Sashe 81
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi na ya ce mata. "Bani number mana!" Ya mika mata wayarshi, ba musu ta saka mishi, sannan yayi fitarsa. - A can Baihak tunda suka tono kwarangwal din Rihanna, Tirsila hannunta yake ciwo, domin bayan ta dawo gida hannun sai duhu yake tun tana boyewa Sanayah har ta gano halin da take ciki, a hankali ta ce mata. "Gargadi aka miki akan abin da kike aikatawa, Kaka ki daina kafin lokaci ya kure miki, ina ji a jikina Layla tana nan tafi kuma babu ji babu gani fansa zata zo auka." "Ni zan kashe ta da hannuna!" "Tayi girman da ba zaki iya tunkarar ta ba, domin ya samu yarda da kusancin da take bukata ki tattara naki ya naki mu bar Baihak." Murmushi Tirsila tayi tana fa in. "Ban tab'a gudu ba, ba zan bar garin nan ba sai na kashe Layla da hannuna!" "Lokaci zai ci maki ba tare da kin samu yadda kike bukata ba, na tausayawa lissafin ki da bai baki cewa ko inuwar Layla ba zaki iya tunkarar shi ba, balle ita kanta Layla ina mai kara baki shawara ki bar Baihak a wayi gari babu labarinki yafi a wayi gari ana miki tir da tofin altsine." Ta kama hannun Tirsila ta mstse da karfi sai ga kwarin nan da wani bakin ruwa. "Tun kafin abin gudu yazo ki fara gudu, kafin abin gudun ya cimmaki!" Daga haka ya barta da zogin da hannunta yake mata, daki Sanayah ta shiga tana fa in. "Baki san yadda Layla ta samu matsayi daraja ba ne ba zaki b'ata lokacinki wurin raiwa kanki lokaci da wasu abubuwan ba" a can cikin fadar Baihak, ana kan tattauna yadda zasu tashi Rihanna, duk lissafnsu ya tsaya gorunfa ne ya kalli Falwa ya ce mishi. "Ina kwayar idanun Jamima!" Mika mishi Falwa yayi ya nufi kan kwarangwal din, amma ya kasa isar da abinda yayi niyya ja da baya yayi ya ce musu. "Ku nimo Tirsila ita da jikarta zasu iya wannan aikin!" Haka Falwa ya B'ace, tirsila tana zaune ya bayyana. "zo muje!" Haka suka B'ace sai gasu. Mika mika mata abun yayi Falwa na mata bayani. Tana tunkarar kwarangwal din ta zuba a kai. Kafin Falwa ya kawo gawar Kalfana ya ajiye a gefe, koma wancan kwarangwal din da idanun Kaka Jami da suka ajiye suka yi aka zuba mishi wasu alasuman tsafi sannan suka bude cikin Kalfana suka zuba kayan tsafi amma gangar jikin bai motsa ba, haka yasa duk suka sare, tare da zuwa gangan jikin idanun. -- Sai wurin karfe sha daya Maina ya fito daga dakin Layla ya wuce dakinsa, shiryawa yayi yana kallon agogon hannunshi, ya fito parlour sai da ya leka kitchen ya samu babu kome alamun anci kenan, shiga kitchen din yayi ya dafa tea din tare da soyayyen bread ya saka s tire ya kai dakin Layla da take barci ya rufe mata, sannan ya dawo ya zauna yana karyawa. Bai gama ba mijin Jasy ya kira shi. Dake dukkansu maza ne kuma sun san kansu take suka warware matsalar da take damun gidan Maina wanda kai tsaye mijin Jasy ya bashi laifi da kuma nuna mishi kuskurensa, dake Maina mutum ne mai matukar saukin kai sai gashi ya fahimci inda matsalar take., kuma tsakanin da Allah idan aka zo batun gaskiya a fade kawai. Yayi godiya tare da kashe wayar, don haka ya nufi dakinta ya samu Nuri darling nata rigima zata wurin Mami, baya son ya ara kawo wani sabon rigima kawai ya ce mata. "Nur Maminki tana barci sai an jima zaki ko!" Ya tsare Aliyyah da idanun. "Me kike so nayi ne don zuciyarki ta wuce? Tunda Allah ya gani ba ina yin wani abun da ranki ya b'aci ba ne, nasan da na dauki halin mahaifina da wani labarin ake ba wannan ba, amma nayi kokarin na kaucewa wancan dabi'ar domin a zauna lafiya. Idan kuma akwai ko kuskuren da nayi miki tow kiyi hakuri!" Daga haka ya bar dakin, sai dai shi bai ji kome ba, amma kuma tabbas ita taji babu dad'i, din wani abin da take ji sai ta ga ashe ba kome ba ne. Har wurin karfe biyu bata fito ba don tunda tayi sallah ta koma ta kwanta sai da biyu yayi ta fito ta ga Yaranta a parlour. "Kun dawo ne?" "Eh Mum babu abinci ne?" "Eh yanzu zan daura!" Ta shiga kitchen din ta fara kokarin daura abincin, Layla ta fito sanye da doguwar riga ash colour, hannunta dauke da tire Nuri na biye da ita tana shan chocolate. "Ina kwana Mum!" Share ta tayi kamar bata ji ba, ta ajiye tiren sannan ta fara kokarin wanke kayan ta ce mata. "Fita min a kitchen!" "To" ta fada tana wanke kofin, ta juya tare da barin kitchen din yadda Sanah ta tsaya a kofar kitchen din yasata nad'e hannunta a kirji tana fa in. "Bani hanya na wuce!" "Idan naki fa." Murmushi Layla tayi tana mata. "Babu abun da xan yi amma zan wuce tabbas, Mum ki gaya mata ta bani hanya na wuce!" "Ba kina da me tsaya miki ba, ki kira shi mana. Ke ga ki mara kunya!" "Mum haka bai da ce ba, ko babu kome matar Papa ce, bai dace Sanah tana shiga rigimar ku ba, ni gaskiya ban ga amfanin haka ba!" "Dake baki da zuciya ba!" In Sanah saka hannu Layla tayi a hankali ta maida Sanah baya sannan ta wuce abinta. "Ke!" Banza tayi me musu domin Aliyyah ta kira ta. Amma bata kulata ba, har ta shiga dakinta bata kuma bin ta kansu ba. Lokacin da Maina ya dawo ya samu Sanah tana kwance wai bata da lafiya, koda ya so su je asibiti Aliyyah taki da ya tambaye dalilin ciwon sai cewa Aliyyah tayi Layla ta rufeta da duka. Ya juya yana kallon Sainah da taci kuka ita da Nur suna wuri guda. Da alamun Aliyyah taci Ubansu ne. "Su kuma fa!" "Ai duk tare ta musu dukan!" "Me yasa baki kira ni ba!" "Lallai fa kai da baka ji baka gani akan Layla!" Bai ce kome ba har ya koma dakin shi ya ci abinci ya yi wanka sannan ya nufi dakin Layla da take ta game a wayar. "La Papa ka dawo?" "Eh na dawo, ya kike ya gida?" "Lafiya lau!" Daga haka ta koma ta cigaba da game dinta. Zama yayi yana fa in. "Me ya hadaki da Sanah?" Shiru tayi na wani lokaci kafin ta ce mishi. "Ai wai abin ya faru da safe? Tow ai ba wani abu ba ne tare min hanya tayi na matsar da ita gefe na wuce abin da ya faru kenan kuma su Sainah suka wurin. Ganin yadda maganarsu kowanne ya bambanta ya ce mata. "taso muje ki basu hakuri!" "Hakuri kuma? Da nayi me??" "Muje nace miki!" Yadda yayi maganar babu wasa yasa ta bishi har dakin Aliyyah ta basu hakuri kuma a gabansu ya mata warning kada ta ga yana bin ta, ta ce zata raina mishi mata da Yara ba zai dauka ba. Kan Layla a sunkuye tabbas Maina bai da Adalci. Yana gama fadar ya sallame ta ya kuma ce yaran su wuce dakinsu. Bayan fitarsu ya ce mata. "Sai me kuma?" Juya da kai tayi ta ce mishi. "Ban yarda da kwana biyu da ake yi ba, kwana aya daya ya isa!" "Sai me?" "Daga nan ba zaka kuma fita ba sai gobe," tayi haka ne don yana fita zai nufi dakin Layla, tasan yana zuwa hakuri zai bata shi yasa ta hana shi fita. Tunda Layla ta koma dakinta take kuka domin abin ya mugun mata ciwo bata yi kome ba an sata dole ta bada hakuri dan shigowa da zai yi yaki zuwa haka ta kwana cikin takaici da zazza i har gari ya waye bata ga idanunshi ba, sai can rana da zazzabin ya fada tayi wanka ta fito tana niman abinci ta ganshi zaune cikin iyalinsa yana ta aiki da wasu takardun, kwalla ya cika mata idanun ta ce. "Papa ina kwana?" "Lafiya lau Layla!" Bai kalle ta ba ma balle har Aliyyah ta ce wani abu. "Mum ina kwana?" "Lafiya!" Shiru tayi tana tsaye a wurin. "Abin karyawa na Please zan samu da magani don bana jin dadi ne?" A wani hargitse ya juya yana kallonta fuskarta tayi wani fayau, mikewa yayi ya nufeta. "Tun yaushe baki da lafiya?" Wannan yar kulawar da ya mata yasata fashewa da kuka har jikinta yana rawa. "tun jiya!" Ta fada tana kuka sosai. "Sainah dauko min key mota yanxu nan!" "Babu inda zaku magani tace ba asibiti ta ce ba, abin karyawa kuwa ta shiga ta dafawa kanta ai mace ce ta iya deal da namiji abinci ne ba zata iya girkawa ba! Comon my dear shiga kitchen. Kowacce mace ma haka take idan tana iya daukar Lamarin miji." "Wannan wata irin hauka ce? Ciwon ne ya zama abin dogara a ci zarafin wani? Ke dauko min keyna nace!" Babu musu Sainah ta wuce ta kawo mishi yana rike da ita suka nufi asibitin, a iya binciken da aka yi babu wani abu sai zazza i da ya sakata a gaba da rashin barci, magani aka rubuta mata suka dawo gida. Da kanshi ya mata abincin. Ya Kawo Mata sannan ya koma wurin Aliyyah duk da tana son tashin hankali amma fir yaki kulata har zuwa dare zai koma wurin Layla ta ce bata san wannan ba sai da suka yi ta bala'i ta ga da gaske zan iya mata rashin mutunci ta kyale shi ya fita. Washi gari tun safe ta buga musu kofar dakinsu.... (Masu tambayar account din Yar Mace 500N ne 0472282105 ramlat Manga gtbank ayi min magana sai na saka mutum a WAIT-LIST 08130269641) [9/9, 12:30 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu _________52 Yadda take buga kofar dakin zaka auka wani abu ne ya faru, Layla ce ta fara bude idanun tana kallon yadda barcin da yake yayi nauyi don kwana yayi yana fama da zazza in da ya ke damunta. A hankali ta hura mishi iskar bakinta, tuni barcin ya kara nauyi. Yadda ba zai ji karan bugun ba, ta sauka a gadon ta nufi kofar