← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 115

Sashe 62

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

niman jikin da zata zauna domin ramuwa!" Dafe goshinsa yayi yana kallon yadda take kallon parlourn. "Na ji amma!" "Amma me ye? Na gaya maka abin da baka sani ba?" "No need!" Wani gatsine fuska tayi ya ce mishi. "No need!" Ta kwaikwayi muryan shi. Tsaki yayi itama ta yi mishi. Komawa yayi can jikin babban kofar da yake wurin me kama da window. Yayi shiru. "Yaranka biyu Nur da Sanah suna hannun dodon da yake musu tsafi, Sainah kuma tana tare da addu'arka ne, nasan abin da kake son sani kenan me ye alakar ciwon Malik da Nur,ta gaya maka ai kiranye aka maka. " "Zan koma Baihak!" Da sauri ta taso tare da rungumar shi ta baya. "Namiji kenan, amma ba yanzu ba domin ko kaje ba zaka fahimci haka ba, ka bari lokacin zuwa bai yi ba!" Janyota yayi gabanshi yana kare mata kallo. "Leave!" Tura baki tayi tana fa in.."Zan tafi amma me yasa ka saya mara gida baka tsoron Aliyyah ta sani!" Wani matsiyacin kallo ya mata, da sauri ta fice ita kuma Layla ta koma zata zube ya tare ta, ya kwantar da ita har zuwa wani lokaci yana ganin Aliyyah tana kiranshi bai dauka ba, sai bayan yayi Sallah la'asar yayi odar din abinci, yana amsowa Layla tana farkawa. A kunyance ta farka tana kallon shi yadda yake cin abincin shi kai tsaye. "Ga ban daki can ko wanke bakin ki!" Tashi tayi a hankali idanunshi ya sauka kan kujeran da ya b'aci da jini, tashi yayi ya shiga daya daga cikin dakunan gidan, ya dauko mata wani kaya tare da sanitary pads ya buga kofar "bude ki amsa!" Budewa tayi ya mika mata, sannan ta rufe ta gyara jikinta, kunya ya hanata fitowa can ta fito sannan tana rike cikinta. "Are you okay!" Gyada kai tayi tana me zama a kan kujeran da ya gyara kamar babu abun da ya faru. Mika mata abinci yayi ta girgiza kai, tana kwanciya a kujeran parlour. "Sannu!" Wayarshi tayi ara. Dauka yayi ya na fadi. "Baby ya dai?" "Papan twins Nur ta farka kamar babu abinda ya same ta." Idanunshi yana kan Layla ya ce. "Alhamdulillahi ina zuwa?" Sai da ya gama waya da ita, can ya kira wata nurse da ya sani a nan Washington, tazo har gidan ta duba Layla ta saka mata ruwa da allurai sannan ta mishi sallama bayan ta gama, kallon Layla yayi hannunshi a gefen fuskarta. "ina zuwa kin ji." Gyad'a kai tayi a hankali sannan ta lumshe idanu, fita yayi daga gidan ya nufi asibitin, lokacin da ya isa da farincikinta ta rungume shi, sai dai kamshin turaren Layla da ta rasa a ina tasan shi ta shaka a jikin rigarshi da ya wanke inda jinin Layla ya tab'a shi, kallonshi tayi murmushin da yake kwance bisa fuskarta ya dauke ta koma yake, "Alhamdulillahi!" Kamar zata yi kuka take kallonshi, tana yake. Sai da suka jima har dare yana asibitin tana lura da yadda yake kallon agogon hannunshi ya ce mata. "Ku zo na ajiye ku, yau ina da wani event da nake son zuwa ne sai zuwa anjima zan dawo!" Gyada kai tayi, tana fa in. "Su sallame mu kawai!" "A'a a bari ta sake murmurewa!" "No muje gida kawai!" "Ok ma!" Ya fada da dukkanin girmamawan da ya dace ya bata, haka yayi magana akan sallame su, dakyar take murmushi amma kuka take a cikin ranta. Ina ma da Layla ce tasan Maina ba zai tab'a mata wani abu na renin hankali ba, haka tasan da kunya yazo mata ya rungume mace, haka tayi ta ha iye kuka da b'acin rai har suka isa gida ya kai mata Nur har dakinta, sannan ya dawo ya wanka ya shirya dama tasan yana fita irin wannan bikin amma sai kamshin da taji a ranta bata gamsu, har ya shirya ya shigo dakin yana son tambayarta yayi kyau amma sai yake ganin rashin amfanin haka. A gaban mirror inta ya karasa shiryawa, wayarshi da ya saita Alarma tayi kara ya dauka yana fa in. "Gani nan!" Sannan ya kalli Aliyyah da taki kallonshi. "Babe zan tafi zuwa an jima zan dawo!" "Ok!" Haka ya fita har ya isa bakin kofa ya ce mata."Uwargida Sarautar Mata babu a dawo Lafiya ne?" "Hmm Allah ya tsare!" "Amin Na gode!" Yana barin kofarta tana fashewa da kuka, har jikinta yana rawa Maina ya samu wacce yake so shi yasa har da gyata mata karya..... Aliyya wallahi wurin Layla zai tafi oho dai ja fa Allah yasa ta ji [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _________________35 Kallon kanshi yayi a madubin motar yana gyara fuskarshi, har zai wuce sai ya ga wani shagon gyaran kai parking yayi ya nufi wu rin, a hankali ya fito daga motar ya nufi shagon aka gyara mishi fuskar tayi kyau sannan ya biya kudi ya fito yana kallon yanayin garin da yake lullubewa da Hadari. Da sauri ya wuce ya shiga motar sannan ya nufi apartment din, bai isa gidan ba sai da ya tsaya ya saya mata abinci da wasu abin bukata, sannan ya shiga gidan da kaya a hannunshi. Bude kofar yayi yana sallama, a hankali ya kunna wutar parlourn yayi Idanunshi ya sauka kanta, tana juyo a tsakar parlour, sake kayan hannunshi yayi ya nufeta da sassarfa ya d'ago ta cak zuwa jikinshi. "Ke Layla open your eyes im here!" Bude idanu tai sannan ta kuma rufewa, tana nishi saboda azaban ciwon ciki. Cak ya dauketa zuwa bedroom din da ya shiga dazun nan, ya kwantar da ita. Kitchen ya dawo ya jera kayan da yazo mata da shi, sanan ya ha a mata tea ya shiga dakin da shi, d'agata yayi ya zauna da ita sannan ya fara bata, kurba daya biyu tayi, ta shiga kwara amai a jikinshi da ita kanta. Duk ta wanke su tass da Amai. Zuba mata idanu yayi yana kallon yadda ta koma ta tura kanta a kirjinshi jikinta yayi laushi yasa shi gyara mata kwanciyarta a jikinshi kafin ya tambaye ta. "Kin gama?" Motsa kai tayi alamar eh, kwantar da ita yayi ya nufi ban aki bayan ya ajiye kofin ya had'a mata ruwan zafi, sannan ya dawo ya kalleta. "Zaki iya gyara jikinki kuwa?" Gyada kai tayi tana kwance. "Ok shiga akwai ruwan zafi kiyo wanka." Shima ya fita zuwa daya dakin ya cire kayan jikinshi ya kara yin wanka, sannan ya duba a cikin kayan da aka kawo gidan akwai wani box na jallabiya da yayi odarsu dafa Oman. Wani cream colour ya dauka ya saka sannan ya nufi dakin, ya samu har lokacin tana dunkule a wurin, daukarta yayi yana fa in. "Ba zaki iya ba ko?" Hawaye ne ya zubo mata muryanta can kasa ta ce mishi. "Ka bari zan yi yalla.." yadda ya ware idanun akanta yasa ta ha iye sauran maganar. "Ki min shiru!" Daga haka ya wuce da ita ban dakin, ya shiga kokarin balle mata kayan jikinta tayi maza ta rike hannunshi kanta a sunkuye. "Na rantse zan iya ba sai ka cire ba min ba!" "Ok ki tabbatar kin yi ko nazo na miki!" Gyada kai tayi tana kallon kasa taki yarda ta kalle shi, yana fita ta jingina da inda ya ajiye ta, kafin a hankali ta shiga cire kayan sai da tazo kan pant din ta mike jiri ne ya kwashe ta, ta fadi sai da ta kwala ihu. Turo kofar yayi ya ganta yashe a kasa, a hankali ya isa tare da cire jallabiyar shi, "ai na gaya miki ba zaki iya ba!" "Papa ka fita zan iya na rantse zan iya!" Ta fashe da kuka, tsaki yayi yana fa in. "Idan ma kada na kalle ki ne, ki ji a ranki ke daya ne a ban dakin babu kowa." Wato ma'ana ta daukaa baya wurin bai kalle ta ba balle ta ji kunyar shi. Rufe kirjinta tayi da suka dan cicciko saboda zuwan period in. Cak ya dauketa zuwa cikin ruwan wani wawan ajiyar zuciya ta sauke kwalla na zuba mata, yana sakata cikin kwarmin wankan dumin ya ratsata, har lokacin hannunta yana kirjinta, dariya ma abin yaso bashi sai ya kyaleta ya shiga zuba mata ruwan a jiki tana kaucewa, juyawa yayi ya dauko wani karamin towel a drowe din bandakin ya saka a can wani roba, sanan ya tari ruwan zafi ya surka ya fara gasa mata jikinta. Ya sannan yadda mata suke jin wannan al'amarin, baya manta lokacin suna tare da Lady Ayrah, tana yin ciwon cikin lokaci zuwa lokaci, shi da kanshi yake nimo masu kula da ita,akwai wata tsoho nurse ita ta gaya masa, idan tana cikin wannan yanayin ya samu wata tana gasa mata bayanta, maranta, don haka ya gayawa Ayrah ita kuma tasa ayi mata har ya mata alkawarin duk ranar da ya mallaketa in sha Allah shi zai na mata, shi har haihuwa a tare zasu yi laulayi su haihu tare ba xai barta da wahala ba, kuma yayi al awarin idan ta haihu shi ne mai renon Yaranshi ita nata basu nono. Bai auri Ayrah ba amma ya cika al awarin shi akan Aliyyah. Ganin hannunshi yana gangarowa kan cikinta yasa ta rike hannun gam. "A'a ka bari!" Cire hannunta yayi ya cigaba da gasa mata wurin, yadda ya matsa wurin yasata cacumarshi tana me boye fuskarta a kafadarshi, sannu ya fa a yana shafa bayanta. A hankali Maina ya wanke Layla, asalima yadda ake wankar zai baka dariya, domin yana kauda kai tare da nuna mata kamar bai san me yake yi ba, omo tass ya wanke ta sannan ya fita ya kawo mata pad da pant sai doguwar riga, sai da ta shirya a ban dakin ya buga kofar dakyar ta fito, ya ajiye mata takalmi ta saka zuwa kan gado, ganin yadda take rawan sanyi sakamakon sanyin ac da yake dakin yasa shi kashe ac in, yadda ake walkiya yasa ta jan bargon, fita yayi ya hado mata abincin, dakyar ta ci ta sha magani, sannan ta kwanta "no ba zaki kwanta ba!" Ya d'agota zaune tana me lumshe idanu. "Zauna abincin ya fa a sai ki kwanta." Haka
Chapter 62 · 0% Book details