Sashe 21
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ta bugu da bango, ta fara ganin dishi-dishi har kofar ta rufe. Daga nan bata kuma sanin inda kanta yake ba, sai after few hours. Tana bu e idanu ta ganta daure da sarka a wuyarta da hannunta. Farkawan ma ruwa aka watsa mata, a hankali ta dawo hayacinta. Kalaman Kalya ya dawo mata. *Zuwa yanzu rayuwar Layla ta zama abin farauta. Tirsila ta karya tsaron wagadu ki nisanta Layla ga wagadu domin zasu iya cutar da ita* murmushi kaka Jami tayi lokacin da Tirsila take tambayarta. "Ina kika kai Layla!" Dariya ce ta kwace mata, "zai auke ku shekara daya biyu uku hudu goma kafin ku iya samota, ita kuma daga ranar da ta fahimci jinin ahalinta kuka tab'a zai d'auketa awa ashirin da hu u ta bayyana a gabanku." Mari Falwa ya tsinka mata, tare da rike gashin kanta. "Ina jikar Zafir take?" Yawu ta tofa mishi. "Tababbe maciyi amana, ka fara gudu domin bayan uwargiya da take kanta, uwar gijiyoyi goma suke rufe mata ba..." "Jamimah ina kika kai Layla?" Murmushi tayi ta ce mata. "Ki nimota mana." Kaka Jami ta kalli yadda jinin al'umma yake gudu, aka kawo wasu gabanta Tirsila ta ce mata. "Ki gaya mana ina Layla take ko na saka a kashe su?" Kallon mutanen tayi da suka yi imani da ita. "Koda na fada muku, ba zaku kyale su ba, me zai hana ku kashe ni madadin su." Harbi aka sake musu, duk suka fadi matattu. Rintsa idanu tayi tare da d'ago kai tana murmushi. "yaku Jama'an Wagaduwada, kunga kenan Kaka Jami ta nuna ran Layla yafi naku. Me kuke ganin ayi mata?" Tsirarun mutanen da suka rage, suka zubawa Kaka Jami idanu, kafin suka sunkuyar da kansu, for long time bata tab'a cin amanarsu ba, iya daidai gwargwado tana kare hakkinsu, koda kuwa Layla bata kyauta musu ba. "Falwa a kashe Jamimah!" Dariya yayi yana kallon Tirsila. "A'a jininsu yana had'e, duk inda yarinyar ta je zata dawo niman Jamimah idan muka kashe ta, babu wani amfani ko alfanu domin ba zamu tab'a samun yarinyar ba." "Ya aka yi ban yi tunanin haka ba?" Ta fa a tare da nufar kaka Jami, ta shafa kafarta tare da dibar kasar wurin ta saka a kunnenta. Wani irin iska ne me karfin bala'i ya shige da kasar cikin kunnenta. Kara ta sake tare da watsar da asar jini ne ya shiga zuba daga kunnen, Tana kallon kaka Jami da take murmushi hawaye na zuba mata. "Me ya faru?" Inji Falwa Duba kunnen yayi yaga jini yake zuba, abu ya dauka ya toshe kunnen. "Jamimah zamu barki a cikin mutanenki amma ina Layla take." Shiru tayi tana murmushi. "Ba zata fa a ba mu bar wagadu. Haka suka dauki kaka Jami kawai, ita daya ba tare da sun hada da kowa ba, suka bar garin baki aya. Sai a lokacin sauran mutanen da suka saura, suka shiga fitowa ana binne gawarwakin mutanen da aka kashe. A hankali suka tattara kome ana ta koke -koke. Daga nan Malamin majami'a yayi addu'a tare da cewa. "Kun ga abin da ya faru, yadda Tirsila ta ci amanar Uwargijiya da Kaka Jami, tow ba makawa zamu dukufa wurin addu'a domin Uwargijiya ta kawowa Kaka Jami dauki, sannan duk inda Layla take ta samu kariya." Al'amarin Layla kuwa ita da Haeda, iskar tsafi me karfin tsiya ya raba su ne, yayinda karfin iskar ya sumar dasu baki aya, Layla ta fada cikin ruwan Baihak, ita kuma Haeda ta tafi wani bangare na cikin kasar. Lokacin da fada cikin ruwa Magariba ya fara yi, babu wanda ya sani. Sai da asuba dattijo Salis ya fito niman abin da zasu ci inda ya hau ruwa yin su domin ya samu na kalace da yan jikokinshi, watsa komar shi yayi can ya fara ja, a hankali ya janyo da ita. Tsoro yasa shi jin kamar zai kifa, ganin da gaske mutum ce yasa shi janyo ta ya saka ta cikin jirgin dakyar, ya duba bata yaji numfashinta yana nan, su din da bai yi ba kenan. Ya fito da ita daga ruwan ya dawo tudu, ganin safiya ce, da sauri ya wuce da ita gidanshi, yana isa gidan sulallar zinari yana zuba daga cikin aljuhunta. Cikin tsoro yake kallon Layla baki aya bata mishi kama da mutanen Baihak ba, sannan yafi tunanin satota aka don kada ta tuna musu asiri aka jefata cikin ruwa. Haka ya fita makotarsu ya kira wata mata da take aikin magani na gargajiya, ya kawota ta duba Layla. "Zata farka da Yardan Allah, amma kasan dai yarinyar nan kyanta yayi yawa, idan Hakimin ruwa yaji labarin nan zai hukuntaka ya auke ta zuwa Palace din Baihak idan da shawara ka maida ta namiji." Yayi shiru. "Hajar taya haka zai faru? Mace fa." Murmushi tayi ta ce mishi. "Wannan ba matsala ba ce, kawai dai ita ce zata sauya shigarta. Zan kawo mata duk abinda zata bukata." "Ina tsoron kada a kama mu." "Babu abunda xai faru, sauran yan matan da aka shiga da su ka.ji labarin sun dawo ne? Abu ne na rashin imani kawai ka kula da ita!" "Kin ga abin da ya fito daga jikinta!" Ya nuna mata silan zinari. Murmushi tayi ta ce mishi. "kana ikon Allah ya baka.yadda xaka yi shine ya turo maka da ita lokacin da talauci ya maka kamun kazar kuku." "Hajar nawa xan biya ki!" Girgiza kai tayi tana fa in. "Idan ta farka ka dawo da ita wurina, ina son Y'a mace duk Yarana sun watse." "Nima ina sonta, ba don abin hannunta ba sai ganin ta nake kamar tana da gobe me kyau kamar zinarin nan!" "Ashe tunaninmu daya." Haka suka ajiye zancen tare da komawarshi gidan Mai magani Hajar, domin kawai Layla ta tafi da zuciyarsa. A cikin fadar Baihak kuwa tana can a karkashin kasa, sun daure ta da sarkokin hannu da kafa da wuyarta. "Zuri'arku sun jima suna amfani da yardan mu,domin bamu abin da Allah ya dakatar damu, taya zamu kyale ku bayan mun samu biyan bukata? Gaya min ina Layla take?" Kallon Queen Hamidah tayi tana fa in. "Layla? Tow ku nimo ta mana!" Kifawa kaka Jami mari tayi, "na rantse da Allah, idan na ganta da ranta xan yanke namar jikinta har sai ta mutu.". "Kiyi fadar ku hadu lafiya ba tare da yasan wacece ke ba, daga lokacin da tasan kin kashe mata iyaye kin kama ni, kare ma ba zai kalli gawarki ba, ni ba hango mutuwr da zaki yi, mafi munin da takaici " sake marin kaka Jami tayi tana fa in. "kirata!" "Koda wasa ba zan kirata ba!" Juyawa tayi ta kalli Malik da yake tsare jikin wani koren wutar tsafi, ya ciro karfen da yayi jajjur ya kawo ya danna akan cinyar kaka Jami, tare da toshe mata baki, wani irin gurnani take zufa na karyo mata, tana ihu me azabar radadi. Gurnanin da iska ya dauke shi yayi ta yawo da shi har ya fita ta wata yar karamar kofa, ya fita cikin iska ya baje. Karfin jini da kuma shakuwa, ya saka iska niman inda Layla take, sautin gurnanin ya daki dodon kunnenta bude idanu tayi tana fa in. "Kaka Jami?" Ta tashi zaune sulalar suka zubo baki aya. Kallonta wata matashiyar budurwa kamarta tayi, tana fa in. "Sannu kin tashi!" Mikewa tayi zata fita ta riko hannunta. "Baiwar Allah ki nutsu,yau ba a fita rana tayi idan kika fita mutanen Malik zasu tafi dake fadarshi an zo niman Yan mata ne." Shiru Layla tayi ta fashe da kuka, tare da komawa ya kwantar da kanta, tana jin nishi da gurnanin kaka Jami, " a ina take?" "Waye?" Yarinyar ta tambaya. "Kakata!" Kallon mahaukaciya ta fara mata domin taya za ata san inda Kakarta take girgiza kai tayi tana fa in. "Ban san inda take ba " Zama.tayi ta rushe da kuka, domin ta fahimci tana nesa da Kakanta. Jin ana arin shigowa kakan yarinyar yana musu bayani babu yan mata a gidan, duk yara maza ne. Itama yarinyar ta rude, A hankali Layla ta kalli kofar da yake rufe, yarinyar ta fashe da kuka. Ganin dakarun sun iso kofar suna arin... #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s *MASU NIMA DAGA FARKO DON ALLAH GA LINK NAN SU SHIGA ZASU SAMU* *Yanzu sai ku rena pagen Ni fa yar baiwa ce me faffutukar niman Money ________________10 *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*