Sashe 31
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Uwata!" "Idan kai ka auro min ita, sai ka d'auketa dan banza mara mutunci." Murmushi Maina yayi ya bar asibitin. Haka suka wuce airport, anan suka samu Bahiyyah da Salahudeen da Haisam suna jiransu. Kafin jirginsu ya tashi aka kafa hiran Queen Hamidah, domin gidajen tv sai haska abin da ya faru jiya suke. Dauke kai yayi yana jin kamar ya fasa ihu, wannan tozarcin da me yayi kama? Haka har jirginsu ya tashi,suka yi bankwana da Ammar da Salahudeen, kowa ya shiga motar shi ya wuce aikinsa. Daga office dinsa masarautar Salahudeen ya wuce ya tattara shirgin Ummimi ta koma gidansa domin kawai jikinshi wani abu zai iya faruwa a kowani yanayi. Da Malik yaji labarin abin da ya faru, bai magana ba sai da Salahudeen din ya zo da matarshi da Yaransa, Malik ya ci mutuncinsa. Kamar zai dake shi. Shi dai Salahudeen yaki fir ya maida Ummimi domin ya zai yarda masifar da suka lakato ya shafi Uwarsu ba. Tsawon wuni guda suna falfala gudu a sararin samaniya, kafin suka isa kudancin Baihak, koda suka isa rikidewa yayi Kyakyawar matashin saurayi, saketa yayi ya rigata sauka ta fado a hannunshi yana tafe mayafinsa yana bin bayanshi har cikin fadar da Haeda take tsaye tana kuka, ya shigo da Layla da take sume, Ajiye yayi a wani kujera ya gyara mata kwanciyarta. "Ga ta nan na kawo muku ita, na cika alkawarin!" Ravi da yake can tsaye idanunshi ya cika da kwalla, tausayin Layla yana kara cika zuciyarshi." Sannu da ari khatir!" Inji Haeda ta nufi Layla da take sume, amma hawaye na zuba daga idanunta. "Zata dauki fansa, dole ta ga bayan Baihak da mutanen cikinsa." Inji Haeda tana kuka sosai, "Taya zata shiga Baihak?" Inji wata tsohuwa da take tafiya da sandar tsafinta na asalin jar karfe. "Dole ta shiga Baihak." "Taya to!" "Zan bincika nan kusa." Al'amarin tirsila kuwa bazama niman Sanaya take tare da, bibiyarta ta allon tsafi, duk yadda ta nimeta ta rasata, don haka tayi amfani da abin wuyarta, sai ga Sanaya kwance jini na zuba a kanta, haka yasa tayi maza ta lulla sama a guje, dakyar ta samo inda take, bsu dawo baihak ba, sai cikin dare. Queen Hamida ta basu wani gida a wajen gari, babban gida me auke da ginin zamani. Anan suka samu har da bayi aka basu, zuwa yanzu lissafinta, ta gina rayuwar sanaya domin tunda ta ga Maina, taji kaf duniya babu wanda ya dace da Sanaya sama da shi don haka tasan yaki ne Babba a gabanta matukar tace zata cusa musu Sanaya zai iya zama wani abu na daban, gara ta gina goben jikarta. Ta hanyar bata ilimin zamani sosai. ** Duk abinda ya faru Malik ya samu labari, sai dai bai wani damu ba, yasan duk abinda Mahaifiyarshi zata yi tow don kare shi ne, kuma ba zata tab'a abin da zai cutar da shi ba, don haka ya mike kafa, nurse din shi me suna Suhana tana zuwa duba shi tana mishi treatment, dake Allah ta daurawa Malik Jarabar mata, ganin manyan mazaunai da yaja hankalinsa haka ba karamin bawa Lady Ayrah haushi yake ba, dama Lady Hidayah sau aya tazo shima da rigima aka rabu tsakaninta da Lady Ayrah, domin kishin da suke da juna har yna shirin kazamta. Ita lady Ayrah tana takama don Malik yana manne da ita, ita kuma Lady Hidayah tana takama don ta haihu da Malik, haka yasa kowacce take jin ta isa a jikin Malik, ai kuwa Malik ta kori Lady Hidayah da kwanaki biyu, ya fara kyarkyaran Nurse Suhana, ai kamar Lady Ayrah zata yi hauka fada da habaici wulakacin da cin mutunci babu wanda bata yiwa Yarinyar ba, ita dake tana manufa akan Malik sai ta dauke kafarta ko kwana uku ba ayi ba, Malik ya tashi hankalin kowa, sai ita ce zata mishi jinyar afarsa. Wannan abin ya bawa Lady Ayrah haushi, tattaro ta bar asibitin babu shiri taya zata cigaba da ganin kayan haushi haka, Lady Hidayah tana jin labarin tayi ta dariyar mugunta. *** Yau kusan sati daya kenan, wannan abin yana tab'a rayuwar Maina, rashin walawalar shi ta kai har Yaransa sai da suka fahimci hakan. Sannan ko a wurin aiki dole suka bashi hutun hucin gadi, domin baya iya tabuka kome, yarinyar da ya gani da abin da take, ya tsaya mishi a rai, a bakin Bahiya yake jin labarin jikar matar ce, kuma da alamu Baihak tayi sabuwar enemy domin yadda take abin yayi imani da Allah dole zata dawo, zata dawo daukar fansarta. Sannan a yadda ya fahimci labarin tun lokacin shekarun baya abin ya faru, lumshe idanunshi yayi ita ce tsaye tana ihu iska na fita daga bakinta, gashin kanta ya mike baki aya wurin yayi jajjur, bude idanu yayi yana kallon Aliyah da take tsaye. "Papa food is ready!" "Ku ci kawai!" "Ok!" Ta ce sannan ta fita, wayar shi ne yayi kara ya auka tare da sakawa a kunne. "Don Allah ka saka a sallami Malik kafin ya bude shashin concubines a asibitin!" Murmushi yayi yana me cewa. "Ina ruwana!" "Maina amma kasan mutuncin kingdom ne yake zuba ko?" "Sai me?" "Don Allah nayi wani abu!" Inji Salahudeen, yasan yadda Saraki yake masifar kamun kai, yasa shi ce mishi. "Shi kenan!" "Yawwa da fatan kana lafiya, Haisam ya gaya min an baka hutu!" "Hmm!" "Maina ko baka da lafiya ne?" "Lau nake!" "In sha Allah, zamu zo ganinku nimaena gaji xan dauki hutu amma zamu fara zuwa umara ne!" "Baka gajiya da magana ne?" "Eh musamman idan ina tare da kai!" "Sannu!" Maina ya fa a mishi, duk ya kagu Saraki ya kashe wayar,kamar ya sani ya ce mishi. "Wallahi ba zan kashe wayar ba, Malam hira na kira muyi." "Ga Haisam da Bahi sai ni zaka addaba?" "Eh saboda kai kafin dacewa nayi hiran da shi." "Dakyau." "Kare ya ga rawan kura." "Zan kwanta?" "Kai ne gado, karewar kwanciya." Yadda yake maida mishi magana abin dai ta bawa Maina dariya, kuma karshe hiran da yake kin ya saki baki yayi ta murmushi, yana bashi labarin Ammar suna jami'a, kamar Ammar din ya san da haka suna hiran shima yayi ta kira, karshe Maina ne ya ha a musu conference call, tunda aka fara hiran yaja bakinsa yayi gum sai yar murmushi me sauti zaka ji yayi cikin wani irin nishadi hira sosai suka yi, har karfe biyu na dare kafin ya kore su, ya sauka a gadon ban daki ya shiga yayi Alola ya fita, sannan ya gabatar da sallah nafilla, ya fita zuwa dakin Yaranshi yayi musu addu'a, kafin ya nufi dakin Aliyyah tana barci a dakin ya kwanta a dogon kujeranta, domin tunda ta samu cikin take gudunsa, shi kuma ya hakura da kome yana dai tare da ita ne don matsalar da take samu na laluran b'arin da take yi.-- Layla ta dauki tsawon kwanaki goma sha bakwai tana kwance ba tare da tasan inda take ba, a daren na sha bakwai ta farka, sakamakon mafarkin Kaka Jami da tayi ta ce mata. "kina cikin duhu mafi muni, ga haske can ya tawo miki, kada kiyi wasa da damarki irin namu, domin mun rike ababben da ba zasu iya kare mu ba, maza tashi ki tafi ga haske maganin duhu kada ki yarda duhun da muka rayu akai ki rayu a cikinshi, ki kasance daren alkhairi ga Al'ummar wagadu ku nemi tafarkin tsira wannan hallaka ce da dubu mara iyaka, maza tashi ga haske can!" Bude idanu tayi tana waige-waige, ganin fitilar kwai yana ci, a hankali ta fara taryo abin da ya faru da ita, da ta fasa ihu me arar gaske dai da duk wani abin da yake dauke da ruwa, fitilar kwai, rumbun abinci, fashewa hasken da mutane suke gani yayi ta mutuwa, wani tashin hankali ya bayyana a kan fuskarsu, sun dauka wata masifa ce, ta zo musu sai daga baya suka gane Layla ce take ihun da gudu Haeda ta shiga dakin babu haske, ta nufi inda take jin muryanta. Ta rungume ta tare da shafa bayanta domin kuwa ihun ba zata daina ba. "Ya isa haka!" Kuka ta fasa me cin rai tana son tayi magana amma ta kasa, rike Haeda tayi tana kukan a lokacin aka kuna wutar dakin, tare da kwashe abubuwan da suka fashe...... (Yau sai a hankali) #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu *MASU BU ATA DAGA FARKO DON ALLAH SU SHIGA LINK ABUBUWA SUNA MIN YAWA GA CIWON IDO GASKIYA BA ZAN IYA BADAWA DAGA FARKO BA TA PRIVET KO GROUP LINK CHANNEL GASHI NAN IDAN KA SHIGA ZAKA SAMU DAGA FARKO PLEASE joining the last* https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s _________________14 *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*