← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 115

Sashe 86

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba zai ji daga gare ni ba, don haka ki kyale su. Ai ita ba'a yi bikinsu ba a nan, ita ayi haka kawai." "Kina nufin sadaukar da bikinki ki kayiwa Aliyyah?" "Tow meye a cikin? Shi mijinta yana son haka don haka ki kyale su!" Zata kuma magana aka turo kofar. "Ni ne mijinta?" "Kaico!" Ya fada tana dafe goshinta. "Nace Ni ne mijinta? Bama Mijinku ba!" Sunkuyar da kai tayi tana murmushi. "Me ya sa kika rena Ni?" "Ban rena ka ba, kai ne baka fahimce ni ba." "Kada ki rena min hankali." "Amma dai wallahi ka ba ni mamaki sai ka je can kuyi ta fama da matarka ita kuma Allah ga wa ka kyaleta tunda bata gabanka!" Inji Ummimi. A fusace ya fita murmushi me ciwo Layla tayi. Duk rabin abin da ya faru a kunnen Jasy, abin ya bata mamaki don haka ta nufi bangaren da ake bikin ta riko hannun Aliyyah. Suka fito daga hall din. "Me kika aikata?" "Ni kuma? Me xan aikata?" "Amma bikin Maina da Layla ne ko?" "So what?" Ta fa a tana ware idanunta. "Amma baki da adalci wannan ba adalci ba ne." "Hehe Malama kada ki ce zaki fara koya min abin da xan yi don haka biki kika zo kuma zaki koma idan tsarin bai miki ba ki je bama maraba dake!" "Aliyya sai kinyi cusawa wanda bai nufeka da sharrin ba bakinciki." "Ni sau nawa suka cusa min, har gidana yazo ya kwanta da ita ina jin ihunsa da kome da bance xan kwanta da shi ba mijina ne kuma na kwace abuna sai dai masu mana bakin ciki su mutu." Tana gama.fadar haka ta juya abinta. Sai yamma likis Haida suka iso da kayan biki, tunda Layla ta ganta ta kwanta a cinyarta. Kuka take son yi amma wani abu ya tsaya mata a kirji ta kasa kukan sai lumshe idanu tayi. Ranar Lahadi aka shiryata zuwa bangaren Queen Hamidah, suka gaida ta sannan suka fito inda ake hawan daba, aka fito da ita a matsayinta Na Amarya domin Bahiyya da Haeda sun ji zafin abin da ke yi, ko cikin dare sai da tazo suka fita waje. "Naji wani babban al'amari a cikin gidan nan!" "Eh ana hada wani kazamin tsafi ba!" "Ashe kin ji haka!" Murmushi tayi tana kallon Haeda. "Ina ravi!" "Ya wuce wagaduwada!" "Allah Sarki!" "Kina ganin me ya dace a yiwa Aliyyah!" Dariya abin ya bawa Layla ta ce mata. "Kuma sai mu mata asiri don rashin adalci? " "A'a mu koya mata hankali!" "Ina ruwan sarauniyar matsafa matar Maina ko sai na mata wani abu don ta bar min mijina! Hmmm babu tsafi tayi kissarta ni nawa zai zo bana tunanin hanyar da ya dace na rama abinda tayi min kenan, zuba idanu ki ga yadda ake wata kissar sai mata." "Amma dole zaki fita kallon hawan daban!" "Kalar kayan da zai saka nake son Kalya ta nimo min!" Ta shafa wuyarta. "Uwar dakina gaya min na cika miki!" "Kayan da Maina zai saka nake son zan saka!" "An gama." Ta B'ace."me kike so gobe!" "Jikina yana bani akwai wani abu a tare da bikin da Queen Hamidah ta hada gobe. Duk rantsi kada wani abu ya samu Maina." Anan suka shirya zazzafar shirin su. Kafin suka watse a daren zuwa wurin kwanciyarsu. Washi gari aka tashi da hawan daban... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/18, 12:14 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu _Alhamdulillahi Ubangiji ya saka muku da alkhairi Allah ya bada ladan ta'aziyan da kuka min Ubangiji ya jikan iyayenmu da magabatan tare da Al'ummar Annabi Muhammad SAW_ _________55 Kwanciya tayi amma zuciyarta yana wurin Maina, baki aya sai juyi take a hankali ta shiga ban daki ta sake ruwa akanta, me sanyi kalau. Har tana jan zuciya tabbas tana bukatar Maina a wannan daren amma tunda ya juya mata baya zata yi hakuri. Sanyi ne sosai ya shiga jikinta har ta fito waje. Ta hau gado ta kwanta tana rawan sanyi, a hankali ta fara atishawa jikinta ne ya fara wani irin kerma wanda har gadon yana jijjiga, sai da Bahiyya ta farka, ta fara kokarin fita ta ce mata. "Dawo ba kyau fita a wannan daren, in dai Sultan ne yanzu zai shigo ya farka." Ta fada tana kara rike bargon, shima a cikin barci ya ji kamar tana kiranshi haka yasa shi farkawa ya saka rigarshi ya fito zuwa bangaren Ummimi. Koda ya zo dakin ganin Bahiyya tana jibga mata zanuwan gado yasa shi rike hannunta. "Muje ki kwanta." Ya fita da Bahiyya har dakin Ummimi ya ce mata. "Sai da safe!" Ya wani juya tare da hade rai kada ta rena shi, don farin ciki bata san lokacin da ta fara taka rawa ba, lokacin da ya dawo dakin janye bargo da duvet din da aka rufeta da shi yayi. Ya shiga tare da rungumarta a jikinshi. "Kada ki ga haka ki dauka na zo bukatar wani abu ne, nazo na taimakawa yanayinki ne!" Ya fada yana mita, a hankali ya kara rungumarta sosai tun tana rawan sanyi har barci yayi gaba da ita ya sauka a gadon yayi sallah a dakin sannan ya mata addu'a ya fita. Don idan ya tuna tace bata son shi abin kara bata mishi rai yake, lokacin da ya koma dakin Aliyyah tana ta barcin tow abin da ta dauka ya mata yawa. Tun asuba da ya farka ya je masallaci bai koma bangaren shi ba, wurin Ummimi ya wuce ya samu Layla ana gyara mata gashinta. "Waye ya tashe ki?" Ya tambaye ta yana tsare ta da idanu. Langwabar da kai tayi tana kallonshi. "Abinci na tashi naci shine Mama tace a gyara min gashina ayi kafin lokacin zuwa kallo yayi." "Kin samu lafiyar fita ne? Ina kullum Aliyyah tazo ta miki magana cewa kike ba zaki ba, ta je." Cike da mamaki Layla ta kalle shi sai kuma ta ce mishi. "Shi kenan ku je ni zan tafi wagaduwada yau!" Ya fada bata yarda ya kalleta ba, gudun kada ya lalata mata shirinta. "Ban gane ba? Da izinin waye zaki tafi?" Sake kanta me gyaran gashin tayi ta mike ta fita ita kuma Layla tana kallonshi ta ce mishi. "Tafiya xan yi wurin sauran al'ummar da suka rage su rike Ni!" "Ke Layla ina wasa dake ne?" "Gaya min me nayi maka?" "Da kika ce bakya sona!" "Oho na zata wani abu nayi na daban ashe don nace bana son tsoho ne kuma ai ba karya nayi ba, ba kai nake so ba Ifraz nake so, kai min shigar sauri ka raba ni da shi!" Cak lissafin Maina ya tsaya ya kura mata idanun. "Kaga tunda babu wnada ya san da auren mu ka sake ni naje na aure..." Bata san yadda aka yi ba ta dai ganshi kamar zai yi sama da ita ta koma jikin bango tana tura baki. "Wallahi sai na saka an sare mishi kai!" "Ka tab'a min masoyi ba zan yafe maka ba!" Jin shi yayi kamar ana rusa mishi kanshi da duwatsu ya ce mata. "na rantse da Allah sai na sab'a miki!" Cikin tsiwa ta ce mishi. "Oho dai kada a tab'a min masoyina!" Ta rab'a gefenshi zata wuce ya fisgota. "Layla Aisha!" "Yaushe na muslunta da zaka saka min Aisha!" Ta fada tana tura baki, "sai na miki rashin mutunci!" Daga haka ya fita dariya tayi tana fa in. "Sai na hanaka sakat a masarautar nan!" Daga haka fito da kayan da zata saka wanda Kalya ta mata, murmushi tayi tana kallon kayan. "Haed!" "Na'am Layla!" Murmushi tayi tana fa in. "Kin shirya kome?" "Eh!" "Shi kenan!" A hankali haeda take taimaka mata ta gama saka kayan, sannan ta dauko alkyabba ta saka, mai kwalliya tazo ta yi mata sannan aka tabbatar ta shirya. Turaren riyal ta saka sai wani kamshi take kamar zata zautar da me jin kamshi. Parlour suka fito Ummimi ta zuba mata idanun tare da fa in. "Barakallah!" Murmushi tayi tana zaune, can sai ga Maina ya shigo, wayarta da ta saka a silent ta saka a kunne can asa kasa ta kashe murya tana fa in. "Please kazo mana, babu abin da zai faru!" Wani kalar shagwab'a me sanyi tayi tare da wani kukan rigima mara tushe balle makama ta ce"hmmm!" Tare da wani dan girgiza kafin ta kara da cewa. "please kazo na ganka ko sau daya ne!" Fauce wayar Maina yayi bai tsaya duba fuskar wayar ba ya kashe baki aya ya saka a aljuhun wandonsa. "Kuma ba zan kara baki wayar ba!"ya fada yana watsa mata harara. Fitowa Ummimi da Haeda suka daga cikin. Kamar zata yi kuka a wani narkakken yanayin shagwab'a me kashe ruhi da zuciya ta wani narka fuskarta ta ce mata.."Ummimi!" Yadda tayi da bakinta ya kara haukata Maina wanda bai san dama can ya jima da haukar ba. "Na'am Layla! Me nene?" Ta tambaye ta cikin kulawa. "Ki ce ya bani wayata!" Ta fada tana tura baki. "Baban twins bata wayarta mana, wannan ai cin zali ne!" Kamar dama tana jiran Ummimi tayi magana ai kuwa ta kama kwal-kwal da idanun. Wani irin abu Haeda taji baki aya tausayin Layla ya cika mata zuciyarta, sunkuyar da kai tayi tana tuna Kaka Jami. Duk wannan shagwab'ar da wa kaka zata yiwa. "Ummimi yarinyar nan bata jin magana!" "Kai kuma baka da hakuri!" Mika mata wayar yayi yana fa in. "Biyo ni!" Daga haka suka fita, suna fitowa mamaki ya kama Aliyyah da take kallon Maina da Layla tayi maza ya kama hannunshi, kallonta yayi ta wani narke mishi. "Kada ki sake ki bata min wannan kwalliyar na gaya miki!" Tura baki tayi tana fa in. "Bayan baka ce nayi kyau ba, na san da Ifraz ne!" Matse hannunta yayi yana fa in. "Sai dai ifiritu!" Ba fada ba kome Layla ta dawo da Maina jikinta ta hanyar gaya mishi wanda take so yana wurin, "Baban twins Ina son magana da kai!" "Sultan na tafi ne kasan bana iya jure tsayuwa!" Baki aya suka saka shi a tsakiyansu. "Ina zuwa!" Yabi Aliyyah, ta juya
Chapter 86 · 0% Book details