Sashe 104
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi tana fa in, "Don soyayyarka da Annabi kada ka tako!" Ta fada jini na zuba daga hancinta da bakinta. "Layla!" Ji yayi an buga shi da bango, da gudu ta rungume iska suka hantsila can, ta kuma mikewa da gudu ta tare jikin wardrobe din. Iya abin da zai iya tunawa kenan daga nan bai kuma sanin abin da yake faruwa a dakin ba.. A zahirin gaskiya kuwa Ruhin Rihanna ne suke dambe da Layla sakamakon shigowar da Aliyyah tayi ta duba Layla din,, dake bata da hankali ta samu Layla tana barci shi ne ta je tashinta, kawai ruhin Rihanna ta sureta tana me bugata da kasa, ihunta ya farka da Layla. Ganin halin da Aliyyah take ciki, kawai ta fisge hannunta jikin sarkan wanda ya janyo mata targad'e a hannun baki aya. Da gudu ta iska gaban Aliyyah zata d'ago ta kawai Ruhin tayi kwallo da ita. Sai da ta bugu da bango ta sake mikewa dakyar ta nufi Aliyyah ta taimaka mata, ta mike riko gashin kan Layla Ruhin tayi sama da ita tana dariya, kafin ta sake ta. Ta fadi akan hannunta sai da yayi kara, cikin wahala da kuka ta cewa Aliyyah. "Tashi ki shiga wardrobe ba zata iya shiga saboda akwai Alqur'an me tsarki!" Jin haka da ruhin Rihanna taji yasa ta kara fusata ta yi ta kwallo da Layla ita kuwa Aliyyah wahala ya hanata kuka. Shigewa wardrobe din tayi tana fa in. "Kefa!" "Rufe kofar tayi duk yadda ruhin yaso shiga ta kasa shiga, dariya Layla wani bulala ta bayyana ta shiga zuba mata ta ko ina. Kifawa tayi akan cikinta gudun kada ta tab'a mata cikinta. Duk da wannan azabar bai hana Layla dariya da kuka ba tana fa in. "Tunda kika sake na gano lagonki, ki gudu kawai zan yafe miki amma tsayawarki anan za a rufe fansarki!" Nufarta tayi tare da shake Layla. A cikin wannan lamarin Maina ya shigo dakin. D'ago kai Layla ta hango Maina a sume da rarrafe ta nufe shi. Ta saka hannunta ta toshe kunnen Maina. "Aliyyah ki toshe kunnenki!" "Tow!" Ta fada a rarrabe saboda abin da ya faru ya saka mata wani irin tsoro da girgixa. Cikin karfin hali ta d'aga kai sama ta fara karanto wasu irin alasuman tsafi wanda ta haifar da wani gagarumin girgizan kasa da na cikin gidantun tana yi a hankali har ta fara yi da karfi kafin ta fara fada da mugun karfi wanda ya saka dakin ya fara tsatsagewa. Karfin sanyi da guguwa yasa Maina bude idanunshi, tarfashewan a hankali ara masu tsini kamar takobi suka fara bayyana tare da wasu irin sarkan ara suka zagaye Ruhin Rihanna, tare da lullube ta baki aya suka rufeta suka saka ta a cikin wani sundukin karfe suka rufeta aka yi sama da shi, saukar da kanta tayi tana kallon Maina hawaye na zuba mishi. Idanunta yayi fari sol a hankali ta koma jikinshi. Jikinta ya koma kamar farkon cikinta har alamu ya nuna bata da jini, domin har ta fara Koriya -Koriya, "Sultan!" Ta furta a hankali ta koma ta kwantar da kanta a hankali ta sauke ajiyar zuciya. D'ago kanta yayi tare da jijigata ya kira sunanta da arfi, duk abin da ya faru ilahirin masarautar babu wanda bai gani ko ya ji abin da ya faru ba, haka ya dauke ta ya fita da ita da gudu. Ba takalmi a kafarshi. Sai lokacin Aliyyah ta fito daga wardrobe din, tana wani irin kuka domin bata tab'a kawowa Layla zata iya bada rayuwarta akan ta ba, haka ta biyo bayansu. Malik da Ammar tare da Jafar da Auta suna masu rufa mishi baya, yadda yake gudu da ita zaka.gane ya fita daga sarrafa kanshi, cikin wani irin zafi nama, Jafar ya tare shi tare da tab'a gefen kirjinshi daidai zuciyarshi. Cak ya tsaya tare da zubewa akan gwiwarshi. Amsar Layla Jafar yayi shima yana jin kamar ya fashe da kuka. "Ku kula da shi, xan tafi da ita." "Ina?" Malik ya tambaye shi. "Wagaduwada!" Ya furta a hankali ya nufi motar da ita, Auta ya bude mishi. "Doctor Jafar! Me ake bukata?" "Zan kaita can idan muka isa zan ajiye ta na dawo da ita amma tabbas a wannan matakin Layla tayi kuskuren rufe ruhin da yake jikinta bayan ta shiga jikinta abu ne me matukar wahala ba wai ban san yadda xan kore ta bane a'a ta shiga mataccen gangan jiki. Kusan ta kashe jikin Layla ne saboda zaman da tayi a jikin Mahaifiyar Layla, ban san yadda xan iya raba jinin Layla da yake jinin Ruhin ba ne. Shi yasa na kyale ta yanxu kuma Layla ta rufeta tare da sakawa a kaita kurkukun rauhanai." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cewa Auta. "Idan ta tafi can zasu nimo hanyar da zata rayu!" "Ni kuwa sai nake ganin babu abinda zai gagari Allah, a barta anan mun hada da ayoyin Allah mu ga abin da zai faru. Idan sadaukarwa ce ma muna dayawa ko babu wasu wasu nan. Abarta mu faffatan domin Allah yana nan." "Shi kenan!" Jafar ya fada, wannan abin ya saka aka auki Maina da Layla zuwa parlour Malik. Wannan abin da ya faru ya saka Queen Hamidah ta ware domin Ruhin Rihanna ne yake haukatatta. Layla na dauke ruhin Rihanna take Queen ta ji kamar an cire mata ciwon da take fama da shi. "Bahira!" Ya kwalawa Bahira kira da sauri ta leko. "Queen!" "Zo nan na.ji sauki meke faruwa?" Cikin wani farin ciki Bahira ta shigo ta fara bata labarin abin da yake faruwa. "Shegiyar yarinya ki nimo min tirsila!" Da sauri ta fita daga angaren, Queen ta shiga wanka, sannan ta nufi bangaren Malik anan ta ga tashin hankalin Malik da Anna da Ummimi. Murmushi tayi kafin ta ce musu. "Hukuncin wanda ya mana tsafi a masarautar Baihak kisa ne, ya kenan Malik zaka cigaba da kallon Maina a cikin wannan yanayin ne? Yarinyar ce matsalar masarautar Yarona a kashe Layla!" "Yaushe yar macukule ta samu lafiya?" Inji Abraham yana kallonta kafin wani yayi Magana Auta ya ce mata. "Da alamu allura zata tono galma, ki tafi kada mu fara hukunta ki, zamu kyale ki ne domin shekarunki." Zata yi magana Babban Malami Sheikh Bin Musa, alkandariya, ya shigo cikin tsantsane irin wanda ya sha ayoyin Alkur'ani ya koshi, tsigar jikinshi ne ya motsa ya mike, kallon Queen Hamidah yayi kafin ya ce. "Assalamualaikum! Ina ga ku bani wuri! Amma ke ki zauna." Ya nuna Queen fita kowa yayi aka rufe kofar ya zauna a kujeran parlour yana addu'a kafin ya kalli Almajirinsa ya ce mishi. "Amso min buta da ruwa nayi alola!" Yana fita ya kalli Queen. "Shekaru arba'in na gaya miki ki daina abin da kike!" Ya fada yana kallonta bakin hayaki ne a bayanta wanda ya hango haka akan Layla har gara Layla ba iya kadai bakin hayaki ba ne hayakine sun kai kala sama da ari akanta. Murmushi yayi ya ce mata. "Ban da tayi sanadiyar tafiyar wancan haka zaki tabbata ki tuba wannan bakin hayakin ya daina bibiyarki domin matukar Yarinyar ta tashi ki nemi mafaka shine gaskiya. Nima zuri'a ne daga Wagaduwada....... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/7, 8:09 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________72 Wani sheke Queen Hamidah take kallon Sheikh Bin Musa alkandariya, kafin tayi murmushi ta ce mishi. "Hala zato kake na bar garin nan saboda wannan abin?" Tambaye shi tana takawa a dakin idanunta akan Layla. "Wannan yarinyar kake cewa na nime mafaka domin zata kashe ni? Tow zan tsaya naga karshen gudun ruwanta." Daga haka ta juya tare da barin parlour tana fa in. "Ka tabbatar ta farka domin cigaba daga inda muka tsaya." Shi a tunaninshi Queen Hamidah zata razana da abun da zai gaya mata sai ya lura irin Hamidah bata bukatar tausassawa gara Allah ya mata yadda yakewa duk wani fitinanne a cikin al'umma. "Allah ya baki sa'a!" Ya fada tare da mai da hankalinsa kan Layla da Maina, kallon Almajirinsa yayi ya ce mishi. "Uzairu ka kira su Nuhu da Amir maza su tare da wasu almajiran! Sannan su hado da kayan aiki!" "Tow ya Sayyid!" Haka ya fita tare da nufi waje, sannan ya kira Amir ya gaya mishi sakon Sayyid ai ko minti talatin ba ayi ba suka iso masarautar, da yayi wani irin shiru kamar babu mutane. Haka suka shiga cikin gidan, kallon Amir Nuhu yayi ya ce mishi. "Akwai karfin tsafi a cikin masarautar nan ga tarin rauhanai kamar babu gobe!" Murmushi Amir yayi yana fa in. "Nuhu fadar nan dole Rauhanai su yawaita, domin an bauta musu tare da jinin Al'umma, ka ga kenan babu batun rabuwa da su." "Babu mafita ne?" "Akwai mana ai ba yau ba Ya sayyid ya gaya musu su dakatar da haka ko ayi rashi me girma!" Suna tattaunawa suka hadu da Auta, murmushi yayi musu ya mika musu hannu. "Yallabai tunda ka bar masarautar nan ka daina zuwa daukar karatu." Murmushi yayi ya ce. "Malam Amir bari kawai ina tare da dan uwana ne!" "Ayya tow ai ba kome." Suka shiga korido na masarautar. "Akwai sanyi sosai!" Nuhu ya fada yana kame jikinshi. "Ka nemi tsarin shaidanu domin suke bin ka ta baya!" Tsayawa yayi zai juya Amir ya riko shi ."Baka bukatar gani!" "Tsafin da ake yi ne ya tara su!" "Kamar ya?" Inji Auta"Anyi tsafi me karfin da yasa kana shigowa zaka fahimci haka." Kunya dai ta lullube shi ya kasa magana a bakin barandar Malik suka same mutane. "Barkanku!" "Yawwa!" Ummimi ta amsa musu, shiga cikin suka yi . "Amir ka fara aikinka shi ba Tsafi bane, ita ce tsafi kayi wani abu akanshi." Sannan ya juya ga Nuhu ya ce mishi. "Nasan Allah ya maka baiwa da iya fahimtar junnu duk da baka ganinsu. Ko zaka taimaka ka yi wani abu akan yarinyar nan. Ni kuma zan tsaya da ayar Allah." "Shi kenan Sayyid!" Ya fada yana me komawa gaban Layla. A hankali ya bude jakarshi tare da ciro wasu tarkace tare da karamin kur'ani. Ya fara karatu a hankali cikin tausashiyar murya, mara