← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 115

Sashe 63

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya fa a yana me dauke kayan abincin zuwa waje. Ya wanke sannaj ya dawo dakin, ya samu har tayi barci gyara mata kwanciyarta yayi, yana zaune a bakin gadon. Har kusan karfe biyu saura sannan ya mike tare da kashe wutar dakin, ya matsa kanta ya tofa mata addu'a. Kafin ya bar dakin , sai da ya gyara gidan sannan ya juya ya fita. Ya rufe mata gidan domin yasan ba zata fita ba. Kuma yadda ta yi barcin nan babu abin da zai farka da ita zai nima mata abokiyar hira. Daga nan gida ya wuce, a parlourn shi ya samu Aliyyah Allah ya taimaka kayan da ya tafi da su, da shi ya dawo. Kallon agogon wayarshi yayi ya ganta zaune. "Babe baki yi barci ba ne?" "Eh ina jiranka ne!" "Ya kin duba Yaran kuwa?" "A'a kai nake jira!" Ta fada a gatse. "Allah ya huci zuciyarki!" Ya nufi hanyar dakin Yaran ya duba su, ya musu addu'a sannan ya dawo bangaren shi yayi kwanta, ya saka kayan barci ya zo gadon ya zauna a hankali yake duba wayarshi tare da duba agogon. Sannan kwanta "zo ki kwanta anan!" Ya nuna mata kamar zata ce mishi ita wacce ka je wurinta bata baka ba ne. Ai tasan duk lokacin da ya fadi haka yana bukatar wani abu ne, sai ta je ta kwanta a gefen shi. Daga nan hidimar ya sauya jidali iri da kala ya nuna mata a wannan daren, wannan kirban da yake mata yana kara saka mata jin zafin duk macen da zata rab'e Maina. Mutum lafiyayye irinshi ba zata yi wasarairai da shi ba. Bayan sun gama ya shiga ban daki tayi maza ta dauki wayarshi wato Senior Man yasan kan duniya ita kanta wayar babu password balle ta ce yana cin amanarta. Ta gama bincike tass bata ga sunan Mace kai hatta mazan babu wanda taga yana yawan waya da shi idan ta cire Ammar da Salahudeen sai Ummimi da Hajja wacce ta ga kiran wayarta ya kai talatin kuma a rana guda, bata san ya fito ba sai da ya ce mata. "Ki duba dakyau ai babu macen da ta dace da Muhammad Hatim kamar Gimbiya Aliyyah!" Ya fito daure da towel, ajiye wyaar tayi tana fa in. "No ina duba number Jasy ne, ko na kira ta." "Tow ki duba da kyau!" Ya wuce ya saka kayanshi. Ya kwnata abinshi. Yana mamakin yadda ya kamata tana bincike. Washi gari da safe ya duba Nur ya bata magani sannan ya shiryata suka fita, kai tsaye bai wuce da ita ko ina ba sai wurin Layla da ta farka tayi wanka, ya sameta a parlourn, ya shigo yana kallonta. "Nur" ta kira sunanta a hankali, "Didina!" Rungumarta juna suka yi yana kallon yadda take farinciki, musamman yadda ya take kome a sanyayye. "Good morning Yallab!" Watsa mata harara yayi, sannan ya wuce yana me duba maganin fa ta sha. "Ya jikinki?" "Da sauki!"ta shiga ha awa Nuri darling tea, shi kuma ya wuce kitchen din ya shiga. Ya ha a musu abincin rana. "Na fadawa Principle dinku baki da lafiya!" "Thank you!" Ta furta tana kallon kasa don har yanzu kunyar mata wanka da yayi, sai da ya gama sannan ya ajiye musu a micro, sannan ya bar gidan bayan ya tsare ta da idanu domin bawa Nur tap yayi ya wuce dakin sannan ya juya yana kallonta. Yadda ya kalleta yasa ta mikewa zuwa wurin shi ta tsaya a bakin kofar, ha e rai yayi ta shiga dakin. "Bakya bukatar wani abu?" Girgza kai tayi tana wasa da yatsunta. Dafe goshinta yayi yana fa in. "Jikin da sauki maybe gobe ki koma school zan 1zo na dauki Nur an jima ina babu matsala." Girgiza kai tayi tana fa in. "Babu kome." "Shi kenan!" Haka ya fita ya barsu a gidan a tare suka wuni. Yana office Aliyyah ta kira. Dauka yayi yana fa in. "Ina Nuri?" "Tana daycare!" "Hmmm!" Ta kashe wayar, tashi yayi ya nufi waje, shaf ya manta bai gaya mata ba, haka ya isa gidan suna cin abincin rana, har ta mata wanka ta gyara mata gashin kanta. "Papa!" Ta fada tare da nufar shi, d'aga ta yayi sama. "Kun gama zata tafi!" Tashi Layla tayi ta nufi dakin ya bita. Ita kuma ta je dauko mata kayanta ne da ta baza a dakin don daga ita sai vest da pant, da ta zo da shi sai kayan da ta baza mata a dakin. Juyawar da zatayi bata san yana bayanta ba, suka yi karo, hannunshi ya kai bayanta. "Sannu!" Kaukaucewa ta fara yi zata kwace jikinta. "Didi!" Da sauri tana fa in. "Na'am Darling!" Daukar Nur din tayi tana mika mata tap din, "rungumarsu yayi baki aya yana kallon yadda Layla take son barin jikinshi, kasan ya kai kunnenta. "Don let Nur!" Murmushi Layla tayi na karfin hali haka ya amshi Nur din hannunshi yana shafo yan kirjin da yaji tudunsu. Da sauri ta kalle shi, ya dauke kai kamar bashi ba, sai lokacin kunya ta kama ta. Haka suka fito ta shirya Nur suka mata sallama. "Zan tafi kina bukatar wani abu ne?" Girgiza kai tayi. "Ga key nan!" Ya mika mata, tana kawo hannunta ya janyota yana tsare ta da idanu. "Zan dawo an jima." "Gashi ban da abin da zan bata!" murmushi yayi ya ce mata, "me kike so a bata?" "Kome mai!" Shi kanshi bai san lokacin da yake wani abubuwan ba domin wani abu yake fisgar shi. A hanya ya saya mata abubuwan kamar yadda yasan Layla zata bukata, yasan akwai rikici a gaba domin yadda yake ganin Layla tana kin abin, yana isa gidan da sauri Aliyyah ta zo amsar su, kamshin turaren jiya, kura mishi idanu tayi. "Kamshin turaren wacece!" Kallon Nuriyya yayi da ta sauka a jikinshi. "Ban gane kamshin turaren wacece ba?" Ya tambayeta shima. "Papan twins jiya naji kamshin nan, yau ma na sake jin kamshin!" "Look hancinki ne yake janyo miki gaskiya domin daga nan day care na tafi na dauko yarinyar nan!" Sake baki tayi tana kallonshi, hawaye ne ya cika mata idanu. "Amma shi kenan." Ta wuce ta bar shi yana tsaye, tabbas shi yasan ya rungume Layla bai san lokacin da ya shafi turarnta ba, tabbas ya fahimci lallai akwai gurmi anan gaba, bin ta daki yayi yana shiga ya samu tana ta kuka. Domin bai san cewa Lamarin ya kai haka ba, rarrashinta karshe abin da ya kwaso can wurin Layla shi ya sauke akan Aliyyah domin wani irin abu yake ji yana..... [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _________________36 Ko da wasa Maina bai ba da kofar da Aliyyah zata zarge shi ba asalima sai ya kasance yana kyautatta mata sama da yadda bata zata ba, abin har ya sa tayi ta daurawa a internet musamman IG, tare da kalaman kauna da soyayyar mijinta, Ammar yana yawan gaya mishi ya duba handling dinta, ranar da ya fara dubawa ya mata reply da thank you my lovely wife like no other. Abin da ya janyo hankalin Ayrah kenan, don masifa ta nufi page din ta shiga rubutun hauka da rashin mutunci, _Har mu za a gayawa Fake love, matar da cusawa Hatim aka yi, waye bai sani ba_ Jasy kuwa ta rubuta a kasan posting din Ayrah. *Alhamdulillahi! Aliyyah Mrs Prince Maina Hatim tafi arfin zama concubines, sai dai next crown Princess wacce zata zama new Queen Dowager.* Wayyo Allah na, ji tayi kamar zata mutu bata san lokacin da ta kira Jasy saboda masifa tayi ta zaginta. Da ta gama Jasy ta ce mata. "Mahaukaciya ko a birnin mahaukata Maina ya haramta a gare ki Balle a birnin masu hankali, kwadayayya wacce kwadayinta bai amfane ta ba." Dariya Ayrah tayi tana fa in. "Sai na ture Aliyyah a gidan Maina matukar ina raye. Yar kawaliya!" "Tabbas idan har abin da ummina tayi shine kawalci Alhamdulillahi domin ta sanadinta an samu albarka dadin abin bata yi abin da zai saka ta danasanin ba, a banza a banza talaka ya girmi sarki sannu Kwarkwarah Malik you Are not wife zaki kare a concubine ne har abada d'anki kuwa sai da ya rako su Maina ba dai ya zaka sarki na ya kare a yarima shi kenan." Wayyo Allah kafin tayi magana Jasy ta datse kiran, sannan ta kira Aliyyah tayi shiru kafin ta ce mata. "Kada ki sake wani abu ya faru tsakaninki da Maina, kada ki bari wani ya san matsalarki da Maina, yau idan Maina yana kawo miki mata gida kiyi kamar baki gani ba, Ummimi mahaifiyar Maina tayi hakuri ta zauna ita bata samu kulawar da kika samu ba, Ummimi ta samu hutu ne ta silar Yaranta, kada ki sake Ayrah ta kara amfani dake wurin lalata alakarki da Mijinki, na gaya miki kada ki maida shi munafuki karfi da yaji!" Sai a lokacin ta tuna abin da ya faru ta gyara zama ta gayawa Jasy, wani irin tashin hankali Jasy ta shiga tana maimaita abin da taji. "Maybe abin da ya fa a gaskiya ne, sannan kada ki ce zaki bibiyi sawun shi don zaki ga tashin hankali, ki bar wannan al'amarin mu ga abin da hali zai yi." Haka tayi ta bata shawara ta kuma nuna mata ko mace yake nima tayiwa kanta adalci ta kyale shi tunda bai wulakantatta ba, sannan ta gaya mata harin Ayrah akanta don haka tayiwa kanta adalci ta zauna lafiya, ai dabi'arsu ce son mata fiye da daya. Da wannan Aliyyah ta dauki shawara musamman da taji za a kashe mata aure, sannan shima Maina ya yi baya da Layla don kawai makaranta ya maida ta, abin sai ya kasance babu kare bin damo, zaman lafiya a gidan Maina abin ba magana, haka yasa baki aya ya samar musu nutsu. Bahiyyah tazo kwananta biyar ta je ta ga Layla har su Aliyyah. Yadda Layla take takura yasa Maina komawa mota ya zauna yana kallon yadda take takure domin bata san zai zo ba, kuma yau riga da skirt ne a jikinta, skirt din iya gwiwa ne haka yasa baki aya tayi wani irin zama, ranshi yayi masifar b'aci,
Chapter 63 · 0% Book details