Sashe 50
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ki shirya ta zasu koma tare ne!" Dan kallon Sultanah Dilshah Khatoon yayi a fakaice, dauke kai tayi tana fa in. "tashi ku tafi!" Fita suka yi ya maida hankalin shi kacokan kan Sultanah ya ma rasa yadda zai yi da ita amma gaskiya a wannan bangaren bata kyauta mishi ba. "Yanzu kina ganin haka da kika yk akwai adalci a cikinsa? Ni ba kaina nake ji ba, yadda kome zai iya juyawa ya zama banbarakwai!" Wani had'e rai tayi tana fadin. "Ko Malik bai isa na ce ga yadda zan yi yace a'a ko Uwarka bata isa ta ce ban kyauta ba, amma dake kai munafikin Allah ta'ala ne zaka ce ban kyauta maka ba me yasa ka saka ta a makarantar boko? Kasan na. Kyauta maka ba me yasa da zata dawo baka kira ka gaya min abin da ya faru ba sai da bahaya ta gaya min ka sake cewa ba kyauta maka ba sai na kaikaici fuskarka na dinkeka da mari sai dai ka ji tau." Kasa kasa yayi da murya cikin takaicin da baya son bayyana shi ya ce mata. "Hmm duk abin ya biyo baya ke zaki dauki nauyinsa." "Oho dai sai ka tafi da ita, kuma idan ta kosa zan zo na dauke ta na mata mijin da raina yake so." Tsaki yayi kasa-kasa yadda kunnenta ba zai ji ba, don yau ranshi a mugun b'ace yake. Daga haka ya mike tare da barin parlourn, ya fita waje ba karamin matsanancin damuwa yake ciki ba, bai san ranar da zai huta ba. Haka yasa ko da yaushe yake kebe kanshi cikin shirgin mutane, d'ago kai yayi ya kalli hasumiyar masarautar wuri ne aka gyara domin hutawarsa lokacin Kakansu yana raye, can ya a hankali ya cigaba da tafiya cikin nutsuwa domin baki aya baya jin wani nutsuwa, shi mutum ne da baya son shiga hakkin kowa balle har akai ga zalunci. Shi bai zalinci kowa ba baya jin a ranshi za a yi zalunci ya zuba idanu. In fact wannan ba abu ne da za a dauke shi karamin al'amari ba, har ya haura sama yana haduwa da bayi aiku suna gaishe shi. Tunda ya isa wurin ya zauna yaji damuwarsa ta ragu sosai. Ganin shi da bayi suka yi yasa isa bangaren Bazlah aka gaya mata, hada kayan lashe-lashe tayi ta ce yar autarta me suna Maira ta kai mishi tare da jagorancin wasu bayi har biyu. Da sallama suka shiga ta gaishe shi cikin girmamawa da tarbiyya. "Ya Maina inji Mami ta ce a kawo maka." Murmushi yayi yana fa in. "Na gode!" Suka shirya mishi, har suka gama zasu tafi ya kalleta. "Autar Mami!" "Na'am!" Mika mata kudi yayi don tunda yazo yake yawo dasu bai san abin zai yi dasu ba. "La mun gode!" "Oya zaki amsa bana son reni! Ku raba!" "Allah ya kara budi da daukaka, ya biya maka bukatarka duniya da lahira!" "Amin Ya Allah!" Sauran bayan suka amsa shima kuma ya ce Amin. Barin wurin suka yi ya kasance shi daya ne a wurin babu kowa. A can kasa kuwa yara ne suka saka Layla a gaba suyi wasan yar boya, bata so amma haka ta biye musu har yau Nuri darling ce a ranta, tun zuwanta take hada itacce da magungunan gargajiya na mura take ta hada musu. Burinta ta bawa Sultanah da zasu tafi bikin Bahi a kaiwa Sainah tana dafa mata Nuri amma sai gashi zata koma. Murmushi tayi ita ko zata koma don Nur din zata koma, haka yasa ta sake a ranta ba zata kuma yarda Sanah ta mata abin da ta mata ba, don lokacin da Bahi take gayawa Hajja har mata fa a sai da tayi da tace meye amfanin Ummimi a gidan a gabanta ta kira Ummimi ta kuma mata rashin mutunci akan tana ganin za a kashe Layla bata ce kome ba, ita Bahiyyah burinta a bata Layla su tafi gidan aurenta, kirmisisi Hajja ta ce ba zata bata ba, tunda ya sakata a makaranta haka xai zo ya auke ta, ya mai da ita makarantar ita ba za amata wannan iya shegen ba. Ta isa har baihak ta ci mutuncin Hamidah. "Layla muje saman hasumiyar nan, muyi wasan boya don Allah!" Kallon saman tayi ta cewa Yaran. "Wurin hutawar masu gidan ne kada muje!" "Don Allah ko bamu yi wasan ba ki kai mu wurin." Yadda suke mata magiya yasa ta juya suka shiga bin karamar hanyar da zata sadasu da Matakalar, suka haura kuwa har can saman. Shi Maina ya tashi yana ta sakawa da kuncewa. Su kuma suna shiga suka hango kayan lashe-lashe da aka ajiye mishi da sauri daya yaron ya nufi wurin, "Layla Zakir zai tafi can!" Da sauri ta isa wurin tana sha ar kamshin turaren Maina, da sauri ta riko hannun yaron da zai tab'a apple din daidai Maina ya zagayo kenan. "Kada ka tab'a akwai me shi!" Ta fa a tana janye hannunsa, "don Allah ki bari na dauka sai mu raba!" Ha e rai tayi ta ce mishi. "Ai na gaya maka akwai me s...." Kamshin da taji ya kusanto su sosai yasa ta juya ha iye yawu tayi makwat. Zubewa tayi a kasa tana gaishe shi ya dauke kai kafin ya kalli yaron da ya koma bayanta. "Me kake so?" Ya tambayi Yaron cikin kulawa. "Wannan!" "Ku auka!" Hannu ya kai zai dauka ta make hannun. "Allah ya amfana, sanan ta dauka musu. Tare da Mikewa zasu fita ya ce mata. "Kin shirya ne?" Kamar ba shi yayi maganar ba, ya saka waya a kunnenshi yana magana a hankali. Kallonshi tayi kafin ta cigaba da tsayiwa kanta a sunkuye yaran samun abin da aka basu yasa suka tafi abinsu suka barta nan tsaye, yadda yake magana yasa ta juya zata fita ya ce mata. "Hey!" Juyawa tayi ya nuna mata inda take tsaye ta cigaba da tsayuwa har ya gama waya ya kuma sake wani wyaar bai ce mata cikanki ba. Sai da ya gama last wayarshi ya ce mata. "Ku dauko min Laptop Dina!" Diriricewa tayi domin bata san a inda ya sauka ba, haka yasa tayi ta zare idanu tana ta yawo a cikin gidan, kafin wani hikima ta fado mata ta nufi angaren Sultanah Dilshah Khatoon,ta tambayeta. Ita ta saka aka rakata har dakin da ya sauka ta dauki laptop din zata juya ta hango hoton Nuri a saman kayanshi dauka tayi tare da sumbarta goshinta. Sannan ta ajiye ta kalkala da gudu, a lokacin da ta isa ta samu yana ta waya ne, tana haki ta ajiye mishi laptop din. Har xata tafi ya nuna mata ta jira shi. Haka ta cigaba da tsayuwa. Haka ya gama wyaar ya kunna Laptop din yana me cigaba da aikinsa. Wayar shi yayi connecting kafin ya kira wayar Aliyyah. "Fafa! Ina didina!" "Hey!" Ya kira ta da hannu, ya mika mata laptop in. "Didina!" "Nurina! Ya jikinki? Kina shan kunnen madara kuwa? Kinci chips kuwa?" Girgiza kai tayi ta ce mata. "Kullum ana min allura ne!" Kamar zata yi kuka ta fa a tana kallon wayar. "Samun duniyar dan tsako har kin manta damu, Layla!" Ware idanu tayi tana fa in. "Ranki shi da e Sainah ba xan manta da ke ba." Ta fa a tana murmushi. "Yaushe zaki dawo kin san an fara karatu ko anan zaki ci-gaba?" Juyawa tayi ta kalli inda Maina yake, sai ta kama sosa kanta tana zare idanu. "Sai yadda hali yayi!" "Hmmm mu dai ba haka ba ki dawo kawai we need you." Murmushi tayi tana fa in. "Ina Aunty Bahi?" "Hmmm tana Baihak ga Papa ya wani hana mu zuwa bikin ni daya ne babu Sanah, sai Mum itama don Nuri ne yasa bata tafi ba, ga wancan matar yar jaraba Please Layla ki dawo wallahi ina kewarki Deviya ma tana kewarki gashi baki da waya!" Kamar zata tambaye ta Sanah tana iya sai tayi shiru tana ta wasa da yatsunta. Daukar laptop din yayi ya ce mata. "Tana hanya!" Ya kashe tare da mika mata, bai barsu sun yi sallama ba don sun ishe shi da mita d magana. Tana zaune har lokacin sai da ya tuna ya ajiyeta ya ce mata. "zaki iya tafiya!" Da sauri ta bar wurin, ba zaka ce yana kallonta ba, domin da wutsiyar idanu ya bita da kallo, "hey!" Juyawa tayi da sauri. "Ki duba dakin da kika dauko akwai pink box ki auka." Maganar da yake son yi tayi girma don haka ya dauke kanshi ya ce mata. "Kin sake ciwon cikin?" Kamar kasa ta tsage ta shiga ta boya, da bala'in gudu ta bar wurin, tab'e baki yayi domin bai ga abin gudu ba, take tikar gudu nan. Dakin da bata je ba kenan, a can Baihak hidima ake sosai domin kuwa biki ake na gata, duk da Hamidah bata da lafiya amma haka bai hanata saka Ummimi a gaba ba, domin gani take kamar Ummimi tana son kwace mata wani abu daga mutane, a ranar Ummimi ta ga abin mamaki domin har parlournta aka kawo mata Sanaya. "Ga ta nan yarinyar da xan aurawa Maina!" "Allah ya baku Sa'a!" "Ke kika sani!" Sannan ta gaya mata tana jiran Maina. Ita dai Ummimi bata kulata ba, haka ka yi ta hidima har Washi gari da ake da labarin zuwan Maina, wurin karfe biyu na yamma ya iso tana biye dashi kamar wata tail, guard din da ya samu a filin jirgin suna take mishi baya, tun kafin ya isa Motarshi ya fahimci how he's miss Baihak yadda ba zai tab'a furtawa ba, tun kafin ya isa motar an bude mishi, juyawa yayi ya tsaya ka an, yana me sauraron inda zata shiga, bude mata gaban motar aka yi ta shiga shima ya shiga na shi wurin zaman, "Barka da hanya, ranka ya da e!" Shiru yayi na wani lokaci kafin ya dauke kai kamar ya kaita fin era estate, sai kuma yasan Bahi tana ta buwayar rayuwarsa da tura sako ya zo mata da Bahi ita kan tunda ana samun matsala ya taimaka ya bata ita su tafi Egypt tare, bai kulata ba kawai ya ce idan ta dame shi ba zai kawo Laylan ba shi kenan. Haka