Sashe 73
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na rage shi da zai auri baiwarsa?" "Waye ya gaya miki kin rage shi da wani abu ne? Ki godewa Allah da tunaninshi aure ne idan kuma baiwa ya dauketa baki da katabus da Mijinki, ya kamata ki daure kamar yadda kike nunawa duniya kina happy marriage ya kamata ki daura hoton Layla sannan ki gayawa duniya kishiyarki ce, yadda idan labarin ta fito babu me kalubalantarki domin wallahi Ayrah tana shirine akanki!" "Don Allah Jasy ki tsaya a gefena yadda koda nayi kuskure zaki saka ni a hanya, don Allah kada ki sake cin amanata!" Murmushi Jasy tayi tana fa in. "Har abada babu wannan a tsakaninmu, yanzu me zaki yi?" "Ban sani ba Jasy!" "Ki shirya yar aramar liyyafa!" "Zan iya ko?" "I trust you zaki iya!" Haka yasa jikin Aliyya ya samu dan Kwari, bayan sun gama ta duba hoton Layla ta daura akan IG story inta, da manyan baki tayi amfani Allah ya sa an gama a sa'a Amaryan Muhammad Hatim kenan Layla Hatim! Tana send hawaye na zuba mata domin bata ta a kawowa Maina zai iya ajiye mace ba. -Dariya Ammar yake mishi yana kallonshi. "Kana nufin tsoron Aliyyah kake?" Girgza kai yayi yana shan ruwa da yake kofin. "Kunyarta nake ji!" Dariya Ammar yayi ya kara kallon Maina da yake cikin wayar dake video call suke. "Tow yau sai dai ka kwana a waje, ko ka koma wurin kwaila!" "Stop joking ka shigo Washington jibi!" "Kutumar Uba ni zaka wa kiran karen farauta?" "Mtsew!" Ya ja tsaki, daga haka ya kashe wayar, yasan zai zo dole ma ya zo, haka ya mike tare da nufar hanyar waje, a can gidan Layla ya nufa anan ya ga Layla da Sainah suna ta kiciniya a kitchen, Sanah tana zaune abinta. "Fafa Didi ta bani cake!" Kallon Layla yayi da kanta yake sunkuye. "Me kuke yi?" "Lady Ayrah ce ta ce mu yi mata abinci!" Inji Sainah, ranshi ne ya b'aci. "Papa ta mari Sisi kalli gefen fuskanta." Takawa yayi ya nufi kitchen din yana me d'ago fuskar Layla da yatsun Ayrah ya bayyana. "Me yasa baki ji da ita ba? Meye amfanin baiwar da Allah ya ba i?" "Ka haramta min amfani da shi, sannan ba ina ajiye da shi don kowa da kowa ba ne. Kuma ai kai kace kada na kara amfani da shi fa!" Hannunshi ya sa ya janyo ta tare da rungumeta. "Papa su Sainah!" Murmushi yayi ya ce mata. "Ki shirya muje can gidan!" "Babu matsala?" Ta tambaye shi. " A can zaki kwana!" Yadda yaga tsoro a idanunta yasa shi jan kumatunta. "Kada ki damu!" Sannan ya juya yana kallon kofar dakin da Ayrah take. " A hankali ya kalli Layla. "Ki dauke hankalinsu baki aya!" Kallon cikin idanunshi tayi a hankali ta janye tare da cewa. "Kana nufin!" "Yes do it!" "Zarbarara!" Ta furta a hankali take Yaran suka fara barci, "me kike so nayi mata!" Kifa kanta tayi a kirjinshi. "Kyale ta kawai ta ci darajar Ummimi!" "Me yasa?" "Saboda ba koyaushe ake maida kowa abokin gaba ba!" "Shi yasa nake sonki!" Murmushi tayi, a hankali ya janye ta daga jikinshi, ya nufi dakin da Ayrah take wato da ya shiga mata rashin mutunci tare da wulakanci, haka ya tattara kayanta ya watsa ta waje, "Maina ni ka wulakanta?" "Kada na kara ganinki a inuwar iyalina!" Ya rufe kofarsu, sai da Layla ta gama abinci suka d'aga yaran suka ci, sannan suka nufi gidan Aliyyah da take jiran zuwan su. Lokacin da suka iso ta kar e su kamar babu kome A ranta, tayi ta hidima da su daga shi munafikin har Layla kasa sake jiki suka yi kuma abin mamaki Aliyyah bata ce kome ba. Har suka watse daga table din ta nufi akinta. Tana kwance ya kira wayarta,nufar dakin tayi tana shiga ta same shi zaune! "Ina tea?" Kamar zata ce me yasa Layla bata bashi ba sai ta share ta juya zuwa kitchen ta hada mishi ta kai. Koda ta ajiye mishi jyyawa tayi zata futa ya ri e ta."ki kwana anan!" "Anya kuwa? Amarya fa?" "Ki kwana nace!" Ba musu ta kwanta tana nan tayi ta tuna yadda yayi ta rough sex da ita ashe a can yake kwaso jarabarshi yazo ya zuba mata bata san lokacin da hawayen bakin ciki yayi kwace mata ba, tana wurin har barci ya kwashe ta. Wurin karfe biyu na dare ta farka ganin baya dakin bai bata mamaki ba, amma ranta ya b'aci, lumo tayi shaidan na ta ingiza zuciyarta, haka yasa ta mike tare da fita daga dakin tana sand'a. Sai da ta fara leka dakin Bahiyyah wanda ya san Layla tana dakin, bata ga alamar yana dakin ba sannan ta leka dakin Yan matan anan ta ganshi yana gyara musu kwanciya tare da musu addu'a. Kunya ce ta kamata ganin yadda yake kallonta. Mikewa yayi ya gyara musu kwanciyarsu, suka fito."Kin tashi ne?" Sosa kai tayi tana fa in. "Na farka ne naji motsinka." "Muje mu kwanta!" Daki suka wuce, murmushi yai a ranshi wato ita tunaninta kada ya b'ata rawanshi da tsaye. Sai da yayi Sallah dare sannan ya kwanta tare da janyota. Duk da ranta baya so amma haka ta biye mishi aka ci Uwar sabada, dakyar ya kyale ta sai yanzu ta kara hango fitinarshi da ya karu sama da yadda ta sanshi a baya. Barci suka yi da asuba ya tashi sai da yayi wanka sannan ya yazo yayi sallah, da Gari ya waye a lokacin ta duba wayarta tayi ta ganin sakon fatan alkhairi da yadda mutane keta jinjina mata ana alfahari da ita, sai wurin sha daya na rana suka fita har da Yaran wurin spa and saloon, aka gyara musu jiki, ita Layla ta za i a yi mata lalle ja a hannu da kafa, don ta kula da suka zo yaga menu din zanen lalle haka yayi ta kallon yan siraran yatsunta. A nata hankalin yana son tayi amma yana tsoron kada Aliyyah tace ya mata iyayi! Haka aka gyara musu jiki har da lallen aka mata sai satar kallonta Aliyyah take tayi kyau kamar ba ita ba, sannan abin da ta kara fahimta Maina yana tab'a Layla domin kirjinta ba haka suke ba, yayi tudu ka an. Can ta tab'e tana fa in ko meye ruwanta oho. Haka suka dawo gidan, wurin yamma Aliyyah ta shigo dakin da take zaune ta ce mata. "Ina ga gobe zaki koma gidanki, Allah ya sanya alkhairi domin gaskiya ba zan iya zama dake a gida aya ba!" Kanta a sunkuye ta gyad'a ba tare da tace kome ba. Haka da Maina ya dawo ta ce mishi gobe ya tafi da Matarshi domin idan tana ganinta kishi zai kwashe ta tai ba dai-dai ba. Dake bai da gaskiya bai ce mata uffan ba. A daren ranar ya so ya mata bayani amma taki, sanin zasu ta bawa juna wahala yasa shi jan bakinshi yayi shiru. Next day da zai tafi aiki ya kaita gida ya zuba mata idanu yana kallon yatsun hannunta da take ta wasa da shi. "Yau ki shirya tarb'ana a ango!" D'ago kai tayi kamar zata fasa kuka ta ce mishi. "Papa ni fa." "Ke me?" "Ka kaini wurin Sultanah Dilshah Khatoon!" Ta fada tana kallon asa. "zan kai ki amma me zaki bani sai na kai ki" da murna ta kalle shi tana fa in. "Me kake so?" Hannunshi ya kai kirjinta yana mulmula lemon tsamin kirjinta. "Su zaki bani na ta sha" da gudu ta shige daki tana me jin kunya. Binta dakin yayi ya samu ta dunkule a gado ya haura gadon yana jan necktie dinsa su....(su Maina ba a rena d'aga buje dan taure kawai sai kace ba samu wurin Aliyyah) [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS _* Mai_Dambu ___________44 "Waye ya baki wannan kazamin labarin?" Yadda ta daka mata ta tsawa yasa Ayrah jin wani irin tsoro ya kamata ba dai hakarta ba zai cimma ruwa ba, muryanta narawa dake ta kware a munafunci ta fashe da kuka ta ce mata. "Mother taya zan samu labari a wani wuri na baki wallahi akan idanuna na ga kome matan Maina biyu ne." Wani irin ihu Queen Hamidah ta tsaya tare da fa in. karya me ni za a yiwa haka? Tow basu isa ba daga shi har iyayen shi. Fice min daga gaba;" ganin yadda hakarta ta cimma nasarar yasa ta mike tana share kwalla burinta ya cika kuma haka take so ta raba duk wacce zata shiga rayuwar Maina da jin dadi, ba iya ita ba hatta Aliyyah bata jin zata kyaleta haka domin ita tana da burin azabtar da zuciyarta. Haka ta bar Hamidah cikin tashin hankali da kaduwa kafin wani lokaci ta fita hayacinta domin bata tab'a kawowa ko a mafarki Maina zai yi aure ba tare da saninsu ba, don haka ta sa aka kira mata Ummimi. Yadda take yi tsare Ummimi da idanun yasa itama ta cire kunya ta shiga tambayarta. "Lafiya kuwa Mama?" "Muhammad yayi aure ne?" Kallon Queen Hamidah Ummimi tayi kafin ta ce mata Eh yayi aure wani abu ne? sake baki Queen Hamidah tayi jikinta har wani rawa yake tana kallon Ummimi. Khamilah kika ce min yayi aure? murmushi Ummimi tayi sannan ta mike tsaye tana fa in. Auren nan dai naga ba haramcin ba ne, shi fa bai da ra'ayin tara kwarakwarah yasa shi ajiye mata biyu kuma Alhamdulillahi tunda haka ya zab'a Ubangiji ya sanyawa rayuwarsu albarka. A zabure Queen Hamidah ta yo kan Ummimi. Da kin ne nutsu domin wannan karon don try mess wrong person Maina ba kanwa lasa ba ne, yana shirye tsaf ya baki mamaki. wannan kalaman ya bawa Queen Hamidah mamaki komawa tayi ta zauna sannan ta ce mata. Ki turo min Malik murmushi Ummimi tayi a karo na biyu ta ce mata. Gaskiya shine daidai da lissafinki." Daga haka tayi wucewarta ba tare da ta ce mata kome ba tow me zata ce mata? Ta ce mata tayi hakuri bayan tasan ba ji zata yi ba, ita yanzu akan Yaranta tsaf zata iya yin kome. Lokacin da Malik ya isa wurin Queen Hamidah ta gaya mishi kome tab'e baki yayi yana fa in. Hmm