Sashe 100
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba, kuma idan na kama mutum sai na kishi kisan kiyashin ba a tab'ayinsa ba!" Ta fada cikin b'acin rai da kunar rai. Domin ba karya ranta yayi azabar b'aci. Haka Ammar ya dawo ya zubawa Sarautar Allah idanu, "Maina baka ce kome ba?" "Me zance?" "Salahudeen baka ji me yake cewa ba ne?" "Na ji me zance tow?" "Kai ban yarda da ku ba, munafuncin me kuke boye mana ne!" *Kada ka sake wani abu ya fito daga bakinka, domin tsaron da yake cikin gidan nan ko fadar shugaban kasa babu!* kallon Maina Ammar yayi bayan ya turo mishi sako ta waya ya cilla da ita. *Meke faruwa ne?* *Kome ma kawai daga yau kada muna haduwa sakon wayar ya isa!* daga haka Salahudeen ya mike yana me barin gidan. Ammar ya mike ya bar gidan. Tabbas Hamidah tayi shiri akansu, ya fahimci haka ne bayan sun dawo akwai dakin da yake cikin dakinsa ta wardrobe amma ba zaka gane ba sai ka bude wardrobe din shima yadda aka.yi design din wardrobe din babu alamar, ta nan ne ya gano an saka abubuwan daukae magana. Abin ya bashi dariya da mamaki kuma a yadda suka.yi abin basu san akwai na shi a cikin gidan ba wanda ya zaga ilahirin Baihak shi dai ya saka ne amma bai damu da yasan meke faruwa ba, sai dai a yadda........ ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/2, 8:23 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________68 Ajiyar zuciya ya sauke lokaci guda yaji yana matu ar kewar Layla, murmushi yayi Yarinya ce karama ce, amma da halin manya, harde hannunshi yayi a kirjinsa yana jin kamar ya tura a dauko Layla. Fitowa Aliyyah yasa shi ya maida hankalinsa kanta tana tafiya a hankali kamar wacce take fama da ciwo. Cikin kulawa yake kallonta, kitchen ta shiga sannan ta fito dauke da kofin tea. "Aliyyah!" D'ago idanu tayi tana Kallonshi. "Baki da lafiya ne?" "Meye matsalarka da lafiyata?" Iskar bakinsa ya furza yana shafa kanshi. "Ina ke miki ciwo?" Banza tayi da shi ta wuce zuwa dakin. "Aliyyah!" Ya kira ta tare da cewa. "Zo nan!" Dawowa tai ta zauna tana ha e rai. "Gani nan!" Murmushi yayi ya ce mata. "Me ye matsalarki?" Murmushin takaici tayi tana fa in. "Ni kake tambaya?" Ta mai da mishi tambayarshi. Girgiza kai yayi ya ce mata. "Zaki iya tafiya!" Mikewa tayi ta nufi dakinta, yayi shiru yana auna dabi'un dukkansu biyu, Layla da Aliyyah. Murmushi yayi yana kallon wuri guda ya ce. "wacce mace da irin nata al'adun, haka zan biku a yadda kuka bukata amma ba zan taba sake dayanku ba" ya fada yana me barin parlour, a bakin kofa ya hadu da dan sakon Queen Hamidah. Shiru yayi yana jin abin da dan sakon yake gaya masa. Bai saurari abin da yake fa a ba, yayi gaba abinsa duk inda ya wuce gaishe shi ake. Lokacin da ya isa bangarenta ya same ta da manyan fadar suna ta tattaunawa ya nime wuri ya zauna. "Yawwa Maina muna tattaunawa ne a yadda za a baka mulki!" Bai yi mamaki ba domin yasan tabbas za ayi haka. "Ni kuma?" Ya tambayeta a sanyaye, "Eh kai domin kai ka fi dacewa da rike madafun ikon masarautar nan!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Tow shi kenan Allah yasa haka shine mafi alkhairi na gode sosai!" Haka aka ajiye maganar za a nad'a shi. *** Tirsila ce tsaye gaban wuta, tana ne caka allura jikin wani dan gwai-gwai. Duk cakawa daya sai ta kira sunan Layla Kalfana, Ruhin Rihanna. Lokaci guda ta cika allura a jikin gwai-gwai din, sannan ta yanka hannunta tare da d'iga jinin a jikin gwai-gwai din, kafin ta wulla shi cikin wuta tana sauke ajiyar zuciya. "Kina tsammanin haka da kika yi zai dakatar da Layla ne? Bayanta sa kin kashe mata kakarta? Ina ta son ki rabu da lamarin Layla amma kaka baki gane ba, ki kyale Layla Amma kin kasa fahimta Layla bata kyale ki don tana tsoronki ba, tayi haka ne don tana kallonki kamar kaka kaka Jami ce na rantse matu ar Layla ta juyo gare ki ba zan tab'a dakatar da ita ba. " "Wai me Layla tayi miki hakan kike sonta ne? Na ga dai duk wani nasararki yarinyar ta kwace? Duk wani abin da nake miki mafarkin samunshi Layla ta amshe me yasa? Don haka idan.na ga bayan Layla kece xaki zauna da Maina zaki yi farin ciki." Murmushi Sanaya tayi tana me kallon Karya kafin ta ce mata. "Har abada ba zan tab'a farin ciki ba domin Layla ta rasa rayuwarta na auri mijinta babu wannan mafarkin, Kaka ki zo mu bar wannan alkaryan don ba zaki iya fada da Layla ba." "Zan iya sai naga bayanta." Ta fada tana kara zuba wasu masifar da take ha awa a wutar. A can garin kuwa barci Layla take, me cike da wahala domin kuwa mafarki tayi gata a gaban wasu mutane, wata mata da bata san wacce ba ta biyo ta zata caka mata wuka Maina ya tare aka caka mishi a baya, zuciyarta na wani irin bugawa ya kwala ihu. Tare da farkawa tana haki. "Mamyn Nuri!" Sainah ta fada tana kallonta. "Me nene?" "Papa zan tafi wurin shi!" "A wannan daren?" "Eh babu kome wurinsa xan tafi!" "Taya?" Murmushi tayi sannan ta shiga ban daki yayi wanka ta fito tana kallon Sainah da itama barci ya kaurace mata. "Kwanta ki yi barci idan gari ya waye ki gayawa Ummimi!" "Tow!" Daga haka ta kwanta. Ita kuma ta juya zuwa waje babu kowa a gidan. "Kalya kin iso!" "Eh!" "Muje!" Juyawa Kalya tayi Layla ta haura bayanta. Kafin suka lula gajimare suka b'ace b'ata. --- Maina yana zaune akan abin sallah,.Layla ta fado mishi a rai. A hankali ya mike yana nad'e abin sallah, iska yayi kamar a bayanshi bakin shi dauke da sunan Allah, ya juya mutum ne a tsaye dake dakin babu haske sosai. "Waye!" Kunna hasken dakin tayi ya kalleta da kyau. "Sultan!" "Kina tsammanin zaki mai da ni Sakarai ne?" "Sultan ni ce fa!" Ya ciro dan kunnenta, ta cakawa hannunta sai ga jini. "Layla!" Ya fada da dan karfi ya nufe ta. "Me ya kawo ki?" "Mafarkinka nayi shine na biyo bayanka!" Bude mata hannu yayi ta shiga jikinshi yana rungume da ita. "Ina kika bar min Ummimi da Sainah?" "Suna lafiya, sannan suna cikin amincin Allah." Rungume ta yayi yana fadin. "Nayi kewarki Yan matana!" Sake shi tayi ta ce mishi. "Kwanciya zan yi!" Haka ta janyo shi suka kwanta. Har lokacin ya kasa yarda ita ce domin baya jin Layla ce ta biyo shi sai dai wani makircin aka hada musu. Abin da basu sani ba kuwa Tirsila kiran Layla tayi don haka ta zo, canza kayan shi tayi sannan ta kwanta, koda ya kwnata a gefenta shigewa jikinshi tayi tana sauke ajiyar zuciya. "I miss you," ta furta a hankali, "me too Baby!" Ya rungume abarshi. Haka suka kwana cikin farin ciki. Wurin asuba bayan ya dawo masallaci, ya samu Aliyyah tana ta kaiwa da komowa. Kai tsaye ya ce mata. "Layla tana nan!" Juyawa tayi tana kallonshi kafin ta ce mishi. "Ban gane Layla tazo ba?" "Eh ta zo jiya Salahudeen ya daukota!" "Y'ata fa?" Ta tambaye shi, domin lokacin da ya ce mata Sainah tana tare da Layla bata damu ba, don tasan matukar Layla tana tare da Yaranta ba zata bari wani abu ya same su ba. Kawai daga sama ya ce mata wai ga Layla ta dawo jiya. Bata san lokacin da ranta ya b'aci tayi ta zazzaga bala'i ba haka kawai Layla zata dawo ba tare da Sainah ba akan me? Bai kulata ba domin yasan idan ya bi na zuciya zai bata mata rai. Duk wannan rigimar da ake Sanah tana jinsu bayan ya shige cikin dakinsa ne ta fito tana fa in. "Mum ki bari ya fita zan ci Ubanta sai ta bar gidan nan!" Haka ta goyawa Sanah baya, dayawan iyaye a haka suke barin yaransu suna shiga tsakanin kishinsu. Lokacin da ya shiga dakin ya samu tana ta kokarin farkawa amma abin ya ci tura, hawa gadon yayi ya rungume ta. Sai gashi ta bu e idanunta. "Sultan!" Ta furta muryanta na rawa. "Na'am beauty!" Kwantar da kanta tayi a kirjinsa. "Ina jin tsoron kada na rasa ka!" "In sha Allah ina nan ina tare da ke!" Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli fuskarshi. "Nayi kewarka!" Ta fada tana tura hannunta cikin jikinshi. Shafa bayanta yayi yana fa in. "Likita yace kada ayi haka baby!" Sumbatar bakinshi tayi tare da mikewa zata nufi ban daki ya ce mata. "Ya?" "Zan wanke bakina ne!" "Dawo nan!" Ya hade bakinsu, rungume ta yayi a hankali yana tsareta tare da iska fadar da ya jima yana kewa, saboda matsalar cikin jikinta babu hayaniya babu kwaranniya Maina yake murza kambunsa. Maina bai kyaleta ba sai wurin karfe tara na same, suka zube a gadon suna sauke Ajiyar zuciya. Kafin ya dauke ta zuwa ban suka yi wanka sosai suka fito. Can bangaren Ummimi ya je ya kwaso mata kayanta, ta saka sannan ya fito ya samu Aliyyah tea kawai tayiwa yaranta suka sha. Nuri na ganin Layla ta rungume ta. Ita kuwa Layla ta rungume abarta don tai kewarta. Kitchen suka shiga ya ajiye musu kujera suna hira, ya ha awa Layla tea me kauri sannan ya bata, Nuri kuma ya ha a mata juice. Suna zaune yana aiki sai hira suke suka dariya. Aliyyah ta fito ita da Sanah, "Papa!" "Na'am!" Ya amswa Sanah yana kallonta. "Dama ina son fita ne." "Zuwa ina?" "Zuwa garden zan ciro gwaiba ne." "Bana son fitarki ke daya jira na dauko miki!" Ya ajiye abin da yake yi, haka kawai Layla ta ji jikinta ya bata rashin mutunci zasu mata zai fita ta rike hannunsa. "Duk abinda ka dawo ka samu kada kayi mamakin yadda ka same shi!" Shafa kanta yayi ya kalli Aliyyah da take tsaye. "Ki kare kanki ga duk wanda ya farmake ki, ina tare da ke." Daga haka ya fita kamar