Sashe 68
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba har muka fita da ita bari zan dakatar da abin da muke mu koma." Daga haka ta kashe wyaar ana gama musu Bahi ta biya kudin, da murmushi Aliyyah ta kawo mishi abinci, murmushi yayi ya ce mata. "Sannu da ari, baki gaji ba ne?" Girgza kai tayi. "Baka da ja indai akai na ne!" Jan hancinta yayi yana daukar kofin tea ya kurba yana fa in. "Na gode!" Sai da ta shanye sannan ya ajiye kofin ya saka jallabiyar da ta dauko mishi ya saka sannan ta wuce dakinshi, laptop dinsa ya dauko ya fara aiki, murmushi yayi yana kallon fitarsu da dawowansu. Tun kwanciyar Malik wani yaron da ya tab'a taimaka ya kira shi bayan sun gaisa ya ce mishi. "Yallabai Queen Hamidah ta biya mu, kudi mu bincika mata wata yarinyar da kazo bikin Bahiyyah da ita, tow maganar gaskiya ta ce idan muka ganta mu kashe ya ne, Yallabai ba xan iya kashe ko kare ka ajiye a gidanka ba, ni zan bada rayuwata domin kare nata, amma ta biya mutane da yawa domin a kashe yarinyar don Allah ka kaita inda baxa a iya samunta ba!" Ya sani ba zasu iya kashe Layla ba, ba wai don kome ba yayi imani da Allah ba zata tab'a barin a cutar da ita ba, sai dai idan tana cikin mutane ta dalilinta za a iya tab'a rayuwar wani. Murmushi yayi lokacin da ya gayawa Principle da kuma nuna mata kome ta ce mishi ya maida ta gida. Haka yasa shi baza jami'an tsaro na musamman masu boyayyen kaya, wanda babu wanda yasan dasu Asalinsu daga Baihak suke horon Salahudeen ne, sannan suna cikin apartment in domin asalin apartment din na Maina ne, wani dan kasar ya ci bashin bankin duniya, kuma yaki biya banki tasaka gwanjon kayanshi, shi kuma Maina ya saya, haka kawai yake jin bari ya mallakawa Layla gidan baki aya, domin tausayin da take bashi. Tun daga floor 1 har zuwa nata, jami'an tsaro ne, maza da mata amma idan baka san kome ba, zaka dauka kawai yan haya ne gudun kada a tab'a kowa yasa yaki aukar yan haya. Kashe laptop din yayi ya kira Timee. "Ba xan dawo ba!" "Ok Sir!" Daga haka ya kwanta a gadonshi.-a gida Bahi suka yi ta gyara mata jiki, har tsawon kwanaki uku,a ranar Dr Abbas ya iso Maina ya kai shi asibitin da zai yi aiki, sannan ya kuma kai shi gidan da zai zauna, a daren ranar suka kwashe kayansu zuwa gidansu aka bar Layla da kewa dama Bahi tun safe ta wuce wurin mijinta. Layla tana kwance Maina ya shigo dakin, kallon shi tayi ta lumshe idanun. "Yau anan zan kwana" da sauri ta mike, "Da gaske?" "Wallahi!" Bari na je nayi abinci." Ware idanu yayi ya ce mata. "Ni bana jin yunwa!" "A'a wa kaina zanyiwa!" Ta fita tayi ta hada shirme da shiririta. Kayan jikinta riga ne iya cibiyarta sai gajeran wandon na jeans ya kama ta yan siraran kafafunta sun fito da dan madaidaiciyar mazaunanta da suka fito dan kadan, tana aiki ya fito ya je ya sameta ya rungumeta. "ni gaskiya ka daina!" Yadda tayi maganar da gaske yasa shi saketa, ta gama aikinta, ta dawo parlour tana cin abinci tana nazarin karatun da aka turo mata ta tap din.koda suka kwnata ya kuma gwadawa taki karshe ta fashe da kuka tana fa in don yaga bata da galihu yasa yake son lalata mata rayuwa. Tun daga nan Malam Muhammad ya daka zuciya, a parlour ya kwana da safe bata san cewa a bar gidan ba, itama ta hada kayanta sai airport. Yana office aka gaya mishi gata nan a airport don wauta ita kawai ta tafi ne bata san yadda zata yi, lokacin da aka korota daga cikin Airport din ta zauna a waje tana kuka, sannan tunda ta bar gidan ake binta bata sani ba, kanta a saman cinyarta. Ta ji kamar ranar da yake haskata yayi sanyi d'ago kai tayi suka yi ido biyu da Hatim zabura tayi zata mike ya damke ta, ya nufi mota da ita ihu take da kuka yana zuwa ya bude mata motar yasa ta, security din da yake binta ya dauki akwatinta ya saka a motar , sannan Maina ya ja motar da mugun gudu..... [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _______________40 Bai kula kukanta ba, domin yasan farincikinta yayi mata yawa ga dad'i, don haka. Ciro na Yaranshi yayi ya shiga saka musu. "Fafa ina na Didi!"Inji Nuri darling "Ke dai yarinyar nan kin iya kinibibi!" Inji Sanah da haushin Nur ya gama cikata sai tambayar wata Layla take mtsew. Ita bata son haka, a bangaren Aliyyah kuwa wannan kyautar a daren aka auke shi, tare da daurawa a IG story tana fa in. *Na samu wannan kyauta ne daga Mine Ubangiji ya shiga lamarin ka! Jasy last week aka yi launching fa! Omo zo ki tayani murna love in Paris! * Abin mamaki ita Aliyyah zuciyarta daya ta daura hoton Ayrah da take dakin kwalliya ita da kawayenta suka ga posting din, kallon juna kawayen suka yi kafin suka kalli Ayrah da bata san me ake ciki ba suka ce. "Princess kin ga abin da matar d'an Mijinki ta daura kuwa?" Bu e idanu tayi da ya sha kwalliya kamar ba gobe ta ce. "Meye yar matsiyata ta daura hala Maina ya fara sonta ne?" Mika mata hoton Sugra tayi bata san lokacin da ta kwace kanta ba, tana wani irin huci domin bata tab'a kawowa zata ga haka daga Aliyyah ba, wani uban nauyi ne ya danne mata kirjinta ta mikawa Sugrah wayar tana tab'e ba i. "Zan je naga wata duniyar ta samu har take fisga haka." "Amma kin san sarkan last week aka yi launching dinsa? Nayi mamaki da ban gani a wuyarki ba, sai wata can da Uwarta da Ubanta suke kaye-kaye na yadda zasu jona rayuwarsu!" "Inji waye? Karya kenan, baki ga gidan da Maina ya musu ba ne, hmmm ai ki bari gayen nan yana kashe kudi akan Aliyyah ni har mamaki nake ji idan akace baya sonta maneji yake da ita." "feener ki fito kawai ki ce kin koma jikin Aliyyah abin da kowa yasan Saurayin Ayrah ne aka kwace mata shi." Ita kuwa Ayrah kamar kadangariya ta kama gyada kai. "Uban waye ya kwace mata? Ku fa na lura baku kaunar gaskiya. Ayrah bari na gaya miki har abada Maina ya haramta a gare ki, ba shi ba abokin Maina ba zai aureki ba idan da halacci, ku bude idanunki da kyau kiyi kishi da Uwar Maina sannan kiyo da Aliyya abin naki ya zama cin kai, asalin cin kai fa nake gaya miki!" "Amma Feenar ban tab'a sanin ke yar bakinciki ba ne sai yau, sannan batun Ayrah zaki samu Malamai zasu iya gyara alakarta da Maina tunda yanxu Malik in bai da wani amfani!" Sake baki Feenar tayi tare da Mikewa, "Allah ya shirya ku!" Ta saka kai zata fita Ayrah ta ce mata. ",Ki ce kawai Aliyyah ta saye ki, kin manta lokacin da nake kashe mana kudi ko ce miki aka yi kwalliyar kin ci banza ne? Oya ki biya kudi idan kuma kin kasa tow sai a kira Aliyyah ko Aliyu ta biya miki!" Murmushi Feener tayi kafin ta bude jakarta tana fa in. "Ke ce matsiyaciya, kin manta da aikina ko kin manta waye Ubana? An gaya miki ni kwadayayyiya ce irin wadannan karanukarki? Ubana har yau yana cikin dattawan kasar nan da ake ji da su, yayana dan majalisar kasar nan, ke Mijina manyan shaguna ne da shi ni babban goro ce nafi karfin iskancin irinki wallahi!" Ta mikawa Yarinyar shagon ATM inta cikin isgilanci ta ce musu. "Ke ki dauka har da na Kwarkwaran Malik!" Tana gama fadar haka ta juya ta bar shagon spa and salon din, "Bura Uban can, yarinyar nan ta ci abinci a kanmu!" Kwafa Ayrah take tana ganin kamar Feener bata kaunarta domin da tana kaunarta ba zata mata iskanci haka ba, tana mata hassada don haka zata yi maganinta. Yadda take jin ko da boka da Malam sai ta dawo da Maina rayuwarta. Haka aka gama kwalliyar ranta kamar ta cire idan ta tuna zunzurutun kudin sarkan kawai tana ji kamar ta mutu kawai, haka aka gama kwalliyar suka tafi bikin da zasu. Lokaci zuwa lokaci tana duba wayarta abin mamaki sai ganin Feener tayi tana reply wa Aliyyah. *Matar King Muhammad Maina Hatim wata rana kina tare da bayi da kunyangi ana miki fifitar ban girma, ni kuma nazo nimawa Asad dina auren Nur! Mommy Boy da Daddy Gal!* Ihu ne kawai Ayrah vata fasa ba, amma ranta ya b'aci Sugra da Haulat sai zugata take tayi rashin mutunci wa Aliyyah. Zuwa tayi ta binciko wani tsohon hoton khoi noor inta, ta daura a IG story inta! *My first night gift daga King AbdulMutallab Hatim!* Can ta kuma dauko hoton sunan Jawad. *My prince king to be! Jewelry din nan na samu kyautar shi daga Sarauniyar Austaraliya!* Sannan ta daura hoton wani dankareren mota, ta saka *kyautar da na samu na haihuwarshi King to be My Jawad! Dole a kira ni Queen domin na haifawa Baihak jarumin maza!* Sam ita Aliyyah bata san da abin da ake yi ba, ke Feener da ta ga abin budar bakinta ta rubuta a pagen inta. *Haushin bakin kare baya hana kura shiga gari! Akwai banbanci tsakanin Wife and Concubine! Akwai tsawo me yawan gaske! Wife zata kasance a zuciyar King amma concubine kuwa zata kasance kamar mistress ne wurin hutawar King* Wayyo Allah kafin kace me IG ya kacame da rigimar manyan mata masu manyan mazaunai. Take aka samu rabuwar hankalin mutane yayinda wasu suke hango laifin Aliyyah da take daura abin da zai janyo hankalin Ayrah ai ko babu kome ita In-law dinta ce, yayinda wasu suke ganin kamar yadda Ayrah take hauka ai shirme bata isa hana Aliyyah daura abin da ranta yake so ba, tunda handling social media ce babu wanda ya isa hana wani yadda yake so. wata kawar Jasy ce ta kira ta, take tambyarta meke faruwa ne? Ta