Sashe 52
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shima ya fama mishi abin da yake mishi ciwo. "Me yasa ka fadi haka?" "Saboda a bawa Kowa damar yayi abin da yake so." Sai da Babanshi yayi nisa da nan ya ce mishi. "Ba soyayyar ba ce illa rikidewa da soyayyar zata yi ta koma kiyayya ita ce illa, ba hana kowa aka yi yayi soyayya ba, tasirin masarautar yana kan soyayyar ce, idan har an yi haka ne domin ceto rayuwarsu wasu ne fa akwai abin da xa ayi ? Tabbas anyi kuskure amma soyayyar ba zai yiwu ba." "Baba Maina!" A hankali Dattijon Wazir Abu Ammar ya mike tare da tab'a wani wuri, kundin littatafan da suke dakin karatun ne suka fara matsawa, a hankali zanen hoton wani Kyakyawar budurwa ya bayyana. A hankali ya kara tab'a wani wurin hoton wani Basarake ya bayyana. "Wannan shine King Salahudeen na farko!" "Wancan hoton fa?" "Sabrina kenan, Mata ce ga King Salahudeen, kuma yar Uwarshi ce ta wurin Mahaifiyarshi." A hankali ya taba wani abu sai ga zanen yan mata uku ya bayyana. "Hanna da Rihanna, Hilda!" "Baba me kake nufi?" "Masarautar nan ya samu kariya ne daga jinin wa annan Yan mata biyu, ita kuma Sabrina ta kubuta daga jinin wannan Budurwar!" Kasa fahimtar kome Ammar yayi ya ce mishi."zauna na gaya maka ka an daga cikin abin da ya faru wanda ban san sauran ba, nima kasancewar Mahaifiyata Babanta shine ma'ajin masarautar ya gadar mata da wannan zanen!" Kurawa Babanshi idanu yayi a hankali ya ciro wayar shi ya saka a record.. "Sabrina da Salahudeen sun yi aure kuma auren soyayya, wanda kowa yasan irin soyayyar da sukewa juna, sai dai bayan wani lokaci sai aka fahimci Sabrina ba zata tab'a haihuwar da namiji ba, duk da ta haifi Yara mata har uku, a lokacin an samu juyin juya an kifar da Gwamnatin muslunci a andulus da wasu wuraren, daga cikin wuraren da ake hari ka gaba ita ce Baihak saboda akwai maguzawa da suke kewaye a daular. A lokacin wasu daga cikin mutanen fada suna shirka a boye, haka yasa aka gayawa Salahudeen ya bi ra'ayin masu wancan shirkan koda zasu tsira da daular da mutanen cikinta. Yaso yaki amma wani abin mamaki sai aka turo mishi sakon matukar yana son d'a namiji tow ya saka ranshi a inuwa sai ya kauce hanya, abu biyu suka zo mishi a rai, daular shi me karfin tsiya da kuma burinshi na son da namiji haka zuciyarsa tayi galaba akanshi ya tafi har tsibirin da aka gaya mishi ya cire soyayyar Sabrina a ranshi da kome, zata haifi d'a namiji amma sai ya jira Yan mata uku, da zasu zo. Haka kuwa aka yi zuwan yan gudun hijira yasa aka bukaci su taimakawa Baihak, zuciyarsu aya wada ta turo su. Sai dai a hanyar su ta zuwa suka hadu da HILDA, wacce bata boye musu dalilinta na son tafiya dasu. Haka suka iso Baihak duk wani abin da ake bukata sun yi, sai dai Salahudeen ya kasa tsallake sharadin da aka gindaya mishi, ya fa a soyayyar Hanna yayinda Hilda tazo ne kawai don tana sonshi, boye soyayyar Hanna yayi ya bude soyayyar yaudara a kan Hilda a takaice Hilda itama wata Shaidaniyar bokayance, ita ta gaya mishi cewa duk wahalar da yake sha na son da namiji Sabrina ba zata tab'a haifa mishi amma ita tasan zata haifa mishi. Shima kuma dama bokanshi ya gaya masa Sabrina ba zata iya haifa mishi namiji ba, sai dai zai kasance da mata uku. Kuma dukkansu zai mu'amalance su. Haka kuwa ya faru domin kuwa tarkon soyayyarshi da Hanna bata boya ba, sai dai kuma an kama Hilda wacce tace ya kashe Yan matan nan domin sadaukar da jininsu shine zai kare masarautar, wani tudu wani gangare aka kama su baki aya. Al'amarin da yaja har aka basu zab'i, su biyu anan wacce za a kashe wacce da a bari. Kallon Rihanna Hanna tayi ta ce mishi. " Ka kashe ni kabar Rihanna!" Rihanna ta ce a'a ita a kashe a bar Hanna kafin ta rufe baki Hanna ta zaro wuka a kugunta ta caka mata a kahon zuciya. "Na jima ina jin haushinki, asalima na fadi haka ne don naji me zaki ce min, an haife mu cikin daya ba yana nufin addaran mu daya ba ce, ban ji a raina ina da burin zama a wancan kauye banza kauye ba. Don haka a sauka lafiya ni zan sauya addini ma daga yau." "Hanna kin cuci kanki, da addinin zaki yi ba matsala amma kuskuren shine jinina zai ta Bibiyar ahalinki, zasu biya abin da basu da hannu ciki, kuma na hango wacce zata rushe alkaryan da kike takama da ita "daga haka ya fadi a wurin, tsafin Hanna ya fita a jikin ta had'e da na Rihanna suka tashi sama, tunda Hilda ta ga haka ta fashe da dariya, kamata aka yi aka wuce da ita wani kurkuku aka ajiyeta, King Salahudeen yana zuwa duk dare inda take tare da mata alkawarin zai saka a saketa. Sai da aka shafe wata takwas lokacin da tsohon ciki yasan ba zata iya kome ba, sannan ta daura soyayyarta akan cikin jikinta, dare daya tana kwance aka zo.aka fita da ita zuwa wani sabon wurin, anan suka daureta tana ta basu hakuri su kyaleta zata bar Masarautar ma amma haka Salahudeen yaki, domin kuwa yasan zata dawo aukar fansa, tsafeta suka yi bayan haka suka farke cikinta suka cire dan aka yi abinda za ayi wannan ya bawa Hanna damar haifar dan cikinta wacce ta sauya zuwa Nabilah, wannan bakincikin da Hilda ta gani yasa ta ce musu. "Sai na kashe duk wanda yake da alaka da masarautar nan, sai na lalata kome na masarautar nan, zan saka kafa akan duk wata mace da ta fa a tarkon soyayyar masarautar nan, tana gama maganar nan aka nimeta aka rasa ashe ta koma can rijiyar da yake wajen masarautar ne ta zauna inda aka wurga mata gawan danta, bayan nan ta cigaba da Bibiyar ahalin masarautar domin ta kashe Sabrina ta kuma yi nasarar kashe Salahudeen amma har lokacin bata huce akan fansarta ba, Nabilah tayi kokarin kare danta da iya karfinta da dan sihirinta ta kuma.tsaya sai da ya zama sarki na masarautar. Zamani ya tafi an baya sun cigaba da abin aka fara, sai dai zuwan sarki Sharifudden ne ya ware ana zuba yan mata a rijiyar haka yasa aka samu zaman lafiya a cikin masarautar da gidan." Ya sauke Ajiyar zuciya. "Tow me yasa Malik yake kokarin raba Maina da duk abinda yake so?" Kallon Ammar yayi kafin ya ce mishi. "Ban gane ba?" Nan ya labarta mishi abin da ya faru, murmushi yayi yana fa in. "Kada ka ga laifinshi. Malik yana son Maina ta yadda kuma Maina ya tsani Malik, ba zaka gane dalilin da yasa haka yake faruwa ba amma nan gaba zaka gane!" "Baba ganar dani!" Dariya yayi yana fa in. "Ta Yaro kyau take bata karko. Zan maka bayanin idan na samu lokaci." Juyawa yayi ya fita daga dakin karatun, ya nuna Hilda ya ce. "Ke kinso ki ci amanarsu, bayan nan King Salahudeen ta fahimci haka shi ne ya ci amanarki, ke kuma kika ci amanar Yar uwarki wato ku dai mata akan abinda kuke muradi cin amana ba kome ba ne, yau babu ku amma kun bar baya da ura." Rufe wurin yayi ya fita a dakin,Abu Ammar kuwa fada ya wuce, ya samu Malik yana tsaye a inda Maina ya bashi. "Me yasa ka tsaya anan?" "Ban yarda yarinyar da take tare da Maina yar Muhammad Ashraf ce, akwai abin da na hango da idanuna." " Me ka hango?" Juyawa yayi yana kallon waziri hannunshi a goye a bayanshi. "Yarinyar tana dauke da jar zare, wanda zai iya zama ajalin Maina!" Shiru yayi kafin ya cigaba cewa. "Rayuwar Maina tana da muhimmanci!" "Amma ai naga ba a cikin masarautar nan aka haife shi ba." "Shi din jini na yake yawo a jikinshi, ba zan bari don soyayya na rasa shi bayan ina raye!" Shiru Abu Ammar yayi, a can kuwa cikin jirgin jikin Layla ba karamin ciwo yake ba, domin ji take kamar an mata kafirin duka, duk inda ta juya babu dadi haka ya saukar mata da zazza i, hawaye yayi ta zuba a idanunta shi bai ma san tana yi ba saboda ya tashi, duk da suna first class ne. Can ya dawo ya ga tana juya kanta. Tab'a goshinta yayi yana kallon yadda take juya kai. "Jikinki yana ciwo ne?" Gyada kai tayi. Kiran daya daga cikin masu kula da sha'anin fasinjoji yayi ya gaya mata, ko minti biyu ba ayi ba, ta kawo mata magani ta amsa ta sha, janyota yayi ya kwantar da kanta a cinyarsa, matar ta kawo bargo ta lullube ta da shi. Barci me nauyi yayi gaba da ita sai bayan awa biyu ta farka, babu zazzabin sai zufa da wata mahaukaciyar yunwa da take ji, a hankali ta tashi zaune tana kallon kasa, "kina jin yunwa ko?" Kamar ta nutse haka ta ji, yau ta kwanta akan kafar Papan Nuri darling. Bata iya bashi amsa ba, yayi magana aka kawo mata abinci. A hankali tayi ta kallon abincin tana juyawa da cokali kallo daya yayi mata ya fahimci abincin bai mata ba, can yayi kuma kira aka kawo mata tea da snacks, anan kan yaga yadda take ta juyar da kanta tana son ci amma tana jin kunya. Mikewa yayi ya fita tana ganin haka ta fara ci tana sha, yana iya hangota a inda yake tsaye, "silly girl!" Ya fa a yana kallon agogon hannunsa, tana gamawa sai juye juye take don ma wurin babu mutane sosai. Tana ajiye kofin yana fitowa a inda ya tsaya, wasu daga cikin mutane basu iya cin abinci idan wani na kusa da su. Don haka ya bata wuri. Koda suka isa Scotland Auta da Sainah suka zo daukarsu. "Wow Layla Oyoyo;" inji Auta yana dariya. - a can kuwa kallon Malik Abu Ammar yayi ya ce. "Ina ga lokaci yayi da zaka bar wannan camfe da al'adar sannan abar Maina ya samu abin yake so." Kallon Abu Ammar yayi ya ce mishi. "Halifa waye zan