Sashe 58
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani Idanunshi ya hango mishi. Gida ya kaisu sannan ya wuce wurin aiki da ya kasa katabus, sai shan tea da lemon tsami yake, a hankali can ya kira Ammar suka shiga hira sai yake jin nauyin mishi maganar abin da yaje faruwa, "Ina Aliyyah?" "Tana garinsu?" "Me ya faru kuma?" Tabe baki yayi ya gaya mishi abin da ta je yi, "yaushe zata dawo?" "Hmm sai na ganta don tace wata sati!" Shiru Amma yayi kafin ya ce mishi. "Maina kana bukatar mace a gefen yanzu haka?" Shigowar wata abokiyar aikinshi office din tayi yarinyar tana son alaka da Maina, amma yaki bata fuska, a yau da yaje jin wani irin yanayi sai yaga gidiga gidigan boons dinta da suke son fasa rigarta kamar zasu fito. Dauke kai yayi baya son ganinta. "Get out!" Ya fa a mata da karfi, da sauri ta juya tana jin haushi. "Lafiya Maina!" "Babu!" "Kayi hakuri please Aliyyah bata kyauta ba, amma zan mata magana!" "No kada ka mata magana ai bata yi kome ba." Daga haka suka bar maganar suka shiga wani maganar na daban, kafin suka sallama. Sai wurin karfe biyu na bar bankin. Koda ya iso gida bai ga kowa ba, "Ina yaran nan!" "Suna can pool suna wanka da bakuwarsu." "Har da Nuri?" Ya fa a da sauri. Gyada mishi kai tayi, da sauri ya nufi wurin dake ba a waje bane, irin wanda ake yi a cikin gidan ne asalin wurin da dumi, sannan ruwan babu sanyi da dumi sosai. Yana tura kofa idanun shi ya sauka akan Layla da ta tuke gashin kanta a tsakiyar kai. Sanye take da wani dark blue dress na wanka, rigar roba ce ta kame mata jiki, Sainah tana musu video tana goye da Nuri darling da take ta ihu da farinciki. "Papa!" Juyawa Layla tayi ta yi maza ta ciro Nuri daga ruwan ta ajiye ta sama,ita kuma taki fitowa. Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce musu. "Kun ci abinci!" "A'a Nuri ce ta saka Sisi lallai ta kawo ta tayi wanka da wasa da ruwa!" Sainah ta fada tana daurawa Nuri din towel, sannan ta mikawa Layla da ta fito, itama yadda kasan yar tsana barber haka ta fito, ta amsa tana me daurawa a kugunta. Sannan ta nufi Nuri ta shiga goge mata jiki ta dauki mai da hand dry tana busar mata da gashi, har lokacin yana tsaye kamar an shuka shi, mamakin yarinyar yake yadda take mantawa da kowa idan tana tare da Yaranshi. "Next week Mamanku zata dawo, Ina ga Layla ta zauna kafin ta dawo" da gudu Sainah ta rungume shi, "thank you Papa!" "Hmm muna da test this week." Layla ta fa a a hankali tana me kallonshi a fakaice. "Zan kai ki school din!" Allah ya gani bai san me yake fisgar shi da ita ba, bai san me yake ji ba, sai dai akwai wani abin da yake ji aduk lokacin da haka ya kasance, tun barinta Scotland ya fara jin haka, haka kawai baya son rabuwa da ita ko ya ga bata kusa a shi, sai ya ga kamar baya da wani cikakken nutsuwa kwaila ce fa. Haka ya bar su, anan ita kan tsoron kada Aliyyah tazo ta same ta take ji don ta tsorata da marin da tayi mata, daki ya shiga ya sauyq kaya, har lokacin yana jin shi wani iri na daban, sai da ya sakarwa kanshi ruwa yayi wanka sannan da ruwan sanyi kafin ya ji dama-dama. - kurawa Ummimi idanu Malik yayi a yanzu yasan bata ta kanshi sannan bata damu da shi ba, ajiyar zuciya yayi tare da cewa. "Yarinyar can Suhana na kamata tana saka min guba, an rufe ta." "Allah ya sawwaka!" Ta fada tana hada kayanta. "Wai ina zaki ne?" "Washington DC!" Ta fada kai tsaye. "Wurin waye?" Juyawa tayi fuska a hade ta ce mishi. "Amma kasan dai ina da d'a a can." "Tow madalla, amma ba da yawuna ba, idan kuma zaki je ki zo min da Yarinyar nan ce maza ba zan hana ki ba!" Cike da takaici ta ce mishi. "Malik baka girma ne? Har mata nawa zaka kwanta da su? Yanzu itama Suhana mikata zaka kayi ga tsafinku?" "Ni ne matsafi?" "Meye maraban dambe da fada? Kai ba matsafi ba ne meye alakarka da tsafi? Malik kana da lokaci ka tuba ka bi Allah, koda yake Allah baya yafewa wanda ya hada shi da wani abokin tarayya!" "Idan Allah bai saka ni wuta ba, me zai hana ki saka ni, kuma na amince ki tafi ki zo min da Yarinyar ni zan reneta da hannuna." ",Allah ya baka lafiya!" Ta fada tana me daukar wayarta ta kira Saraki, can sai ga shi nan, ya gaida Malik sannan ya dauke kayanta suka fita, a wurin motar suka sami Khalifa da Khalil, "Granny ya kike?" "Lafiya lau, shine baku shiga ba." "Abba ya ce mu jira shi!" Shafa kansu tayi ya shiga a tare suka bar garin, domin har da Uwarsu da shi kansu Salahudeen zai je ya ga inda Maina yake. - Maina ya kira Aliyyah ya gaya mata su Ummimi gasu nan zuwa, amma ta ce ita gaskiya sai wannan kwanakin ya cika zata dawo, a ranar da su Ummimi zasu zo ya maida Layla makaranta da kaya niki-niki, su Radiyyah da Deenah sai tsiya suke mata, ita kuwa murmushi take, kwananta biyu da dawowa Ya kawo su Ummimi suka ganta, wani irin kyauta da tsaraba me masifar tadda hankali Ummimi ta kawo mata, babu abinda babu har da cincin. Kayan cimma kala-kala. "Na gode sosai, da kula min da jikokina da kike yi, na gode sosai da sadaukar da lokacinki da lafiyarki, na gode da alkhairinki. Kiyi hakuri kiyi hakuri idan mun sab'a miki don Allah kiyi hakuri idan Aliyyah ta miki ba daidai ba ki yafe mata, Papanku ya gaya min dalilin da ya dawo dake nan kenan, kiyi hakuri kowacce rayuwa akwai jarabawa, idan kika yi hakuri zai wuce.." haka Ummimi tayi ta mata nasiha kafin ta bar makarantar yana kallon yadda take kuka, sai da ya kai Ummimi sannan ya kuma dawowa makarantar kamar ya sani tana inda ya barta...... Me no go eating amanar Aliyyah. Karuwa kawai kada kayiwa yar mutane fyade don naga dan iska ne kai Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take chat me 08130269641 [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _______________32 Zama yayi a gefenta yana kallon sakon da Ummimi ta bata, har lokacin kuka take da dukkan zuciyarta. "Wani abu ta gaya miki?" Girgiza kai tayi,kanta kasa taba wasa da farcenta. "Tow gaya min me aka miki?" "Babu kome!" Sake kallonta yayi na few seconds kafin ya ce mata da"ok zan koma!" Ya mike zao tafi ta ce mishi. "Ina Nuri?" Jim yayi mata kafin ya ce mata, "tana nan lafiya!" Daga haka bai kuma zuwa ba, sai ya dauke kafarshi wani abu daya da ya fahimci yana bu atar mace a tare da shi, Layla kuwa matukar yana zuwa gareta tow zuwa zata fisge shi. Kwanakinsu Ummimi shida Aliyyah ta dawo,daga Ummimi har Maina babu wanda ya ce mata baki kyauta ba, zuba mata idanu suka yi su ga iya gudun ruwanta, sai kuma Allah ya taimaka koda ta dawo bata yarda wani abu mara dadi ya faru ba, sosai ta amshi aikinta kuma a wannan bangaren da ta dawo Maina ya samu sau in zaburar da naman wandonshi yake yi. Ana haka Auta yazo a bakin Sainah ya e jin labarin Inda Layla take, don haka wannan karon bai wasa da damarshi ba, ya fara kai mata ziyara tare da alkhairi dayawa, a wannan karon Deenah kiri-kiri ta ce mata. "Shi kuma wannan fa?" Shiru tayi kafin ta ce mata. "Shine autansu Papa Uncle Auta!" "Yana sonki ne fa!" Murmushi tayi tana fa in. "Eh na sani!" "Tow amma gaskiya wancan guy din yafi shi iya love." "Wa fa?" Murmushi Layla tayi tana fa in. "Babu soyayya a tsakakina da Papa, Matarshi yar bala'i ce, idan tasan mijinta yana sona cinye ni danye zata yi balle ma babu abin da zai saka su yantattu su ce zasu so baiwa akwai tazara tsakanin wannan abin." "Ko jikina kunnuwa ne ba zan yarda ba." "Ke dai da son magana kike, meye laifin wannan gayen?" Inji Radiyyah Aswad, "Ba zaki gane ba ne, shi fa wancan yafi wannan iya action, wannan kuma sam bai yi kama da wanda zai iya ririta mace a kan so ba, ni haushi ma ya ba ni sai wani washe ha ora yake shi gashi nan Prince Auta!" "Deenah me ya yi zafi da kike kwashe Prince Auta albarka" "ina bayan Papi ne ingaya miki!" Daga haka bata kuma magana ba, murmushi Layla tayi ina ita ina Maina sannan maganar gaskiya Maina ai ya mata tsufa. Kamar yadda Maina ya dauke kafarshi haka Auta ya saka afarsa, babu kama hannun yaro tun Layla tana nokewa har saki jiki, a lokacin da suka samu hutu, ko kwana bata yi ba Maina da kanshi ya saka aka wuce da ita Egypt wurin Bahi, Ummimi kuwa ba karamin shan matsin lamba take a wurin Malik ba, kai karewa ya ce maza ya bata kwana uku ta dawo dama tuni Saraki da iyalinsa sun koma, yadda Malik ya tubure abin ba karamin dariya yake bawa Ummimi ba, don haka ta koma kamar yadda ya ce shi a tunaninshi zata dawo mishi da Layla ne sai ya ganta rabbana atina fidduniya hasanata, ai bai san lokacin da ya tadda da bala'i da masifa ba, ita kuwa ta ce mishi. "Kasan yanzu ba da ba ne, wallahi kace zaka min tozarci zan bar maka masarautarku ba zan iya daukar jidalinka ba, ban shirya tashin hankali ba a rayuwata bana son jaraba." Jin yadda ta amsa mishi yasa shi mamaki domin bai zaci haka daga gare ta ba, tana zaune a dakinta da Yaronta Jawad wanda ta ce ba a iya kula da shi ba. Ta kunna data tare da shiga IG, hoton da Jasy ta tura ne ya bata mamaki hoton Maina da Aliyyah ta gani, tare da wasu kalamai