Sashe 82
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta samu har lokacin tana tsaye. Kallo daya suka yi wa juna. Layla tayi murmushi tare da jan kofar ta rufe bayan ta fito daga cikin dakin. "Mum muje parlour." "Wurin mijina na zo!" "Yana barci!" Layla fada tana kallonta, "Ki bani hanya na wuce!" "Ko kin shiga ba zai tashi ba sai lokacin da nayi niyyar ya tashi" ta fada tana nad'e hannunta a kirji. "Ke ni.!" "Mum har yau ina ganin girmanki, ki je kawai kada ki ja ni dayawa domin ba take nake ba Please ki tafi ki kwanta, Mum ni nasan baki aya baki da matsala, ni ce ba zaki yarda mu zauna wuri aya ba. Mum wallahi na rantse da Ubangijin da kike bauta mishi ban auri Maina don na cutar dake ba, nawa bukatar daban Please ki yi hakuri ni bani da buri dayawa idan na ci kasuwa zan kara gaba, ba zaki kara ganina ba." Kamar wacce ta daure Aliyyah domin kalmanta sun kashe jikin Aliyyah ainun sannan sun saka Aliyyah jin wani irin fargaba. Juyawa tayi zata bar kofar Layla ta ce mata. "Kiyi hakuri!" Ta kara furta mata, sannan ta koma dakin ta kwanta a jikin Maina tayi lumo, hawaye na zuba mata. Sake d'ago kai tayi tana kallon Maina da dukkan soyayyar d take ji bata tab'a yiwa wani d'a namiji ba, shafa sajensa tayi tana jin hawaye na zuba mata. Bakinta ta kai kan nashi tana sumbata ai kuwa ya ware idanu ya cabke yana wani irin tsotsa. Da sauri ta cire tana fa in. "Ni dai bani da lafiya!" Janyota yayi samanshi yana fa in. "Rider me!" Bude idanu tayi tana kallonshi. "Sultan!" Sai kuma ta rufe bakinta, sama yayi da rigar jikinta yana shafa kayan marmarinta da suke ta kara hab'aka saboda suna jin dadin yadda ake tab'a su, girgiza mishi kai tayi tana fa in. "Oho!" Tana makale kafadarta. Zamar da wandon jikinta yayi kasa yana kallon yadda ta dauke kai. "Kinyi kuka ko?" "A'a!" "Na rantse kin yi kuka gaya min me aka miki?" Tura baki tayi tana fa in mafarkin kakata nayi." Janyota yayi ta fada jikinshi ya kai hannunshi baki aya yana zame rigar jikinta tare da wandon daga nan mutumin nan ya shiga raya bidi'a son ranshi ( Dan iska) sai da ya nikata son ranshi sannan ya jata suka shiga ban aki suka yi wanka. Suna fitowa ta shirya cikin riga da wando rigar har gwaiwata, ta kalle shi tana langwabar da kai. "Sultan yunwa nake ji!" "Zo na goyaki!" Ya fa a yana nuna mata bayanshi da sauri ta isa gare shi. Ya dan sunkuya ka an ta hau bayan ya zunkud'ata. "Wash!" Ta furta tana cizon bakinta. "Lafiya?" "Lafiya lau ina ga bakona ne zai zo, muje Sultan dina!" Haka ya fito da ita ko ya manta gidan akwai mutane, kai Auta ka shigo gidan kenan idanunshi ya sauka akansu. Wani abu yaji ya dake shi, da sauri ta sauka a bayan Maina tana me juyawa da gudu zuwa dakinta, ta rufe domin ta ji mugun kunya. "Morning Mr Maina, da fatan ka gaya mata waye kai?" Inji Auta. "Bata bukatar gabatarwa ta domin abin da ka gani ya ishe ka, ka fahimci yadda abin yake yanxu ai!" Juyawa yayi Maina ya bishi da idanu. Dakin Aliyyah ya wuce ya samu suna karyawa da Yaranta. "Kun tashi lafiya?" "Papa Ina Mamina!" "Zo muje wurinta!" Ya dauki Nuri darling zai fita Aliyyah ta ce mishi. "Lokacin da na haife ta ni daya na sha azaba ba da Layla ba, ajiye min ya'ta." "Ni kuma ba karamin mutum ba ne." Ya fita da Nur din da gudu ya bi bayanshi. Koda suka isa parlour Layla suka samu tana ganin yadda suke abu ta ce mishi. "Papa ka bata Yarta, yarta ce fa kada mu so kanmu dayawa abin ba dad'i ko ni aka yiwa haka xan ji zafi amma ba zan yarda kowa ya sani ba." Ta fada tana kallonshi, bude baki yayi zai magana ta ce mishi. "Tafi mu gaskiya bata Yarta! Ban da akan hanya nake ai da sai na cika maka gida da irinsu Nuri amma kannensu ba su ba, tow na san koda na tara zan tafi na barsu shi yasa ba zan fara ba don kada su zama marayu irina!" Ta wuce dakin bayan ta dauki ruwa. Tun kafin ta isa dakin take zubda hawaye domin Allah ya jarabce ta da kaunar Yarinyar, sai dai Uwarta bata bukatar alakarsu, tunda ya shiga dakin take kuka sosai, tana jin a ranta itama zata haihu "tow idan na mutu fa?" Ta fada tana rufe bakinta, hawaye na zuba mata. Ta jima a dakin har ya kawo musu abin karyawa. Zama yayi yana kallonta."ina so ki haifa min Yara masu irin halinki!" Hawaye ne ya kwace mata. "Idan na haifa maka su zan mutu, idan na mutu waye zai rike min su." Share mata kwalla yayi yana fa in."in sha Allah, muna tare ko mutuwa ce da yarda Allah tare zamu tafi!" Ya fada yana hada goshinsu. A can dakin Aliyyah kuwa kiran Jasy tayi tana gaya mata yadda gidan ya koma kamar hell. "Kiyi duk yadda kike so kin ji, ni tsakanina da ke sai fatan Alkhairi." Duk yadda taso su yi magana fir Jasy karshe kashe wayar tayi babu mafita. A yan kwanakin nan Layla tana fama da ciwo, amma haka take zama a dakin ita aya Aliyyah ko abinci bata tunanin bata, sai dai Maina ya mata oda yarinyar tana yawan zama tayi ta kuka tana jin gara mutuwa da rayuwar da take a wurin Maina take da sukuni shi yasa ta mai da shi kamar Uwarta da ubanta. Abokinta mijinta kawarta. Shima kuma don a zauna lafiya yake janyawa daga gare ta, amma a haka Aliyyah cewa take yafi son Layla akanta, lokacin da suke waya da Ammar yana nuna mishi gidan ajiyar zuciya ya sauke ya ce mishi. "Kamar kun san yadda nake son tsarin gidan, kaga can gefen Aliyyah da Yaranta nan gefen myfussy cat anan zata zauna tayi ta haifa min Yara masu kalar yayan baby!" "Dan iska kace kaji dadin kwaila shi yasa kake wani kaudi!" "Eh!" Ya fada yana shafa sajensa. "Maina ka ji tsoron Allah!" "Hala tsoronka xan ji dan ubanka!" "Allah yasa baka yaga musu yar mutane don na lura!" "Allah ya tsunewa mai son jin sirrin mutane!" "Amma kai dai dan kutimar Uba ne Allah yasa na san fara nasan baka." "Ni kuma iya su na sani shi yasa naji bana jin sha'awar wasu." Haka suka yi ta hira cikin farin ciki. "Don Allah kada ka zo kayi abin kunya kasan akan ka aka fara soyayya kada ka sa yan matan Baihak fara kishin Layla!" Shafa kanshi yayi yana kallon Ammar. "Na gaya maka gaskiya don Ubanka ko na barka haka?" "Idan kace kada ka fada dan iska mayen mata!" "Eh mana fada da ihu ka.kara da tsalle, Ina son soyayya, kuma zan nunawa duniya cewa karya ake babu wani tsinuwa akan soyayya!" "Sare kanka zan yi ba zaka ja min masifa ba kai sai an jima!" Ya kashe wayar yana dariya shima dariya yayi sannan ya shiga cikin gidan, dakin Aliyyah ya shiga ya samu ta takura Yaranta a dakin. "Nuri ga pizza dinku!" Ya mika mata, Sainah ta amsa tana fa in. "Allah ya ara budi, Papa ya jikin Ma." Hadiye yawu tayi saboda yadda Aliyyah ta kafe ta da idanu. "Bata da lafiya ne!" "Hmm! Dazun na je dauko nuri na samu ta fadi a kasa!" Ba iya shi ba Hatta Aliyyah sai da ta mike. "Me yasa baki fada ba!" Ta ce mata. "Ina tsoron kada ki dake Ni ne!" Sake abincin Laylan yayi ya fita da sassarfa, ya isa dakinta. Ya samu kofar a bu e tana kwance rike da cikinta. Kamar bata numfashi da alamu wanka ta fito cak ya auketa ya sakata kan gado ya bude akwatin ta ya ciro kaya ya saka mata, da sauri ya dauketa suka fita Aliyyah zata bishi ya ce mata. "Ki tsaya a wurin Yaranki, tunda kika zabi haka sai kiyi murna amma idan Layla ta samu matsala ba zan yafe miki ba!" Ya nufi motar, daidai fitowar Auta da gudu ya isa tare da tambayar shi."ina key?" "Yana Aljuhuna!" Hannu ya zura ya dauko ya bude motar Maina ya sakata a baya tare da zama a gefen ta ya daura kanta a jikinshi, haka suka isa asibitin. Ana ganinsu aka karbe ta. Cikin ikon Allah abin da aka fara samu shine rashin jini ( To Team Layla ba ciki ba ne ) rige-rige aka yi a tsakanin Maina da Auta sai dai wani abu tashin hankali da Maina yake ciki yasa ba a dibi jininsa ba, domin ya hau, na auta aka diba, sai lokacin Maina ya lura da yadda tayi fayau abin mamaki dama bata da jini ne? Tambayar da yayi yawa kansa kenan. Haka ya zauna aka saka mata laida biyu, ya koma wurin auta yana samu ya bar asibitin, kiranshi yayi ya ce mishi. "Kana ina ne?" "Baihak!" "Kana hauka ne?" "Kayi hakuri! Na jima da haukacewa akan Matarka, shi yasa zan yi nisa da ku, gudun kada a samu matsala." Kashe wayar Maina yayi yana jin babu dad'i sam bai dace Auta ya saka kanshi a irin wannan lamarin ba, amma babu yadda ya iya tunda Allah ya gani Matarshi ce kuma tun fil azal baya jin zai iya rabuwa da ita don Auta sannan ba zai rabu da Layla sabida Auta ba, haka yasa shi share batun. Har zuwa dare aka sallame su, suka dawo gida. Tun a hanya ya zo musu da Abinci koda suka isa gidan Aliyyah ta kawo na musu abincin da farin ciki Layla ta amsa tana fa in. "Allah ya ciyar dake ranar da babu me baki!" Ta amsa tana me zama ta fara ci, kamshin abincin ne ya dake ta, a hankali ta rufe tana fa in. "Bana son kamshin tafarnuwa." Ba Aliyyah ba hatta Maina da ya shigo dakin sake baki yayi yana kallonta. "Tow ga wannan ki ci!" Ya juya mata soyayyen namar kaza da ya zo da shi. A hankali ta kai bakinta zata ci ta d'ago kai tana