← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 115

Sashe 17

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* __________________ "That's my boy, kuma haka nake alfahari da haifar da irinka don haka karshen kome ya zo koda kuwa ace haka bai samu ba, ba zan tab'a yarda kunci ya cika zuciyarka ba, ta shi ka tafi." Murmushin jin dadi yayi sannan ya mike yana fa in. "na gode Mama! Amma Ayrah tana shirin zuwa Yemen." Yayi shiru kafin ya cigaba da cewa. "Har yau tana son Maina." Murmushi tayi ta ce mishi. "Koda baka kwanta da ita ba, Maina ba zai tab'a had'a hanya da ita ba, balle kuma har kun samu karuwa da ita haka yana nufin babu abin da zai da ita. Kyaleta ta je duk inda zata babu abinda zata samu." "Naji amma yana da kyau ko d'a daya ta samu itama haka zai saka ta nutsu!" "Zan duba lamarin." "Na gode Mamana." Inji yadda ya ce Mamanshi yasa zuciyarta yayi sanyi zata bari Ayrah itama ta rike dan Amma ba dai namiji ba, sai dai mace tana samun d'a namiji tarihi zao iya maimaita kansa, bata shirya ganin tashin hankali ba. Shi yasa take baza zamaninta. "Ka kyaleta ta tafi!" Sun isa Yemen kwana biyu, don haka a gidan da shi Maina ya sayawa Iyayenta da Maman Jasy, suka sauka cikin farin ciki ake tarerayarsu. Musamman ita kanta Aliyah, kada kuga yadda Mahaifiyarta da Maman Jasy ke kula da ita. Haka yasa baki aya ta manta da Maina, sai idan dare yayi sun hadu a daki take tunawa da shi. Tayi ta kame-kame kenan, shi kuma dake bai da lokacinta shima na shi sabgar yawa ce da ita haka yasa baya kulata sao yayi murmushi. "Take your time!" Iya abin da yake ce mata kenan, kuma tasan ko zata kwana tana mishi bayani abin da zai gaya mata kenan, take your time. Haka suke kwana su tashi, kuma kowa ya kama gabanshi. A ranar da suka cika kwanaki hu u, da sassafe sai ga Ayrah cikin gidan. Kowa na barci sai shi da yake ta aiki a akinsu. "Munafukan Allah ta'allah ku fito gamu mun zo, don cin amanar aminta shine zasu tare a gida aya." Firgi Aliyah ta farka tana zare idanu don tun sallah asuba da ta koma sai wannan hayaniyar ce ta farka da ita. "Koma ki kwanta." Juyawa tayi ta kwanta, amma ta kasa komawa barci sai juyi take, tana jin irin zagin da ake musu. Wani ikon Allah duk gidan babu wanda ya fito sai dai can anji kar'ar motar yan sanda a kofar gidan. Daga nan gidan yayi tsit. Daga haka ya cigaba da aikinshi. Yana lura da yadda take juyi, haka yasa shi gyaran murya. Tashi tayi tana kallon shi. "Are you okay?" Ya tambaye ta, gyada kai tayi tare da sauka daga gadon, ban daki ta shiga shima ya ajiye computer din ta nufi waje. Wani lokaci yana iya zuba maka idanu kayi yadda kake so, amma ban da abinda zai taba mutuncinsa da ta ahalinsa, yau a yarima ya e asalin Yarima Baihak shi da ya tura sako aka zo aka yi gaba da Ayrah da uwarta kuma ya saka.aka yi disconnect din layinta yadda zata ci azaba a hannun jami'an tsaro. Sai da ya ha a musu ruwan wanka, sannan ya tashi Nur yayi mata, ya dauko ta a abin dauka tana mishi dariya. "Fafa!" "Hmm haske!" "Shan madara!" "Ok Amra zata kawo!" Bude idanu Husaina tayi tana murmushi, a hankali ta dauki madubin idanunta ta saka. "Good morning Pa!" Isa gabanta yayi ya sumbaci goshinta. "Morning dear!" Ya fa a yana shafa kanta. "Papa Sabahil khair!" "Morning love! Ayi wanka azo a karya." "Pa zamu fita ne?" Gyad'a kai yayi yana kallonsu, Sainah ta fara shiga, can kuwa sai gata ta fito. Mikewa yayi ya fita ya basu wuri, a falo ya samu iyayen Aliyah suna jajjanta masifar Ayrah da uwarta, "Kayi Yarima yau mun!" "Ba kome!" Ya fa a yana nufar dakinsu. Ya samu Aliyah ta cancand'a ado, Aliyah yar kwalisa ce ga ado ga iya daukar sutura, kasa dauke idanushi yayi akanta, omo ta mishi kyau asalin kyau. Don haka kamar wanda aka ja shi, ya nufeta tare da cewa. "Kwalliyar nawa kudinta?" Ai dama ta sani, shi ba zai xauna ayi hira irin na mata da miji da shi ba, sai aukin jidali. Ganin bata tare da shi, abin ya motsa ai kuwa ya janye ya barta nan, tayi two zero shi fa ba ja mishi class. Tunda ya fito suka fita da Yara ya manta da wata Ayrah, sun yi spend most moment a cikin garin Yemen, haka yasa yanayin ya tsaya a ran Aliyah da Yaranta, duk da ma su zasu rigata komawa haka yasa suka yi ta shawagi, a wurin da Yaran suke shakatawa ya kalleta hannunshi cikin nata. "Bance ki zama mafadaciya ba, amma ki koya don kanki." "Tunda na taso ban iya fada ba, kuma har yau ban iya ba, duk abin da kaga Ayrah tayi ta cancanci tayi ne, ex fiance inta na aura me zan iya ce mata? Kasan ta fini gaskiya, ta fini karfi a kowani idan kana nan ne zance kai ne karfina idan baka nan kuma zan rungume duk masifarta." Daga haka ta bar mishi wurin, tana jin zafinshi domin da ya nuna yana sonta koda riritatta yayi da babu me mata haushi kamar tayi sata. But now look at yadda Ayrah take mata bala'i. Haka suka wuri zubur sannan suka dawo gida, wurin Asuba suka bar garin bayan ya ajiye security duk inda zata shiga. Saboda kuma Ayrah ne don yasan bata da dad'i kamar jahila take. Yana barin garin da safe wurin karfe tara baban Ayrah yazo yayi ta basu hakuri akan sake ta, sai da ta kira Maina ta ji wayar a kashe shiga dakin tayi ta ga yar short not. _Ki kira wannan number, zasu sake ta!_ murmushi tayi ta kofe number ta ira, bugu daya aka auka. "Nice Aliyah Mrs Prince Maina, ko zaku sake yarinyar nan!" Ta fa a kamar tana gabansu. "Yes Ma!" Suka fa a mata, sannan ta fito tana wani ha e rai. "Baba na ce a sake ta, and ku ja mata kunne, ta fita hanyar Mijina da ni kaina." "In sha Allah." Daga haka ya bar gidan, yana isa gida ya samu sun dawo sun hi wurijanjan. Amma a ran Ayrah sai ta dauki fansa ta raya, Babanta yayi kokarin nuna mata fa a, amma ina bata ji ba don haka ta kira duk kawayenta da suke zugata ta gaya musu, abun da Aliyah da mijinta suka mata. Sun bata shawara kan amma wanda suka bata na karshe ta amsa. Ta kira Jasrah ta bukaci su gana a wani eatery. Idan suka zo anan zata rufe ta da duka. Wannan shine shirinta, duk haka tun kafin ta kira Jasrah aka kira aka gaya mata, wacce ta bada shawarar. Abin mamaki lokacin da aka kira Jasrah suna tare da Aliyyah, don haka yya saka wayar a hansakuwa, Aliyyah tana ji wani irin mamaki ne ya kamata, "Gaskiya ba zata samu zuwa ba, idan kuma ta kira mijinta ya bata izini shi kenan!" "Na dai gaya muku, koda zaku ta shirya domin Ayrah ta shirya zane Aliyyah ne." Tasan halin Ayrah tun ba yau ba, kuma zata iya duk abin da aka fada, sai dai ko ta gayawa Maina babu abinda zai yi, don haka ta kira shi. Ta gaya mishi abin da Ayrah ta shirya, bai yarda da reni ba, don haka ya ce mata ta je, babu abinda ta isa ta mata ko baya nan ba zata iya kome ba. Ta ji shi ne kawai, amma tabbas Ayrah idan ta saka mutum a gaba, bata da kirki ko kadan, don haka suka zuba idanu har tsawon kwanaki uku, sai ga kiran Ayrah ta fadawa Jasy tana son su hadu amma da Aliyyah tana son bata hakuri da abin da tayi, "Ki ce manya yanzu girma yazo kenan?" "Wallahi kuwa, ina sad'akar uban mijinta dole naja girmana!" "Gaskiya kan!" Daga haka suka yi sallama Jasy ta kira Aliyyah ta gaya mata ita kuma ta gayawa Mijinta. Maina kuwa abin da yayi kiran Ammar yayi ya hada shi da Halifa Abu Ammar, sun jima suna magana. Wanda hankalin Halifa ya tashi, bai bata lokaci ba ya mike domin babu zama ya nufi chamber na Malik. Bayan sun gaisa a nutse sannan ya gyara zama ya ce mishi. "Tsakanin Maina da Ayra'atu wa kake so?" Kallon Halifa yayi kafin ya kauda kai ya ce. "Ana sauya mace amma shi d'a ba a sauya shi, sai dai a haifi kaninsa." "Ka kira matarka ka ja mata kunne, ta rabu da matar Maina, abin da take yi a madadin ya janyo kusancinku, kara nisanta ku take koma meye a duba lamarin." "Amma akan me zan mata magana?" Inji Malik a fusace. "Ok shi Maina zai gaya mata abin da kuke mata, ruwanka ne nime Ayra'atu ta kyale Matarshi." Wani irin zufa ne ya karyo mishi. "Ni Maina zai yiwa barazana?" "Ba barazana ba ne, Maina yasan abin da ba kowa ya sani ba. Duk abinda zai faru Maina yana kallonshi a matsayin shiri ne ba fararre ba ne." Wato ma'anar kallon da yake mishi kenan, shi yana mishi kallon biri, shi kuma ayaba yake mishi kallo. "Ok na ji ba zata kara wani kwanaki ba!" A take ya kirata, ya ce. "Duk abin da kike yi yau ina zuba idanunki a Baihak!" "Malik ban gama ba!" "Nace yau ki taso, kuma zan yi magana da Office din Embassy maza a tattaro ki, ina jira." "Amma!" "Do as I said!" Ya kashe wyaar baki aya, ya cillar, wayar Halifa Abu Ammar ne tayi kara. "Hello Maina mun yi magana." "Shi kenan!" Daga haka ya kashe wayar, Ajiyar zuciya dukkansu biyu suka sauke. "Me yasa kake tunanin Maina zai iya samun damar juya mu lokaci guda." Gyara zama Halifa
Chapter 17 · 0% Book details