Sashe 45
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* ______________________ ________________23 Cikin kanshi yaji muryanta, ya ware idanu don mamaki da al'ajabin ganin yadda take amsa Questions din babu b'ata lokaci ko inda-inda yasa baki aya yaji babu amfanin tsayawa, tafiyarshi yayi domin yana da wani meeting da Committee din world bank, wanda suka zo tun jiya. Yana fita ana kiransa a waya, dauka yayi can kasa kasa ya ce. "Ina hanya!" Ya kashe wayar, minti biyar ya kai shi bankin yana shiga Teemi ta tare shi da bayani, tana fa a mishi duk tsare-tsaren taron. "bayan shi akwai wani meeting ne?" "A'a kawai dai wannan ne kuma har yau chairman bai ce kome ba." Iskar bakinshi ya furza sannan ya ce mata. "Ok mu shiga!" Daga haka suka shiga meeting, sun jima da turawan tare da babban sakatariyar bankin duniya, Mss Ngozi nkonjiwela, tsohuwar ministar kudi, ganin yadda yake bani ta kalle shi, sak ta ji ina ma Nigeria zasu samu irin Maina tana ganin da babban bankin Najeriya zata samu tagomashin arzikin, sai dai yadda suke tare da wasu manyan aikantan kuma gogagu a harkan hulda da jama'a yasa take jin ba lallai yazo Nigeria yayi aiki ma, bayan an tashi break ne take tsokanarshi murmushi yayi yana fa in. "Ina son Nigeria, musamman Arewacinta." Gyara tsayuwar tayi sannan ta ce mishi. "tabbas ko ni aka bani zabin zama a Nigeria zan zab'i arewa domin bana manta tsohon shugaban kasar Alhaji Umaru Musa Yar'adua Marigayi, ba karamin shiri yayiwa kasar ba, sannan har yau ginin Da yayiwa kudanci suke kan cigaba, wa anda suka kashe arewa yan siyasar arewa suka kashe ta. Amma idan kana niman zakwakurai hazikai, masu ilimi da fasaha suna arewa, wa anda suke ilimi bana bogi ba, suna arewa ko anan akwai wani Yaro matashi da muke tare da shi, tare muka zo kasar nan dashi dake yaro ne yasa na mishi uzuri yayi yawon shi. Amma arewa ta wasu fannonin anci gaba ta wasu fannonin kuma sai a hankali. " Murmushi yayi dake ba yawan magana ce da shi ba, sai ya ce. "Haka ne, Allah ya kawo mana mafita!" Daga haka suka koma meeting din. A can makaranta kuwa wani abin mamaki ajinsu Saina aka kaita, da farin ciki Saina ta nuna mata wurin zama ta zauna, uniform ne black and white, skirt din black sai dogon legis black, sai farin slaveer shirt, sai black jacket top, sai bakin hula da ta saka, tayi kyau domin takalmin kafarta ma baki ne. Zama tayi tana maidawa Sainah murmushi. Kafin ta juya tana kallon Sanah da ta wurga mata harara. Kallon allon tayi da malamar take ta bayani, sai da ta gama bayani kafin ta gabatar musu da Layla Muhammad Hatim. Sannan Malamar ta fita, tana fita Sanah da kawayenta suka taso zuwa wurin Layla suka tsaya akanta. Mikewa Layla tayi ta ce mata. "Kina bukatar wani abu ne?" "Bana gaya muku, baiwar gidanmu ba ce, kun san Papa crown Prince ne!" "And so what?" Inji wata Yarinya yar figigiya da ita ta juya tana kallonsu. Cikin jin haushi suka ce mata "Class captain bamu yi dake ba." Inji wata yar lukuta. Takaici yasa ta juya baki aya ta ce musu. "Ku koma ku zauna." Wucewa suka yi suna kunkuni. Murmushi Yarinyar tayiwa Layla ta ce mata. "Hi sunana Deviya Vasidram Nandu." Kallon Sainah tayi tana me gyada mata kai. "Layla Muhammad Hatim!" "Ke yar uwar Sainah ce ko? Naga surname dinku aya." "Yar uwarmu ce, yar coursin din Papa ce iyayenta sun rasu." "Karya kike Baiwarmu ce aka kawo domin tayi renon, little sister dinmu Banafsha shine sister din Papa tace a saka a makaranta tayi ilimi ta waye, ta daina abubuwa irin na jahilai yan kauye, nayi mamakin da aka kawo ta class dinmu." Da karfi take maganar yadda kowa sai da ya juya yana kallon Layla da tayi tsuru-tsuru kanta a kasa. "Sanah sai na gayawa Papa, abin da kike aikatawa." "Sai nace mishi tare muka yi mata rashin mutunci." Haka Malami ya shigo suka ki bashi hadin kai karshe sai da ya kira shugaban makarantar ya tsawata musu. Duka duka suna aji biyu ne na Secondry, amma rashin mutuncin da yaran nan suke zaka dauka sun kai aji biyar ne, kuma wani abin takaici shi ne dayawan Yaran yayan manya ne, ita Deviya Vasidram Nandu babanta dan kasuwa ne anan Scotland. Bata shiri da kowa har gara Sainah suna gaisawa. Sainah a ra'ayinta tana gama aji uku bodin school zata shiga, Sanah ita kuma anan take son cigaba. Bayan an tashi break ne suka tafi cin abinci. Sanah tana zaune su Sainah da Layla suka shiga, tana ganinsu ta kira Layla zata tafi Sainah ta rike hannunta. "Kyale ta." "A'a zanje." Tana zuwa ta ce mata. "Kina bukatar wani abu?" "Abinci zaki amso mata!" Ta wuce tayi ta amso musu har su hudu ta kawo musu,tana zuwa amsar nata aka koma aji. Ajiye tiren tayi ta juya zata tafi me zuba abincin dattijuwa ce ta ce mata. "Burnana!" Juyawa tayi cikin mamaki, haka kawai matar fuskarta ya koma kamar na kaka Jami, hannu ta saka bakinta. "Zo ki diba!" Hawayen da take rikewa ya zubo mata, ya zuba abincin sannan ta samu wuri ta fara ciki, tana kallon matar tawowar Sanah suka dauke tiren suka watsa mata baki aya abincin. Ture su Deviya tayi tana fadin."Zan yi report dinku ga shugaban makaranta, sannan CCTV yana daukar duk abinda kuke yi." "Oh sorry" inji Sanah kafin ta kwashe ketchop din tayi ta shafawa fuskar Layla, ture Sanah aka yi ta fadi Sainah ce tana huci, ta riko hannun Layla suka tafi restroom. Ta wanke jikinta da fuskarta sannan suka wuce class. "Sister dinki ce ta ture ki fa? Kuma kika kyaleta." Kwafa tayi zan gayawa Mum dinmu ai." Haka kawayenta suka yi ta zugata har aka tashi Auta yazo ya dauke su, tun anan ya fahimci Layla bata yi murnan fara makarantar ba, suna isa gida suka ji labarin an dawo da Ayrah gida, tun da suka dawo Sanah take kuka dakyar ta gayawa Aliyah abin da yasata kuka, kiran Layla tayi ta mata fada sannan ta kira Sainah ta kwakwad'a mata mari, sai da tayi kuka tace babu ruwanta da Sanah idan tana saka Layla aiki. A tare da Layla suka ci kukansu, ita Layla tasan haka xai faru dama, Washi gari ma auta ya kaisu makaranta. Rashin mutunci sai wanda ya karu, Sainah bata da bakin magana, a haka suka ta karatun da layla ba fahimtar shi take ba, ba wai ba zata iya kare kanta ba ne idan ta ce zata rama akan irin wannan abin zai zama bata da juriya akan duk abinda zai faru, yakin da yake gabanta babba ne, rashin mutuncin Sanah kuma ba kome ba ne, ko don albarkacin Nuri darling da Sainah ba zata rike ta ba. A haka suka kwashe wata uku, kafin suka yi jarabawar farko. Tun kafin ayi hutu result ya fito ba laifi na Layla yayi kyau na Sainah da Deviya ta fi kyau, dama sune gurayen class din sai wani Yaro me suna Adamson, shi yafi Deviya da aya ita kuma Sainah ta fishi da tazarar maki biyar. Kusan Layla ce karshen class amma ba laifi. A cikin wata uku da tayi tana zuwa makarantar, bata kuma jin labarin Papa ba domin baya ma zama. Ranar da aka yi hutu take jin labarin Ya dawo a bakin Nur din, da ta bata magani duk yarinyar ta kare yar lukuta me ban sha'awa. Haka ta fige kamar ba ita ba. Suna can abinci, Layla ta lura da Bahi da take ta murmushi. A wannan rashin lokacin da basu zama a gida ashe har ta hadu da wani dan kasar Egypt mai suna Mubarak ya kuwa makale mata, zancen da ake har yana son ganin Maina next dake Maina baya zama aikin da world bank suka dauke shi zai yi wani banki a can Washington DC, haka yasa yake son su Sanah su gama aji uku sai a maida su can su cigaba da karatu. "Aunty Welcome to true love world!" Dariya Bahiyyah ta fashe suka shiga hiran Mubarak dan wasan wallon kafar real Madrid ne, da suka zo buga wasa da Europeanship, kamar da wasa suka hadu wurin daukar turare ya kai hannu ita ta rigarshi dauka. Don dole ya bar mata kuma ya saya mata, ya kuma sayi wani daga nan suka kama dariyar abin da ya faru aka yi exchange number, daga gaisawa aka fara soyayya. Gashi yanzu manya zasu shiga cikin maganar. Sati na zagayowa Maina ya gana da Mubarak, sun fahimci juna kuma Maina yaji dadin yadda ya samu mutum irin Mubarak dan kishin yankinsu na larabawa, daga nan Maina ya tura shi wurin Salahudeen da Ammar, suka mishi iso wurin Malik ba laifi Mubarak kakaninsa da iyayensa attajiran an kasuwa ne, uwarsa kuwa yar gidan Sarautar Askandariya ce, haka yasa Malik ya ce ya tafi zai magana da magabatan shi. Ai kuwa haka ya faru sati guda dai ga dangin Mubarak aka bada auren da bikin da kome akan nan sati hu u. - Duba result dinsu yake yana kallon Sanah da takaici ya kusan sakawa ta tashi ta rufeta da duka. Ko Layla ta fita maki da tazara me yawan gaske. "Wannan shine sakamakonki?" Ya tambaye ta, kanta a kasa tana kuka sannan ta bude doguwar wasikar da aka turo miki na abin da take yi a makarantar. "kira min Mamanku!" Ya fa a yana kallon Sanah, Sainah tasan da ita yake don haka ta wuce waje tana rawa. A tare suka shigo da Aliyyah. Mika mata takardan yayi ta duba. "Papa sharri aka mata fa. Amma ai Sanah babu ruwanta." "Haba? Sharri ne kenan aka mata ba yiwa wancan yarinyar da Sainah ba?" "Kayi hakuri tayi laifi!" Domin a yadda ya dauki zafi tasan yanzu zai iya harzuka. Hakuri ta cigaba da bashi ya