← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 115

Sashe 42

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

take yi, "Ai yanzu na gano dalilin tambayar Nuri darling ashe tinkiya uwar tambele, ce a gidan don Allah dubi mutum kamar muciya da zani!" " Bani va ce, wannan ita ce kika gayawa magana." " Ke dai sakarya ce ban da cikin jikinki sai mun miki shegen duka mahaukaciya kawai dalla fita mana a gida." "Zan fita gara ni Ubanki na aura, ko nace Kwarkwaran shi, ke kuma?" Wannan maganar ba iya Bahi ba, hatta Layla da ta fito ajiye kofin da Nuri darling ta sha kunun ya mata zafi, ji al awari tayi koda zata cutar da ahalin Malik ba zata tab'a cutar da yaran Ummimi ba, su kansu ba a kyale su ba, don haka ta shige tana fa i a ranta. "Bahiyyah kukanki ya kare zaki yi aure nan kusa mijin da zai so ki kamar rayuwarsa.* Lokacin da Bahiyyah ta dawo dakin, kuka tayi ta yi, a haka tayi ta shafa bayanta, har ta samo sihirin da aka saka mata. Tun daga ranar tayi ta aukar kasadar karya shi, dakyar ta karya bayan tasha bakar azabar da sai da tayi zazza i a wunin ranar, ita kanta Bahiyyah kwana tayi tana amai da gudawa, bayan kamar kwana biyu duk suka ji sauki. Duk da bata cika amfani da tasirinta ba, amma haka kawai ta shafa abin wuyarta, haske ne ya fito daga cikin abin wuyar tana mamaki. "Nice Kalya me kike so?" Hasken ta tambaye ta, "Bahiyyah nake son ta hadu da wanda zai kaunace ta daga kanshi ba zan kuma niman abu ba!" Murmushi hasken tayi ta ce mata. "Kin kyauta da baki yi tunanin cutar dasu ba, babu ruwansu, kin yi qbin da ya dace amma ki sani musulmai ne idan suka san da haka ba zasu amince ba, ba zamu iya hada addaranta da kowa ba, idan kuka yi hakuri nan kusa ka an ka an fa kamar fita daga gidan nan yafi shi wuya ga mijinta yana shirin zuwa gareta, amma karya tsafin yayi amfani don ba don haka ba ko sun hadu ba zasu jitu ba. Zaki yi albarka amma ba zaki kasance me tsawon zamani ba. Ban sani ba ko addara tana iya sauya amma ina tausaya miki ina tausayawa rayuwarku abin a tayaki kuka ne." Daga haka ta b'ace ta koma cikin abin wuyar ita Layla bata fahimci haka ba, don ita damuwarta Bahiyyah tayi aure ta nunawa Mutane lokacinta yayi itama ta huta da gorin aure da ake mata, koda ta koma dakin zama tayi can gefe tana jin kukan Bahiyyah, turo kofar dakin aka yi Prince Auta ne, d'ago kai tayi tana kallonshi ya sakar mata murmushi, sunkuyar da kai tayi tana wasa da bazar rigar uniform dnta. "Twins kuka kike?" Ya tambaye ta, share hawayenta tayi tana fa in. "Haisam farinciki zan yi don an min Gori? Ni na isa na bawa kaina miji ba tare da lokacina ya..." "Ya isa ina ga wannan ba wani abun tashin hankali ba ne, kina kuka a gaban Baby zata miki dariya" ya fa a tare da d'agewa Layla gira, murmusa mishi tayi ya dan rungume Bahi yana buga bayanta. "Kiyi hakuri rayuwar duniyar nan bata da yawa kome kayi hakuri zai wuce. " Haka yayi ta bata hakuri, har tayi shiru. Sannan ta fita can sai ga Nuri darling da wani jaka ta mikawa Layla. "Inji Uncle Auta!" Zuba mata idanu tayi kafin ta ce mata. "Ba Aunty Bahi ya ce ba?" Girgiza kai tayi ta ce mata. "Ya ce na kawowa didina ne!" Ta fa a tana komawa gefen Layla ta kwanta a jikinta. "Aunty Bahi!" "Ke bana son gulma, bude mu gani!" Bude jakar tayi sai ga chocolate da sauran dangin zak'i. "Yarinya kin zama surukata! Kema mu yi miki aure irin na yan garinku sannan Allah ya baku yarinya irinki me kyau!" Da sauri ta zubar da kayan ta fice da gudu, ai kuwa Bahi ta fashe da dariya, garin gudu da kunya sabo da ta rufe fuskarta da hannu, shi kuma Maina ya shigo gidan dauke da cefane. Bata san yana shigowa ba, kawai ta bangaje shi kayan ya zube baki aya ita kanta zamewa tayi zata fadi ta fa a can jikinshi. Wannan abin ta faru akan idanun Bahiran komawa tayi gefe tana daukar rahoto, zare idanu Layla tayi tare da janye jikinta da sauri tana fa in. "Na shiga uku, na lalace, mutuwa shi yafi dacewa da ni, ranka ya dade." Rab'a gefenta yayi ta kwashe kayanshi ya barta nan, ina zai iya haukarta, shi zafin kanshi yafi karfin ya tsaya jiran surutunta ba, yayi gaba abinshi yana kaiwa kitchen ya ajiye kayan sannan ya bar wurin, har zuwa lokacin tana nan idanunta a rufe, tab'e baki yayi yana mamakin yadda har yau muguzancin nan bai fita a jikin mutane ba, jin babu motsin kowa ta bu e ido aya kafin ta bude idanun baki ayan. "Au ashe ni daya nake ta surutu, humm." Magana take son tayi amma ta ja bakinta shiru. --A Baihak kuwa jikin Queen Hamidah yayi zafi, amma kuma yadda Falwa da Tirsila suka tsaya a kanta, wani zuwan da Sanaya da yake sun zo tare da Tirsila. Cike da mamaki tayi shiru tana son magana, a hankali ta nufi Hamidah, ta dauki wani farin kyale ta mika mata. "ki face hancinki!"............ (BARKA DA JUMA'ATUL MUFIDA) [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu *MASU BU ATA DAGA FARKO DON ALLAH SU SHIGA LINK ABUBUWA SUNA MIN YAWA GA CIWON IDO GASKIYA BA ZAN IYA BADAWA DAGA FARKO BA TA PRIVET KO GROUP LINK CHANNEL GASHI NAN IDAN KA SHIGA ZAKA SAMU DAGA FARKO PLEASE joining Last Empress https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s _________________ *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*
Chapter 42 · 0% Book details