← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 115

Sashe 60

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ita kuma da ta fasa mata goshinta ba mutum ba ce? Ita Sanah ba akan irin wannan mugun halin kika maida ita garinku ba? Tunda Layla ta zo gidan nan akwai yaran Yayun Mubarak basu da abokiyar hira sai ita, kuma ba a samu matsala da su ba sai da ita Sanah, in fact ai ba ita daya ba ce me yasa bata yiwa sauran haka ba? Hm" ya juya tare da riko hannun Layla suka fita, ta wanke mata fuskarta sannan ta saka magani da plaster, koda ta tambayeta kuka ta fashe mata da shi har da shashekar kuka. Kyaleta Bahi tayi tana me mita a ranta, ita ta tsani cin zali wannan masifar da me yayi kama. Kuka da kururuwan Sanah yasa Mubarak da Maina shigowa, Mubarak ya wuce da ita asibiti ita kuma Layla, Maina ya zuba mata idanu yana mamakin yadda ta kasa magana sai kuka take. "Ni na tambaye ki, ki min kuka ne? Me yasa kika amfani da tsafi?" D'ago kai tayi tana me kallonshi kafin ta sunkuyar da kai tana fa in. "na cancanci mutuwa, ban san yadda aka yi tsafin ta tasirantu akanta ba, kayi hakuri ba zan kuma na daga yau na daina amfani da tsafi har na mutu!" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya yana fa in. "Ki kula da kanki!" Ya fita yana rike hannun Nuri da take ta kuka itama. Tunda ya fita ya samu Aliyyah ranta a b'ace sai fada take tana ita ba zata yarda ba. "Tunda ba zaki yarda ba, je ki karya mata hannu kawai a wuce wurin." Inji Bahi da ta gaji da mita. Shiru tayi bata ce kome ba, shima Maina yana jin ta ya kuma share bai amsa ba, kawai dai baya son magana ne da hayaniya. Bayan awa guda Mubarak suka dawo an daure hannun, ba karamin kuka Sanah ta sha ba, har sai da zazza i ya saukar mata. Zuwa jikin Aliyyah tayi ta kwanta. Tana ajiyar zuciya. Rike hannunta tayi zuwa dakin da suka sauka ta kwantar da ita, duk da Layla tana dakin amma Aliyyah bata kalli inda take ba, tana zaune can gefe. "Mum ki ce ya fita a dakin?" D'ago kai Layla tayi tana kallonsu mamaki cike a fuskarta, tana jiran taji me Aliyyah zata ce. Sai kuma taji akasin haka. "Babu inda zata, bana son abin da kike yi Layla ba sa'arki ba ce." Ta fada tana kauda kanta. Abin ya bawa Sanah mamaki ita kuma Aliyyah abin da yasa tayi wannan maganar goshin Layla da ta gani tare da yadda fuskarta yayi jajjur kamar bata so haka ya faru. Kawai sai Aliyyah ta ji a ranta idan yau Sanah ce a matsayin Layla haka itama zata fuskanci takuri da matsin lamba, dauke kai tayi daga kanta ta mike tare da barin dakin. Tana barin dakin Layla ta matsa gefen Sanah din da take hararanta. "Kiyi hakuri Sanah!" "Mtsew!" Daga haka ta juya mata baya, wannan abin ya kara damunta. Har dare walawalar da sauki, Layla taki fita tana dakin, hatta abinci ita ta kawowa Sanah don wulakanci da ta ajiye mata shure abincin tayi tana fa in. "Allah ya kiyaye ni naci abincin hannunki." Ta fada tana shure abincin. "Wannan wani irin hauka ce?" A razane ta kalli Maina da ya shigo. "Laifina ne na kawo mata abincin da bata so!" Ta shiga tattara abincin tana gyara wurin. Bayan ta gama ta fita daure fuska yayi yana kallon Sanah. "Sa'aki ce?" Ya daka mata tsawa. "Sorry Papa!" Ya rasa me yasa Sanah take da mugun hali. "Me yasa kike haka? Don kin ga tana muku aiki ne?" "Papa ni na tsane ta ne!" Mamaki ya cika shi don haka ya zauna da ita yayi ta mata nasiha, sannan ya fita ya hado mata tea ta sha, sannan ya bata magani. Tana zaune a can wurin cin abinci a kasa ta zauna tana ci, don ta ga babu kowa tana gamawa ta mike tana kallonshi da ya zuba hannu a cikin aljuhun wandonshi. Yana waya. "Ina jiranki zamu tafi!" Fita yayi daga gidan, ta zauna a kujeran kitchen din tana shan ruwa. Tana zaune Aliyyah da Bahiyyah suka fito. "Kina nan ne?" Gyada kai tayi tana wasa da kofin hannunta. Bayan Bahi ta dawo daga raka su, ta zo ta zauna tana kallon yadda tayi shiru. "Kina tuna kawayenki na makaranta ne?" Girgiza kai tayi tana murmushi. "Me kike tunawa?" "Babu kome!" "Kina son wani abu ne?" "Ina son na koma wurin Mamana ne." Shiru Bahi tayi tana kallon yadda tayi shiru sai ta bata tausayi. Don haka ta ce mata. "Zaki amma ki tambayi Bro don ya ce na lalata mishi tarbiyyarki da yawo tunda kika zo!" Murmushi Layla tayi tana wasa da abin hannunta. "Ni zan wuce wurin mijina." Ta fada tana barin wurin, "sai da safe!" Inji Layla. "Allah ya tashe mu!" Itama ta kashe wutar gidan sannan ta wuce dakin Shimfida tayi a kasa tare da gyara ko ina ta kwantar da Nuri a gefenta, suka kwanta. Har wurin tsakiyar dare tana kwance bata yi barci ba, idanunta a rufe kamar an ce ta bude tayi idanu biyu da Hilda. "Ke wacce irin mutum ce da kike hakuri da su? Ki kashe su kome ya mutu ma." Girgiza mata kai tayi tana fa in. "Ni fansata babu ruwan su!" Shake wuyarta Hilda tayi tare da d'ago ta, cak ta buga ta da bango sai da Layla ta suma. Haka ta zube a kasa a wurin, sake shake wuyarta tayi sai da kuma farkawa ta sake ta ta fadi akan fuskarta. "Duk lokacin da wani ya cutar dake baki rama, ko yunkurin ramawa ba, sai na kashe kowaye na kuma karya miki hannu!" Gashin kan Layla ne suka mike tare da rike hannun Hilda sai da suka mike, rufin dakin ne ya bude suka fita sama da gudun tsiya,sai da suka yi dogon tafiya kafin suka fada cikin ruwa. Kafin suka fara wani irin dambe me azabar karfi. Babu shakka wannan shine karon farko da Hilda tayo sanadin farkawa wata goddess Tal, wacce ta nutsata can karkashin ruwan tare da daureta da sarkan ruwa. "Tal ina ruwanki da ni? Da ke da Kalya kun dame ni meye nayi muku." "Anan zaki zauna har sai na bukaci haka." Daga nan ta fita cikin ruwan tayi sama, sai gata a tsakiyar dakin ta dirko sama, nufar wurin Sanah tayi ta shafa hannunta, kafin ta daki goshin yarinyar. "Fito!" Wani shaidani ne kamar kuda ya fito, "kai ne kake sakata tab'a Layla!" "Shugabata ki gafarce ni. Da nasan ala arku da layla babu abin da zai kawo ni." "Ka tafi ka rufe kanka sai na nime ka." Fita yayi ya bar wurin. A hankali Tal ta juya inda Nuri take kwance ta zuba mata idanu. Shafa kan Nuri darling tayi tana murmushi. "Ina fatan soyayyarku ta dawwma." Sannan ta kwanta daga nan haske ya fita daga jikin Layla ta shiga barci me nauyi, kallon Layla tayi cikin tausayi domin tasan yadda zuciyar Mutane take, fansa daban, amma saboda Nur din ta hakura ta jingine kome yarinyar da sun kusan gamawa da ita, don ma Hilda tayi wani abu duk da sharrin ta, tana son Yara da aukar kaddaransu bin sama tayi tana ta koma can ruwan. Kallon juna suka yi ta ce mata. "Naga kin bawa Yarinyar abin karya ne yasa?" "Saboda na gaza ceton rayuwar dan cikina, ita wannan yarinyar ganinta nake kamar tawa saboda Maina ya haifeta maida da Salahudeen kuwa kamar abu daya ne!" "Karshen cin amana kenan, gashi ke ba bil adama ba, ke ba aljana ba sun lalata Miki rayuwa kusan shekaru aru-aru," dauke kai tayi tana fa in. "Idan Maina ya kwanta dani, ya bani kome zan dawo...." Make kanta Tal tayi sai da ta kifa. "Ke mahaukaciyar ina ce? Maina ne zai kwanta dake? Har kike tunanin wani abu can? Kul ki shiga jikin Layla na gaya miki!" Tura baki tayi tana hararan Tal, "Ni ba ni bace matsalar Baihak fansata da Baihak kadan ce, fansan da me dauka Layla ce sauran fitinar da xai biyo baya tono kasusuwan Rihanna!" Daga haka ta b'ace baki aya. A ina aka binne kashin Rihanna tabbas an gudu ba a tsira ba waye zata gayawa haka. - a can Baihak kuwa zubawa Malik idanu Hamidah tayi ranta a matukar b'ace. "Tun yaushe kasan Maina ya fara soyayya? Taya zan zuba idanu har aka ya faru? Kasan adadin wahalar da aka sha domin gina masarautar nan da zaka ce min Maina ya fara soyayya? Kenan duk wahalata ya zama na banza kenan. Maza ba yau ba, ba gobe ba a je tsohon gida a tattaro kirti majiya karfi su tono uwar kiyayya, dole mu rusa duk wani jin dadin Maina a haka bai fadq soyayyar ba ya kasa bamu lokacinsa idan kuka sake naji bakin labari sai na tabbatar babu labarin kowannenku." - Washi gari ihun Sanah ya tashe su, kallonta suke. "Ciwo na ya warke, wayyo Ciwona ya warke na rantse da Allah na warke!" Tayi ta ihu tana tsalle, ban daki Layla ta wuce da Nuri ta mata wanka sannan ta dawo da ita daki ta shiryata. Kafin ta fito parlour ta ha a mata abin karyawa tana bata, Maina da Aliyyah suka shigowa. "Good Morning papa ciwon Sanah ya warke!" Kallon fuskar Layla yayi ta wutsiyar idanu, Aliyyah ta wuce ciki da sauri. Mai da kanshi yayi kan Tv har Bahi ta fito, ya ga itama Layla ta wuce angaren Bahi. "Kaji wani shiririta wai hannunta ya warke sai kace Magic da a Baihak ne sai an sare kansu." "Idan kuma da gaske ne fa?" "Sai a nimo wanda yayi sidabarun!" Fitowar Layla daga angaren Bahi ya ce. "Hmmm!" Ya fa a yana kallon shashin da Aliyyah suke fitowa sai murmushi take tana farinciki hannu ya warke dama ba karyewa hannun yayi ba kenan? Watsar da zancen yayi suka karya sannan suka yiwa Bahi bankwana, Bahi ta raka Aliyyah da Yara wurin Uwar mijinta, shi kuma yana zaune a parlour, fitowa tayi suka kalli juna ta sunkuyar da kai ta wuce kitchen tana hada abinda zata ci ta ji alamar shi a kofar kitchen din jikinta ne
Chapter 60 · 0% Book details