Sashe 16
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Maina ya juya a daren ya bar masarautar duk da Halifa Abu Ammar yana kiranshi ina ya tafi, a daren ya bar kasar, garin gudu ne dake a rikice yake gani yake kamar ana bin shi, suka buge wata mata. Wacce itama take gudun ceton ranta, haka suka dauketa zuwa asibiti. Daga nan shi ya bar kasar yadda zaka gane baya cikin nutsuwar shi, har ya iso Texas a firgice yake, ya sani masarautarsu cike take da zalinci amma yaga an kashe rayuka goma rus ko a tarihi bai ji ba, akan idanunshi aka kashe su, ji yake kamar zai yi hauka, jinin da ya gani ya haura mishi kai, haka Aliyah ta kira Ammar yazo ya dauke su, suka tafi wurin dangin Mamanshi, a can ya sha jinya sosai. Idan abin ya motsa mishi yayi ta firgita kenan kan wannan mutumin yana razana shi, a wani dare abin ya tashi, Aliyah tana arin kwantar mishi da hanakali, abubuwa dayawa a daren suka sauya, domin ya samu nutsuwa da ita. Sama da yadda ake tsammani. Ya kuma shiga hankalinshi kamar yadda ya gabata. Tun faruwar haka da samun lafiyarshi, kusan suna tafiya kafada da kafada. Haka yasa shi bibiyarta cikin dare ya turmusata, da safe ya tashi yana ha e rai da tsume fuska. A nan ta samu cikin yan biyu, kafin suka koma Texas inda ya kare karatunsa, ya kuma samu aiki a Norway. A can yayi aiki har ta haihu, tsawon shekaru goma suna suna can, a lokacin bata haifi Nuriyya ba, sai da aka dawo da shi Scotland ta samu cikin Nuriyya, kusan shekaru goma sha biyu, rabon shi da Baihak har Salahudeen yayi aure ya haihu bai taka zuwa kasar ba, sai dai su zasu zo mishi. Queen Hamidah ma taso mishi lokacin haihuwar Nuriyya domin bata san yan biyu ba, sai da ta gansu anan ne ta fahimci cewa Maina baya kaunar dukkan abin da zai alakatanshi da masarautar Baihak. Koda wasa bai tab'a gayawa Yaranshi shi Prince ne shi suma suna da alaka da Kingdom din Baihak, sai zuwan Queen Hamidah har da nuna musu hoton Kingdom din, Sainah da halinta daya da Ubanta bata wani damu ba kamar yadda Sanah tana ganin Kingdom din ta shiga sake silly question. Murmushi Dowager tayi lokacin da ta ga Sainah ta fita tana murna Papa ya dawo. Tun a bakin kofar gidan ya ga fadawar masarautar, shiga cikin gidan yayi da sassarfa. Queen Hamidah ya gani a falonshi tana dauke da Nuriyya. Kallon juna suka yi, Maina da ta sani ba shi ba ne a gabanta. "Our future King Muhammad Maina Barka da hanya!" Cikin izza da isa ya taka gabanta ya amshi yarshi a hannunta. Ya wuce da ita tare da saka yan uwanta a gaba zuwa wurin Uwarsu. "Idan ba ni na kawo miki mutane ba, kada ki kara barin kowa ya tab'a min Yarana!" Sannan ya fito zuwa falon, Queen Hamidah tana jin shi. "Ki saka kai ki fita tun ban kira miki yan sanda su shiga tsakaninmu ba." Zama tayi a restchair tana me jingina shi ya fara gaba da baya da ita. "idan ban fita ba fa?" Kallon cikin idanunta yayi ya ce mata. "Zan fitar dake na watsar a waje." Yadda yayi maganar sarai zai aikata, haka yasa ta mike babu musu, ta fita har ta isa bakin kofar ta ce mishi. "Ina ga baka damu da kasan yadda mahaifiyarka take ciki ba ko? Ka kira ka ji ya jikin nata yake...... Share please and thank #exlover #friendship #LAtriangle #father #gurlfriend #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _Ohni jikar Amadun legas kiri-kiri Uwar Buba ta shiga ta fita ta raba mu da Hamidah ai shikenan._ https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s *MASU NIMA DAGA FARKO DON ALLAH GA LINK NAN SU SHIGA ZASU SAMU* _______________8 *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*