Sashe 26
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sulale ya b'ace, wani abin mamaki da sarar da b'acewar majicin minti biyar kacal, daidai lokacin Queen Hamidah ta iso ita da su Tirsila, jikin shi ne ya fara fitar da wani irin tiririn zafin me tashin hankalin, aka nufi cikin masarautar da shi, domin zai iya mutuwa a kowani yanayi. Yadda garin ya lullube da duhu, Tirsila ta d'ago kai tana kallon wani irin tsuntsu wanda tasan kaf duniya babu me tashin wannan tsuntsun sai kabilarsu musamman wa anda suke da related ga Uwargijiya Wada, "karya ne!" Ta fada tana buga sandarta da kasa, domin walkiyar da ake da rugugin da ya e tashi daidai yake da farkawar daya daga cikin Uwargijiyoyinsu, "Jamimah!" Ta juya cave din da sauri, "ina zaki muna cikin wannan yanayin?" "Matsafin da ya farmaki Malik, yana da alaka da Layla da ake nima, Jamimah ka ai zata iya fadar haka, ku tafi da shi bari na samu Falwa yanzu zan dawo. Sannan ki sa kawo Sanaya kanshi zata yi abin da zan yi gani nan zuwa." Kafin Hamida tayi magana ta b'ace, dira tayi a gaban Kaka Jami. "Me kika aikata?" "Me kike tsoro? Kin ga sako ne? Wannan ba sakon hukunci ba ne, sakon bayyanar yar marayar zakanyar Wada ce." Nunawa Kaka Jami sandar tsafinta tayi take ya shake wuyarta, "Jami ki gaya min yadda zan karya gubar jikin Malik." "Babu abinda ya dame ni, Tirsila idan ya rayu kune kuka d'aga shi idan ya mutu kune kuka kashe shi, ni babu abin da ya dame ni." "Jamimah!" "Ko sau dubu zaki kira sunana ba zan amsa ba, kuma ba zan tanka miki ba." "Falwa muje ka ga dafin!" B'acewa suka yi, kaka Jami tayi shiru cikin zullumin bayyanar Layla a cinin masarautar domin taji rugugin. "Shalele ki bar gidan nan, kin ji lokaci na zuwa da zaki dawo kiyi hakuri." Ta fa a hawaye na zuba mata. A bangaren Ummimi kuwa tana can dakinta kwance rauhanin da aka tura mata suke tsafeta ya kone murus, juyawa Layla tayi zata fita akan Idanun Hajar. "Kina da zuciya me kyau, ki kula da ita domin fansa ya kawo ta, kada ki sake kiyi tunanin cutar da ita domin muna zagaye da ita, kuma akwai Alkhairi a tare da ala arku." Yankar jiki tayi zata zube, Hajar ta tallafeta suka fita sai lokacin garin ya fara wayewa, haka suka fita daga masarautar, kafin hankalin mutane ya dawo kansu. Suna fita aka saka dokar ba shiga ba fita. Bayan fitarsu daga angaren Ummimi, ta farka tana salati domin duk abinda ya faru gani tayi a mafarki, ga yadda yaron ko yarinya ce take zubawa wani abu me kama da dodo bulala, ta jike da zufa tashi tayi dakyar zata sauka Court lady ta shigo cikin tashin hankali, ta zube. "Ranki shi da e, Malik an samu wani matsafi ya turo mishi macijin tsafi ya sare shi, yana can cikin mugun yanayi." Tashin hankalin da ya bayyana akan fuskarta, babu iyaka don haka ta fito da sauri suka nufi villa inshi. Har tana tuntube, suna shiga ta samu baki aya concubines dinshi suna parlour in shi, yadda Queen Hamidah tayi tsaye ta kasa zaune, bata magana can sai ga Tirsi da Falwa, suka shigo a tare aka nufi dakin Malik in, itama Queen Hamidah ta shiga, can ta fito tana kallonsu ta ce musu. "Kuje duk yadda aka yi zan sanar muku." Babu wanda ya musanta mata, duk suka bar Villa din, nan kuwa tsafi da surkulle ake ta bugawa, amma babu labarin Malik. Ummimi tana isa bangarenta ta kira Yaranta, musamman Maina ta gaya mishi. Murmushi yayi ya ce mata. "Allah ya sawwaka!" "Maina kazo don Allah." "Ummimi aiki ne da ni." "Aikin yafi mahaifinka ne? Duk abinda zaku yi kada ka manta shine silar samuwarka, amma kada ka watsar da shi lokacin da yake bukatar agajinka." "Yanzu ya zan yi to?" "Ka zo!" Ta fa a kai tsaye abin ta. "Shi kenan!" Ya fa a, bai kuma cewa kome ba, Albarka tayi ta saka mishi da niman dacewa, Amin kawai yace domin yasan darajar Addu'arta. Layla kuwa a gida Hajar ta maida ita, sai can dare ta farka shima don mafarkin da tayi da kaka Jami ne, tana shafa kanta. "Shalele kada ki kuma zuwa cikin masarautar nan kin ji, yanzu ba shi ne lokacin ba, lokacin na zuwa amma a yanzu babu amfanin haka." "Tow kizo muje gida!" Murmushi tayi tana nuna mata hannunta da kafarta. "Kiyi hakuri ba zan samu zuwa ba" "Tow ki jirani ganin nan zuwa." Juyawar da zata yi ta farka a cikin dakin kwanansu, kuka ta fashe da shi, har gari y waye kuka take domin tana matukar kewar Kaka Jami, Tashinsu tsoho salis yayi suka tafi taku, a lokacin ta ware kamar ba ita ba, don haka sun kamo kifi dayawa, tun a bakin Kogin ake saya, musamman da suka kamo giwar ruwa. Haka suka fito bakin hanya aka baza kwando. Duk da matukar duriya take domin tana mugun jin ba dadi. Yau ka ware murya tayi ta ce. "yakuuwaaaaaaaa Jama'a yau giwan ruwa na kawo muku! Azo a saya ko na fasa sayarwa na je nayi ta kallon abuna." Yadda take tallar tana tsalle zaka rantse da Allah, ita aya ce ai kuwa abin kamar caca lokaci guda aka yi ta muhawara akan kayanta, kafin kamar jiya yana zuwa ya bada ku i me yawan gaske ya sayi giwan ruwan yaja mashin dinsa a guje. Sai da kifinsu ya kare tass ta juya tana kallon sauran yan kifin. "Ke?" Juyawa tayi tana kallon wata basamudiyar mata da ta ninkata sau goma sha daya, d'ago kai tayi tana kallonta kafin ta ce mata. "Dunfama da ni kike?" Ta nuna kanta da yatsa. "Uban waye ya tsaya miki a garin nan?" Kallonta tayi ainun tabbas idan tayi wasa dunfama ta zaune ta,sai wata ba dai ita ba. Murmushi tayi ta ce mata. "Ke uban waye ya ba i zarafin gaya min magana!" "Ubanki ne." "Ubanmu dai ko?" Wani irin duka ta kaiwa Layla tana fa in. "Ubana kika zaga." "Yo naga uban naki ba da zinari aka sassake shi ba, balle ki ce ya fi ubana sheki!" Duka ta kai mata, ai kuwa ta kauce kamar wacce aka fisgo dunfamar ta hantsila da fuskarta cikin kwatar da ake zubar da ruwan kifi da kazanta. Ihu aka saka ashe matar da gang dinta. "Sajid ku gudu, kyale su da ni!" Ta koma saman wani kujera ta zauna tana me kallon tafiyar su Sajida, tasowa suka yi a guje, kamar wanda suke taka tsantsi faduwa suke suna karo da juna, ita kan dunfama sai ta gama yunkurin mikewa sai ta kuma zamewa, tayi haka yafi sau goma bata tashi ba, karshe gang dinta ganin zasu jikata kowa ya farce a guje. *Na rantse da abin bauta Wada yau sai kun san kun tsokano ni, kadangaru da barayen da kifi ku sakasu kwasar gudu kamar ba gobe!* Ai kuwa kowa ya kama gabanshi, akwai daya daga cikin abokan dunfama me suna Raji, sai da yayi gudu har ya kusan gida ya tsaya hutawa sai ji yayi ana fa in. "Ayya wai ka gaji ne? Tow tsaya ina zuwa." Ya duba sama da kasa bai ga kowa ba, "dalla can gani nan a jikin bango!" Juyawar da xai yi ya ga kadangare ya zauna ya daura kafa daya akan daya. "Yawwa ka gane ni ko?" Wato da ya kwasa da mugun gudu, bai tsaya ba sai ihu yake. Can wata yarinya itama ta gama gudu ta zauna a wani kofar gidan tana nishi, aka ce mata. "Shashasha hala dan gudun nan ne kike ni ki san irin gudun da nake idan na dauko gyadar miyar mutane." Itama juyawa tayi bata ga kowa ya ce mata. "Kekeke kada ki take min jelata gani nan bera ne!" Wato bata san ya aka yi ba, sai ganinta tayi tana haurawa katangar gidan mutane, ba tare da sanin cewa tana hawa ba. "Kin ga ko kin haura babu inda zaki bila bari na nuna miki, yadda ake hawa katanga." Yadda ta kuma ganin beran nan, bata san lokacin da ta fado daga katangar nan. Dayan kuwa yadda yayi gudun kuwa, sai ji yayi ana cewa. "Oho ni dattijon kifi, ban da rashin mutunci irin na d'an Adam, wai dan wannan motsa jikin ne ake haki, dalla muje." "Wayyo Allah na!" Dafe kirji kifin yayi shima yana ihu, tsayawa Yaron yayi yana kallon yadda kifin yake ihu, "wayyo Allah taimako,wayyo ku kawo min auki;" zubewa Yaron yayi a wuri ya suma. "Sakarai kawai." Dama su hudu ne, na hudun kuwa sai da yayi gudun aka ce mishi. "Yawwa taimaka na huta, domin tsohon ciki ne da ni!" Bai san lokacin da ya kara juyawa ya koma kasuwar ba. A bisa al'adar matsafa a duk lokacin da suka ga wani sign na magic spells yana tasiri a wuri, duk inda suke suna fitowa. Haka ya faru a cikin masarautar Baihak. Duk da halin da Malik yake ciki ba, hana Falwa jin kamar ya fito ya bar Malik a wannan halin ba. Haka ya daure yana aikin, Salahudeen da Abraham ne zaune a kofar parlour Malik, duk yadda Queen Hamidah taso su bar kofar dakin fir suka ki barin kofar. Har da Ummimi. Wasa wasa sai ga jikin Malik yana liara rikicewa, ba karamin ari Sanaya tayi ba domin har sai da ta fara zubar da jini a hancinta, ganin haka yasa Tirsila tayi maza ya fita da ita daga dakin. Domin karfin gubar tsafin yasa ita tana iya shakarshi. A can wurin yan kifi kuwa, wani dattijo ne ya fito daga wani layi, ya kura mata idanu, yana kallon yadda magic spells yake zagaye da ita, shi ba ita yake hange ba, wata babba Goddess yake hangowa yadda take iya sarrafa mind din Layla, zubewa yayi akan gwiwarshi "My Queen wannan jikin yayi rauni ba zata iya aukar yanayinki ba." Yadda yayi maganar daga nesa ne amma haka Layla ta juya tana kallonshi, tashi tayi ta nufe shi. Yadda take tafiya yasa ya sake kaskantar da kanshi. Tana nufar inda yake ta shafa kanshi. "Ahmar!" Kaskantar da kai yayi yana yana fa in. "My Queen!" A hankali tana