Sashe 53
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sadaukar don Maina yayi farinciki?" "Zan barka kayi tunani dakyau amma ka sani lokaci yayi da za a warware kome a bar kowa ya shaki iskar yanci.. -acikin farinciki da nutsuwa Aliyyah tayi ta gabatar da abin da Maina abincin da zai ci, ka an ya tsakura tea kawai ya sha, yana lumshe idanunshi. "Ka gaji ko?" "jinjina mata kai yayi, ta kwashe kome ta fita da shi sannan ta dawo tana mishi hira akan ciwon Nur in, bude idanu yayi kafin ya ce mata. "na gaji gobe mun yi magana!" Dakinshi ya nufa, Layla kuwa tunda ya ga Nuri darling ta nime gajiyar hanya ta rasa,hira suke har dare yayi suka kwanta, da sasafe sai ga Bahira ta shigo gidan don dai bata san Layla ta dawo ba, tun tafiyarta suke shuka rashin mutunci son ransu shigowar da zata yi suka yi ido hudu da Layla fitsari ne ya kwace mata....... [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu *Tun farko nace ku shiga Link amma kuka ki sai daga baya kuma kuna niman inda kuka yi missing, har ga Allah akwai takurawa ni* Don Allah a bar cire min link din channel wallahi ana damu na daga farko channel din yana taimaka min wurin bawa mutane su sami daga inda suke bukata. _______________28 Tab'e baki Sainah tayi tana shirya kayan makarantar a jakanta. "Fitsari kike yi a tsaye?" Nuri darling ta fa a tana nuna mata inda ta b'ata da fitsari shaaaa, "A'a ranki ya dade, wanke wurin zan yi." Cikin harara da gajiya da abin da sukewa Mamansu Sainah ta ce mata. "Yau ma wani kalar iskancin kika zo da shi? Dadin abin Papa ya dawo!" "Ai ban sani ba ne, amma da na sani ai ba zan zo ba, Allah ta huci zuciyarku!" Ya fita da sauri. "Tow waye zai gyara wurin?" Da sauri ta dawo ta shiga gyara wurin tas, sannan ta fita jikinta rawa yake ta isa parlour Ayrah da take baje kamar asara a gidan biki. "Sun dawo a tare?" Gaban Ayrah ce ya fadi ta zaro idanu waje ta ce mata. "Su waye?" "Magajin Baihak da Aljanar Yarinyar nan!" Wani irin b'acin rai da bakinciki ha e da takaici suka sakata fara jijjiga, lokaci guda haihuwa ya zo mata, amma saboda da haihuwar babu shiri, da gudu Bahira ta fita tana niman agaji. Lokacin Maina da Yara sun fito zasu tafi makaranta, kallon Sainah yayi ya ce. "Ki taso uncle inki su tafi asibiti." Da sauri ta wuce zuwa kofar shi da yake dan baya kadan, wucewa mota yayi Layla tana biye da shi. Sai da ya bude ta shiga ta zauna a gefen da ba kusa da kujeranshi. Har Sainah ta dawo tare da Auta. Ya iso wurin motar yana fa in. "Gaskiya Bro na gaji, tunda ka bar garin nan muke fama da ita, tana haihuwa su tafi wurin Malik domin wallahi mun gaji ranar sai da.." "ka kaisu nace." Ya fa a yana tadda motar, cikin takaici Auta shima ya share ya ce ta mutu ma, sai da yaji Muryan Bahira yasa shi kiran motar asibiti, aka zo aka tafi da ita. Daga ita sai Bahira babu wanda ya taka asibitin. Lokacin da Maina ya kawo su makarantar Sainah ta fita da gudu, kin bu e kofarta yayi ya mika mata jakar takarda da yake, amsa tayi cikin sanyi jiki. "Ki kula!" Ya fa a mata, amsa tayi ta fita da sauri, ta jikin motar ta wuce tana saka abun a cikin jakarta tana kallon gabanta, "Layla!" Inji Deviya Vasidram, itama da gudu ta nufeta suka rungume juna suna ihu, Sainah ta rufa musu ta ukunsu jan motarshi yayi ya bar makarantar, tunda suka shiga aji suke hira bayan gama darasi suka fito break, nan dai kawayen Sanah suka yi ta takalar Layla da rigima, amma bata kula su ba, yau ma har aka tashi suka fito wajen Makarantar babu Maina babu Auta. "Didin Nuri ko zamu shiga Bus ne?" D'ago kai tayi zata yi magana ta hango Motar Maina tana zuwa ta sunkuyar da kai tana fa in. "Ga yallabai nan!" Ta fada tana ara rike Jakar Sainah da ta amsa sun kafin su fito, sai da yayi parking suka ga Auta ne ya fito, yana isowa ya amshi jakar yana jan kumatun Sainah. "Wato matar tawa kike bawa wahala?" "Uncle Auta wannan dai cin zali ne, kuma zan gayawa Papana!" Ta fa a tana dariya, murmushi Layla tayi tare da nufar bayan motar ta zauna Sainah zata shiga gaba ya ce mata. "Waye sa'anki oya go back layla dawo nan." Dariya ta saka tana fa in. "Uncle Auta sai na gayawa Papana.!" Ta fa a tana dariya, haka Laylaeta shiga gaba, wato kafin su isa gidan sai da suka girgiza mishi aljuhunsa, don ma Maina yayi ta kiranshi, suna isa gida suka samu ashe yana nan a gidan jiranshi yake zai koma office, ita kan tana ganin shi da Aliyah sannunku da gida ta ce kawai ta wuce, inda ta samu Nuri tana barci, kayan jikinta ta sauya ta kwashe kayan Nuri ta wuce laundry room ta wanke sannan ta zo ta shanya. Sannan ta koma dakin ta samu Nuri darling ta farka abinci ta bata da magani, sai da ta gama da Nuri darling sannan ta fito ta amshi abincinta, kafin ta koma daki. A can dakin Aliyyah Sainah ce tsaye tana kuka domin tunda Sanah ta bar gidan Aliyyah take blaming Sainah da kin yar Uwarta da son Layla kawai bata nunawa ne don tana masifar shakkar Maina, "tow yanzu Mum ya zanyi? Ki mishi magana da bakinki mana, tunda ni." "Zaki min shiru ne ko sai na taka ki sakarya kuma ki gaya mishi ya dawo min da Sanah!" Fita tayi tana har akinsu ta shigo ta samu Layla na cin abinci, bata ga dogon sauyi a wurin Aliyyah ba, amma kuma tana ankare da yadda take hantaar Sainah. "Biyu me aka miki?" Cikin kuka take gayawa Layla abin da ya faru sai ta bawa Layla tausayi. "Kina son Sanah ta dawo ne?" "Eh mana tunda har yanzu Mum haushina take ji, ke da bakya nan haka wancan matar zata yi ta mari na ba zata yi magana ba, idan na mata magana zata ce ina ruwanta." Kamar daga sama ta ce mata. "Eh ina ruwana kina gayawa kanwar Ubanki ne ta dake ni? Ko kina gaya mata ne don ta shige min kamar yadda ra shige jikinku? Ke Layla kada ki ga na kyale ki, ki dauka wata tsiya ce ke, har kina tunanin shiga rayuwar Yarana zan watsa ki waje na rantse da Allah maza ku tashi ku wuce daki!" "Ni ba zan tafi ba wurin Didina zan zaunar!" Finciko Nurin tayi da karfi. "Kiyi hakuri ki barta zata yi kuka!" Dama tana cike da Layla musamman yadda Ayrah take jefa mata magana, idan tayi kishi da ita ba, zata yi kishi da baiwar da aka kawo mata, tunda alama ya nuna ita ba zata haifi d'a namiji ba, baiwar da aka kawo musu ita ce zata haifa mishi abin da yake so, wannan Maganar ya zauna a ran Aliyyah musamman daren jiya da ta ga fitar Maina yazo har dakin Yaran yana me kallonsu, lullubin Layla ya janye ya tsaya gyara mata, daidai lokacin ita kuma ta shigo dakin ganin bai dawo ba, amma da yake namijin duniya ne sai ya waske kamar bai yi kome ba, sannan ko yau kafin su tafi makaranta tana kitchen tana kallon yadda ya fito da wani jaka a dakin sai bin Layla yake da idanun, amma sai ka nutsu zaka fahimci yana kallon Layla, domin ya iya takun shi ko da ita ne ba zai tab'a tsayawa yana kare mata kallo haka ba, amma ji yadda yake kallon yar cikinshi wannan abin ya mata ciwo. Marin Layla tayi da bayan hannu sai a gefen idanunta. "Mum!" Duk suka hada baki daga Nur har Sainah. "Mum me tayi miki?" Wata razananiyar tsawa ta buga musu suka dunkule a jikin Layla suna masu fashewa da kuka, ai kuwa ranta ya ara b'aci ta rufe layla da duka. Ihun da Yaran suke yasa Auta zuwa cikin gidan ya samu Aliyyah tana marin Layla kau-kau. "Ikon Allah me ta miki?" Ya cire hannunta, "Har wannan yarinyar ya ita ta saka min Yara tana tambayarsu akan me nayi musu? Wallahi sai kin bar gidan nan!" Ta shiga watsar da kayan Layla duk yadda yaso kashe rigima dole ya kira Maina Layla sai kuka take, musamman garin dukanta Nuri ta zo ta rungumeta, Uwar taji haushi ta ture yarinyar sai da roban numfashinta ya fita, cikin kuka take fa in. "Nur zaki duba, ki daina fa a ki duba Nur!" Amma.haka bai hana Aliyyah marinta, dakyar Auta ya fitar da ita waje, fuskarta tayi jajjur. Kiran Maina yayi ya gaya mishi, bai zo ba domin uzurin gabanshi ya kasa tsallekewa amma tabbas zuciyarshi ta kagu da yazo gani yake kamar kafin ya iso aljanarta ta bayyana, a nan kuwa kukan Nuri da numfashinta yasa Layla nufar cikin gidan, ai kuwa Hilda ce ta Bayyana a jikinta, tana shiga dakin ta shake wuyarta Aliyyah. wani juyar da wuya tayi tana fa in. "Ke mahaukaciya ina ce? Taya zaki nime kashe yarinyar da babu ruwanta!" Ta wurga da ita tare da durkusawa gaban Nur, tana kallonta. A hankali ta shafa kirjinta daga Sainah har Aliyyah a tsorace suke domin yadda kome na Layla ya koma light green. Juyawa tayi a fusace kamar wata kwaduwa tayi tsalle a gaban Aliyyah da ta gama razana. "ki gode tana son Yarinyarki da yau sai na shanye kafarki don haushinki nake ji." Sannan ta wuce wurin Nuri darling ta d'auketa tare da sakata a bayanta ta kamkameta, sannan ta haura jikin bango tana me lullube yarinyar da gashin kanta. Lokacin da Maina da Auta suka shigo wani irin shock auta ya shiga bai tab'a ganin bala'i da rai irin wannan ba. "ku fita!" Ya fa a yana kallon Layla datake sama a makale da Nuri darling, ranshi ya b'aci amma ganin hilda yafi fusata shi sama da abin da Aliyah tayi, "sauko min Y'ata?" Ya