Sashe 29
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
har bayan suna tana tare dasu, ance mai da wawa ne, Matar Ubaidu mai suna Amaal, ta dauki soyayyar duniya ya daura akan Layla, domin tsakaninta da Yaronta shan nono, bata san wankan shi ba, bata san kome akanshi ba, itama Layla duk fansarta akan Baihak yake, bata ta a kawowa a ranta zata cutar da mutanen da suka basu mafaka ba. -Baihak ya kuma dawowa sama da yadda ake can baya, sannan duk inda talakawa suke an bi an rushe, domin kuwa sun samu labarin cewa a kananun unguwanni akwai matsafa da bokaye haka yasa aka yi ta rushe su, cikin dare sai dai ka ga ana rusa maka gidanka akanka idan baka fita ba, anyi asarar dukiya da rayukan wadanda basu ji ba basu gani ba. A lokacin Maina yaji labarin amma babu yadda ya iya domin zuwa yanzu Queen Hamidah ta saka an cire mishi kaunar zuwa mahaifansa, sannan suka saka Ummimi a gaba da fitina ita da Malik,shi kanshi Salahudeen babu yadda ya iya kama ya mutu da takaicin Malik amma hak ya hakura ya zuba musu ido. Ummimi bata yi kome ba, amma baki aya sai gashi laifin Maina ya shafeta domin dan abin da bai taka kara ya karya ba, zai zama tashin hankali kuma a gaban kowa Malik baya shakkar mata rashin mutunci. After like wata bakwai. Da shida Haisam ne a tsaye labour room, zuwa yanzu bai fito ya bayyana abin yake d'anshi ba, amma har ga Allah yana fatan da Allah ya albarkace shi da da namiji, musamman yadda kowa ya gama saka rai a kan babyn, sannan a scanning din da aka yi gender din har yau namiji ne, sai gashi sun yi jugun jugun. Fitowar wata nurse a guje can ta shiga wani daki, suka fito da wata nurse kamar zasu tashi sama, suka koma ciki hankalinsu a tashe, yadda Maina ya gansu ya tabbatar babu lafiya, suna zaune a wurin nurse din da ta fito fuskarta dauke da murmushi, ta ce mishi. "Congratulations Mr Hatim matarka ta samu kanta lafiya, sai dai Babyn tana cikin wani yanayi." Cikin karfin hali Haisam ya ce mata. "Mace ta haifa kike nufi?" Wani irin kallo Maina ya mishi, take ya shiga nutsuwarsa. "Ina Babyn take?" "Yanzu zamu kaita dakin hutu!" Murmushi yayi sai da dimple point dinsa suka lutsa ya ce mata. "Zan iya ganinta?" "Eh sir!" Suka shiga dakin dake ita daya ce, tana kwance gajiye, murmushi yayi mata tare da mata alamar tayi kokari da babbar yatsar hannunshi. Dakin da ake gyara babyn suka nufa, shida nurse din. Lafiyayyar yarinyar gwanin ban sha'awa, suna shiga dakin ta sake atishawa amsar ta yayi, nurse din suna ta murna dama rashin kukanta da atishawa yasa suke ganin bata da lafiya, amsarta Maina yayi yana kallon kyautar da Allah ya bashi Yara mata hudu, a haihuwa uku ban da Allah waye zai baka irin wannan kyautar da kari, tasbihi ya shiga yi tare da kadaita Allah, yaso yayi sabo da yayi fatan ta haifi da namiji ya manta da cewa wanda ya bashi haka yake da niyyar bashi Yara mata, shi bai isa ya ja da ikon Allah ba. Mikata yayi bayan ya mata huduba da suna Banafsha, sannan ya fita zuwa wurin Uwar da take kuka. Kallon juna suka kayi ta ce mishi. "Na kasa baka da namiji?" "Dama ke kike badawa?" "But!" "Ki tuba zuwa ga Allah domin wanna abin da kike sabon Allah ne.!" Ganin yadda ya amshi yarinya yasata jin farin ciki a ranta, ko ba kome mijinta ya amshi Babyn. Haisam ya kira Ummimi ya gaya mata, kafin wani lokaci, har labarin ya bazu. Ummimi wucewa parlourn Malik tayi cikin tsananin tsoro, tana shiga aka ce ta jira Malik gana da bakowa,.sai da ya gama iskancinsa da yake kafin Lady Ayrah ta fito tana girgiza. Ummimi bata damu da ita ba, ta shiga cikin parlour a yadda ta ganshi ta dauke kanta, kafin ta tsaya tana jiran ya bata izinin zama. "Meke tafe dake?" "Dama xan gaya maka me matar Maina ta haihu!" Cikin tsannanin mamaki yake kallonta, "ban gane ba? Dama ciki ne da ita?" "Eh nima yanzu Haisam ya gaya min." Bai san lokacin da yayi kwallo da tiren gabanshi ba. "Ina nan da raina da lafiyata har Matar Maina tayi ciki ta haihu a ba gaya min ba? Wato an rena ni ko? Nace an rena ni ko? Ban isa a gaya min tana da ciki sai dai naji haihuwa! Tow daga yau kada na kara ganin kafarki a nan sai ranar da kuka mai dani mutum ke da Yaranki!" Abin sai ya bawa Ummimi mamaki domin bata ga wani aibu ba, tunda shi yayi niyyar boye abinsa a lokacin da suke bayyanawa ma ina b'arin cikin take da ta gaya masa ya ce idan ba zata iya haihuwar ba,ya je manyan masarautun da suke karkashin ikonshi ya zabo mata idan kuma bayi yake so as concubines tow ya zo ya zaba kuma kada ta kara gaya masa labarin matar Maina tayi b'ari, "Tuku na me ta haifa?" Cikin tsannanin kad'uwa da tsoron abin da zai aikata ta ce mishi. "Mace....... #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *Masu bukat a daga farko ga link nan ku shiga.* https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu Shi Maina baya dariya ne ________________12 *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*