Sashe 74
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tow Allah ya kyauta, tunda shi ya zab'i haka tow a kyale shi mana tun yaushe ake so ya ara auren yayi yanzu kin ga sai ta haifa me mishi d'a namiji. ba haka Queen Hamidah ta so ba, Lallai an fara warware mata aikinta domin tasan Malik yana da damuwa akan fushinta, kauda kai tayi tana fadin. Ba sai ka gaya min d'anka ne Maina ba, tashi ka tafi amma da muna da daraja zuwa ya kamata yayi ya gaya mana zai kara aure ba wai muji labarin daga sama ta ka ba, ko da yake waye ya sani ko kana behind abun da ya aikata. girgiza mata kai yayi cikin gajiya yana fa in. "Wallahi ban tab'a shiga wani abu don Maina ba, ke kika ce min idan na sake mishi zai fara harina tare da kokarin mai da kanshi sarki tun lokacinsa bai yi ba, Mama ni wallahi ban sakewa Maina har haka ba, duk da ina son na samu lokaci na sake mishi amma ina kan abin da kika daura ni akai!" Hura hanci tayi jin ya fadi ai yana kan abinda ya daura shi, tafe ta zuba mishi idanun sannan ta mike tana zaga parlour din. "Anyway! Ka ce Maina ya zo da iyalinsa ayi bikin auren domin wannan karon a nuna mishi gatar da akewa kowa sannan Haisam da Ibrahim ayi bikinsu kana a bawa Maina sarautar Magajin garin Baihak! gyada kai Malik yayi yana kara fa in. "Godiya nake in sha Allah zan yi abin da ya dace Allah ya ara girma da lafiya tare da nisan kwana!" Jeka Allah yayi maka albarka! Amin! daga haka ya barta tana kallonshi, kamar tayi tsuntsuwa ta nufi wurin falwa amma ina ba hali saboda rana na ne, lokacin da Malik ya isa bangaren Ummimi kallonta yayi kafin ya ce . "Ashe Muhammad ya ara girma har haka ne?" Sai kunya ta kama Ummimi cikin kaskantar da kai musamman yadda aka mai da ita kamar mara daraja ta ce mishi. Kai hakuri an shiga hakkinka, ni kaina ban san da zancen ba sai da Hajja ta bukaci haka, sannan yarinyar marainiya ce don Allah kayi hakuri an maka ba dai-dai ba, a matsayinka na Uba. Yar dariya yayi yana kallonta baki aya sai yake jin tausayinta sosai a ranshi ya ce mata. "A'a ke sau nawa aka baki hakuri idan an yi miki laifi? Kin ga Khamila Maina yana da damar zab'awa kanshi abin da ya dace kuma yana da ikon yin yadda yake so amma kafin nan ki gaya mishi ni Ubanshi Maina let me behind, kuma na san laifina ne yanzu ina son na janyo shi jikina amma bani da wannan ikon tunda Malik ya warke baki aya yayi matukar sanyi tare da janye duk wani abu da ya danganci mulki, asalima tsoro ne ya ke cika mishi zuciya ba don kome ba sai don yadda Abu Amma ya bashi labarin rashin lafiyar da na yayi ga sanadin da ya kawo. Sannan yasan Abu Ammar ba kazamin mutum ba ne, duk da abin da suke da uwar shi Abu Ammar yasha bashi shawara ya daina irin wannan abin akwai hatsari wata rana za ayi niman rayuwarka sannan da kowa ma za a iya hada baki a cutar da kai, haka yasa ya katse yarda da ganin kowa sannan ya rungume Ummimi domin yasan ba zata tab'a cutar da shi ba. Sannan uwa uba yadda take kula da shi abin har ya b'aci. Ga magani da take hada mishi yana sha domin kuwa ya lura da yadda take hada mishi maganin ba karamin taimaka mishi yake ba, Kayi hakuri Ayrah ta dawo! kallonta yayi kafin ya ce mata. Ke baki da kishi ne? dariya tayi iyaka sannan ta ce mishi. Kishi dai? Haba ina da jikoki irinsu Khalifa da Khalil, Hassanah da Husainah, Banafsha da Nuriyyah kishin me zan yi? Ai naci dubu sai ceto ba dai ta mutum ba sai ta Allah! ware idanu yayi yana kallonta kafin ya ce mata. "Kina nufin ke kainuwa ce?" Murmushi tayi me sanyi ta ce mishi. Tabbas!" Daga haka ta wuce ta barshi nan. Dare aka ce mahutar bawa, ga Queen Hamidah bai zame mata haka ba, ita da Bahira suka nufi cave suka jirata a waye ita kuma ta shige cikin ashin asar. "Maganar auren Maina ko? Nasan shi ya kawo ki!" Inji Falwa, Ni dai a duba min taurarin yarinyar. yadda ya nutsu bai ga kome ba sai da ya fito da Gorunfa yana shafar kanshi ya ce masa. "Ban ga kome ba!" Kwanciyar shi Gorunfa yayi yana birgima kafin ya d'ago kai yana kallon Falwa ya kalli inda aka daure Kaka Jami. Ya lumshe idanu kafin ya bude yana wani irin ihu. Takawa Falwa yayi har zuwa inda aka daure Kaka Jami ya shafa wurin. _Tabbas zata dawo a daidai lokacin da kuke nimanta, ita kuma ta jima da shahara tare da saninku da shirinku_ tsaki yayi da ya tuna kalaman Jami. Da wani abu ne? girgiza kai yayi yana me fa in. "Bari na kira Tirsila!" Haka yayi kuwa kamar minti goma sai gata. Lafiya dai ko? nan suka bata labarin abin da yake faruwa. Girgiza kai tayi tana me buga sandarta take Maina da inda yake ya bayyana amma babu fuskar matar da y aura ga Yaranshi da Aliyyah amma babu fuskar abin da suke bukata dake buga da sandar tayi da kasa, sai gashi za a nuna Layla amma sai ta B'ace haka tayi har sau uku a hankali bayan Layla ya bayyana sanye cikin wani irin shiga da aka yi ado da zinari. Yawwa gata nan saura fuskarta. sai dai kash sake buga sandar yayi daidai da karyewan sandar. Tare da cakar kafar Tirsila ta fasa ihun da yasa ta faduwa, take hoton Layla ya b'ace. Wacece haka? cikin azabar da take sha ta ce. koma wacece dole mu tsaya muji kome akanta! ai kuwa nan suka shiga bawa Tirsila taimakon gaggawa. A take Falwa ya zuba mata wani garin magani me wari take ciwon ya b'ace. Ya zamu yi kenan? kusan me? Matu ar kuka binciko min yarinyar ni nayi muku alqawarin babban al'amari." Kallon juna Falwa da Tirsila suka yi kafin suka mike tare da binciko yarinyar. " Yadda tayi maganar ya ara musu kaimin binciko yarinyar, ita kuwa Hamidah babban damuwarta tasan wacece haka, lokacin da ya auri Aliyyah haka tasa aka binciko mata Aliyyah. Sai dai kuma basu kai ga cimma bu atarsu wani irin haske ya bayyana masarautar Baihak ne ya kama da wuta, har sai ta wutar ya watsu kansu. Haka suka ja da baya, a hankali suke ganin to bayanta tana tafiya dauke da sandar tsafi, kayan jikinta farare ne juyawar da zatayi hasken ya b'ace hankalinsu ya tashi. Kai wacece haka?" Nan suka ta ihu daga karshe Tirsila ta bar su, ta dawo gida ganin Sanaya tana zaune ita aya. "Me kike a wannan lokacin?" "Tun fitarki nake zaune ina jiranki!" "Tow wuce ki kwanta!" "Ki bar bincike akan matar da Maina ya aura gaba idan kika matsa mutuwa zaki yi!" Daga haka ta wuce abin ta domin tasan Layla tayi karfin da babu wanda ya isa dakatar da ita, babban damuwar Sanaya shine yadda Maina ya zurme akan Layla tasan matu ar yadda tayi shiru nan zata iya karban kowacce irin addara walo ta mutu ko shi ya mutu. Wanda haka ba karamin rashin hankali ba ne.. Tunda Hajja ta gayawa Auta gaskiya dakyar ya bar garin, amma babu lafiya domin kuwa ji yake kamar zai mutu, zai iya hakura da kome amma ban da Layla ba zai iya ba. Kwanan shi biyu ya dawo Washington. Dai da yayi da gaske kafin ya nutsu, don haka ya tafi wani chamber da Maina ya warewa kanshi ya samu yana hutawa. "Assalamualaikum!" Ya yi sallama yana shiga parlour. "Barka da hutawa Yaya Muhammad!" Yadda yayi maganar yasa shi d'ago kai yana kallon Haisam din. "Barka Haisam!" "Yaya Muhammad!" Rufe littafin yayi ya zuba mishi idanun. "Yaya Muhammad!" "Na'am Auta!" "Don Allah ka sake Layla ni nafi dacewa da ita domin rayuwata babu barazana Yaya Muhammad kai kuma rayuwarka akwai barazana, yanzu Baihak da kowa jiranka ake ka haifi da namiji a saka Malik murabus, idan har Layla ta haifi namiji rayuwarta zata lalace kamar Ummimi, a yanzu ka ga Aliyyah Yara mata ta haifa amma bata da banbanci da iyayenmu kwarakwarah, don Allah ka kyaleta yarinya ce da babu ruwanta." Ya fada muryanshi yana rawa. Murmushi yayi sannan ya ce mishi. "Ka fini gaskiya Haisam sai dai Layla she meant to me!" Ya fada yana dariya, "Idan har Layla zata haifi yara maza da mata dubu ba zan manta da rayuwarta ba, saboda ita ce mace ma farko da nake kaunar ta da sha'awarta, ina bana jin zan iya barin wani ya rabeta kai ko mutuwa nayi bana fatan wani ya auri matar da na kwanta da ita domin rayuwata nata ne har abada ba zan bar wani ya rabeta ba." Kamar zai yi kuka ya ce mishi. "Zan gaya mata gaskiya!" Dariya Maina yayi wanda ha oran shi suka bayyana. "Ba laifi ka gaya mata haka ma ka kyauta, kada ka damu bani da zafi akan ka gaya mata. Amma ka sani ba zaka iya zama da Layla ba ko da kuwa na sake maka ita domin ita din ta musamman ce." " kana nufin kune kawai masu sa'a?" "A'a ni bani da sa'a, kawai rayuwata na sadaukar domin nata, tana da buri kuma tana da abin da zata cimma domin al'ummarta ita kanta shugaba ce idan kuma ka matsa lallai zaka shiga tsakaninmu tow wallahi babu abin da zan iya maka kuma ba zan yake ka ba, kawai dai nasan zaka fuskanci matsala da zata kai ka ga mutuwa. " "Zan mutu domin ita!" "Ni dama can matacce ne tun daga ranar da ta mutu domin bukatarta....... (Yaushe layla ta mutu domin bukatarta Allah yasa masu hangen nesa su tuna da ranar ) Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS _* Mai_Dambu _______45 Tashi Auta yayi cikin tsananin damuwa ya ce. "Zan gaya maka gaskiya ina son Layla kuma zan cigaba da sonta duk da na san zunubi ne, domin