zai saka yayi ta satar kallonta, sannan yana mamakin kashin da idan ya ganta yake susucewa, idan yayi ala'akari da Yarinyar nan kwaila ce, babu kome na more rayuwa a tare da ita, kawai bawa kanshi wahala yake tare da dimbin sha'awa da yake dawainiyya da shi, yanzu ta kara hango dalilin tare da hujja me karfi da Malik yake tara mata, shi baya fatan ya zama kamar Malik kai ko Ammar da Saraki baya son ya kai su, ita dai yake son ya tab'a yaji irinta. Sannan ya bambance yanayin Babbar mace da yar kwaila shine kawai abinda zuciyarshi take hango mishi, ba wai yayi ta gwaguran yan mata ba, bayi da wannan ra'ayin ko a baiwa baya fatan tazo kawai zai yi nazarin hanyar da zai ullowa Aliyyah. Yasan Aliyyah tana da mutunci da adalci, sannan idan ya cire yan kananun abubuwan da take yi yasan tana da kirki kawai dai matsalarta bata fahimta. Ashe ana mishi magana ne yayi nisa a nazarin littafin layla. "Papan Twins ana magana?" A firgice ya ce musu. "Kuyi hakuri, hankalina yana can na bar aiki a Washington DC ne." Ya duba gefenshi babu Sanah, "Dama Ummu take magana da kai!" Juyawa yayi yana murmushi. "Me kika ce Amiran Askandariya!" Murmushi tayi tana fa in. "Naji baka yi wani shirin zama sarkin gaba ba shin baka da ra'ayi ne akan zama sarkin?" Girgza kai yayi yana murmushi me sanyi daidai lokacin Layla ta fito dauke da fasassun flat, janye Idanunshi yayi akanta ya ce . "Bani da buri akan zama akan kujeran Baihak, nafi gane nayi rayuwata personal, bana son damuwa yanzu sai tsufa ta kama ni,domin ina burin yiwa Amirata kanne har uku idan ta shirya zama Uwargijiya Accounter General na World bank. " Hade rai Aliyyah tayi tare da Mikewa daga kujeran zata bar wurin. "Zauna ba atashi idan ba a gama ba, al'adar mu ce " zama tayi bata kuma cin abinci ba, amma ranta a b'ace yake, shi kuma Maina yana gamawa ya ciro wayar shi yayi yar latse latse ya mike yana fa in. "Alhamdulillahi Amiran Askandariya na koshi." "Zaku iya tafiya ku maza ne!" Kallon Aliyyah tayi tana fa in. "Kishi kike? Kin manta wanda kika aura ne? Ko ba a gaya miki son mace a jinin da namiji yake ba ne? Kina da hankali kuwa?" Mamaki ne ya kuma cika Bahi don bata san Aliyyah da wannan mugun halin ba, "kina nufin ke aya ce zaki zauna da shi? Tow ko Bahiyyah ban boye mata ba, na gaya mata Mubarak yana da damar auren mace sama da ita, ta ce min ta ga a masarautarsu har Kwarkwara Babanta yana da shi ne yasa zaki yi haka? Ki koyi boye kishi halitta ce amma baya nufin baki da daraja ba ne, ki koyawa kanki iya sarrafa shi sai ki zauna lafiya." Kanta sunkuye kamar tayi kuka ta ce mata. "Zan daina in sha Allah!" Girgiza kai tayi ta ce mata. "Ki ce na daina in sha Allah." "In sha Allah na daina!" "Amma idan kika ce zaki daina you Are not ready kenan, ki tuna kina da Yara ki koya musu abin da za kiyi alfahari da ke, don Allah babu kyau ku daina ni da kika ganni sai da mijina yayi min kishiyoyi goma sha biyu, kuma ban tab'a koran kowacce ba, halinsa da nasu baya barinsu zama Mubarak shine autana. Don Allah kiyi hakuri ki daina babu kyau." "In sha Allah ba zan kuma ba!" "Allah ya muku albarka!"........ [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu Maman Nana Sokoto, Aunty Faridah, ga pagenku nan. _______________33 Bai tab'a kallon Layla a matsayin mace ba, sai da Malik da Aliyyah suka yi pushing hankalinsa kan Layla, sam bai ga wani abu a tattare da ita ba, kawai yana kallon ta amatsyin mai renon Yaranshi ne, sai dai kyautatawar da takewa Yaranshi yasa fara tunanin wani abu, sannan uwa uba wancan aljanar da take tare da ita ta kara mishi son sanin Wacece ita. Amma hakan ba matsala ba ne. "Babban Yaya!" Juyawa yayi yana kallon Mubarak mijin Bahi. "My princess ta ce na tambaye ka,.ka bamu aron Layla." Take annurin fuskarshi ta dauke ya kura mishi idanu. "Zata koma gida ba zata zauna anan ba, sai kace kudi ita kenan daga nan sai can!" Murmushi Mubarak yayi yana fa in. "Allah ya huci zuciyarka dama aro ce, tunda na zaa bamu ba, shi kenan." Ya fa a yana murmushi. A can bangaren Bahi da Aliyyah. Sanah ce ta fito tana ihu, hankalinsu a tashe suke tambayarta. "Ban sani ba, hannuna ne kawai ya kamar ya karye!" Ta fada tana fashewa da kuka ga hannun nan kamar na gwani. "Karya kike bugawa Layla mug kika yi, bayan kin mata kitifo da abincinta, kika fasa flat din haka bai miki ba kika dauki mug kika." "Ke Sainah" Aliyyah ta daka mata tsawa, kasa motsi suka yi ta kalli Layla da gefen goshinta yake zubda jini. "Amma ai bai dace ki dake ta ba har hannunta ya karye, fisabilillahi don ta kwala miki mug sai ki mata lahani haka? Gaskiya wannan ba rayuwa ba ce." Yadda take masifa Bahi ta ce mata.