← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 115

Sashe 105

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amo da sai dai akwai sauti me shiga jiki, wanda tunda ya fara karatu dakin yayi wani irin dumm. Yanayin ba dad'i da wannan Allah ya taimaka Maina ya farka, yana tashi Layla ya fara nima, ya kalleta cikin wani irin yanayi bai san lokacin da ya ji kwalla ya cika mishi idanun, ya koma kusa da ita ya zauna yana sunkuyar da kai. A hankali ya d'ago kai yana shanye kwallar, "Yarima Muhammad ko zaka tafi kayi alola ka zo ayi da kai!" Ban dakin Malik ya shiga yayi alola ya dawo, yana tafiya kamar zai zube shi ya manta rabonshi da abinci a cikinsa ma, ana ta Kai wake ta kaya. Haka ya zauna shima yana karatun har fiye da awa uku, suka tafi sallah suka dawo amma Layla ko gizau.. *MadinatulRuhl* A gaban sarki Farwala dibdiddaya take kanta a sunkuye. "Kalya nasan tunda kika zo nan domin kanki ba zuwan kanki ba ne, kalya da kafarki kika bar daularmu yau me ya dawo da ke?" Kanta a sunkuye ta ce. "Abbana tabbas ni ce nace ba zan tab'a dawowa gare ka ba, Abba yau gani idan zuwana zai saka yafe min gani nan nazo gare ka." Girgiza kai yayi ya ce mata. "Dama can na yafe miki, amma kafin nan nasan wacece ke me ya kawo ki!" D'ago kai tayi tana me fa in. "Kasancewar kana cikin wadanda suka samar da geheena, ina rokonka alfarman a duba jikin sundukin da Layla ta aiko da shi akwai digon jininta, ita din zuria ce ga wagaduwada!" Nunata yayi da yatsa take hayaki da karfen wuta ya nad'e ta. "Imma bil adam imma Jinnu ko Rauhani babu wanda ya isa ya saka ni zuwa ga geheena domin ita ce kurkukun rauhanai don haka kafin raina ya b'aci maza b'ace min!" "Abba ko kashe ni zaka yi ba zan tab'a tafiya ba. Da na koma babu Layla gara ka giciye haka zai saka min samun salama! Domin yarinya ce da ta taso cikin maraicin uwa, kamar ni nan da narasa Uwata na zama marainiya karfi da yaji domin Uban da nake da shi bai zame min uba ba." "Kalya!" Ya daka mata tsawa. "Eh ka zame min uba ne?" "Dakaru ku fita da ita." Janta waje wasu maradan matasan aljanu suka yi suka watsar da ita waje. Cikin wani irin ihu ta, taso da gudu ta nufi kofar masarautar tana duka da dukkan karfinta. Amma ina kasancewar da muduwar bakin karfe aka narkan kofar, duk abin da tayi Babu wanda yasan tana yi ma. Komawa tayi da baya ta falfala gudu ta rike zuwa guguwa take sai gashi ta rufe katangar masarautar wanda aka gina shi shekaru kusan dubu ashirin. Duk kokarin dakarun domin riketa amma ina ta isa har kofar fadar. Ta zube akan gwiwarta tare da cewa. "Mai martaba ba zan koma Baihak ba sai dai a sare kaina, Domin Layla amana ce Zafir da Jamima suka bani, bayan sun shayar da ni kwarya goma na jinin zaki!" Ta fada tana kuka me ban tausayi, wannan maganar shi tayi ta fada har kusan shudewan awa daya bata fasa fadar kalaman ba. "Ya Shugabana, ka jima kana nazarin yadda Kalya zata dawo daga duniyar bil adama anya ba zaka amshi bukatar ta ba!" "Kul Zikwan ba zan amshi tubanta ba, sai ta shafe kwana arba'in tana rokona idan har ta rike wannan alkawarin don an bata jinin zaki tow zuwa nan da gobe zata sare kafin sati zata koma inda ta fito idan kuma ta haura sati biyu tow ba iya alkawari ba ne akwai yarda Amana!" "Na fahimci zancenka! Amma a sassauta mata " murmushi yayi ya ce mishi"Zikwan ita aya ce ka ai ta gaji kyawawan halaye da nagarta sannan ta kasance me shiga rayuwar bil adam, bayan ita tow duk sauran bana jin idan na shude wani zai gaji mulkina shi yasa tun a daren da aka haife ta na sadaukar da Mahaifiyarta domin kada ta taso da zafin kishi da halayen uwarta." "Tabbas haka ne, amma gaskiya ya kamata zuwa yanzu ta dawo gida!" "Nima fatana kenan! Amma domin na ga gazawarta zan saka a sake mata ukuba da bala'i da fitina yadda zata gudu da kanta idan tayi haka tow bana fatan tsinuna ya shafeta." "Shugabana ita ce karama cikin Yaranka, baki aya shekarun ta bai wuce dari biyar ba, yarinya ce sosai ai wannan azabar zata mata yawa!" ( shekaru 500Years ace mata baby ) shafa gemonshi yayi yana murmushi ya domin yasan duk cikin yaranshi ita ce karamar kan da gaske ya ce. "Ai Kalya yarinya ce shi yasa nake tausayinta amma wannan lamarin da ta dauko zai saka na iya rasa rayuwata, ba tsoron narasa rayuwata nake ba, ina tsoron kada haka yasa al'umma su ji zafinta ne, ko yayya aka cutar da ita ba zan ji dadi ba a rayuwata na can, don haka nake son gwada karfin zuciyarta sannan na auketa muje geheena." "Na fahimci zance yanzunka!"daga haka ya tawo aka bude kofar fadar yana fitowa ya ga yadda tayi barna. Girgiza kai tayi "yarinyar nan yaushe zaki daina rashin ji? Da fatan baki ji ciwo ba!" Ya fada yana isa inda take ta d'ago hannunta yana duba inda ta bangaji katangar. "Yarinyata ta girma!" "Abba ka yafe min zaka cire min digon jininta!" Juyawa yayi tare da barin wurin, "Abba ka taimaka min kada ta rasa rayuwarta na roke ka " yadda tayi ta ihu, yasa Matarshi Uwargida mai suna Sunbibi. Wata katuwa da ita kanta kamar na giwa, duk da shima Falwara shima kato ne kamar Giwa amma dogo ne kamar basamude. Amma kyan Kalya da alamu daga Mahaifiyarta ne, kiyayar Kalya ga mahaifinta ya samu asali ne daga lokacin da Sunbibi ta bata labarin ai duk soyayyar da Sarki yake mata saboda ya bada jinin mahaifiyarta ne. Haka yasa tayi yunkurin kashe sarki shi kuma ya ce ta fita ko ya tsine mata albarka abin tashin hankali shine matukar ya tsine mata zata zama abin gudu a cikin al'ummar rauhanai haka ta sha alwashin ba zata kara takowa gare shi, haka yasa shima ya lashi takobi ba zai tab'a kyaleta idan tazo mishi. Wannan abin yayiwa Sunbibi da Yaranta dadi, duk da yasan anyi haka ne domin a raba shi da yarshi amma ya saka a ransa ko zata dawo ba zai hana shi karbanta ba, domin tausayinta yake ji yarinyar da ta rasa Uwarta saboda ta rayu cikin aminci da salama ta koma kamar mara galihu. Duk kokarin Nuhu sai da ta kai ya gaji domin sallah kawai yake fitar dasu bayan sallah isha suka yanke zasu kwana a wurin bayan sun ci abinci ne aka daura daga inda aka tsaya anan ne jikinshi ya fara wani irin rawa, jini na zuba ta hancinsa a hankali ya rike kirjinshi. "Kai ya haka?" Sheikh Bin Musa alkandariya ya fada tare da mikewa ya rungume shi. D'ago idanunshi yayi da jini ya kwanta a cikinsa ya ce mishi. "Malam ba iya nan matsalar take ba, sako daga wani wurin yana isa gare " "aike?" "Eh malam!" Ya fada tare da rike wuyarshi shi wuyarshi wani irin girma yayi a hankali yayi ta yunkurin amai sai ga katon kwai ya fado daga bakinshi. Yana fadowa kuwa ya koma jikin Malam yana nishi. "Amir ko zaka amshe shi ne!" " Gaskiya yayi rauni!" Amir ta fada yana me tawowa. Rike hannun Amir yayi yana fa in. "A'a akwai kasada, domin ta rayu ana bukatar jinsi biyu ne mutum da rauhani, ka ga kenan ta ko ina ana bu atar wanda xai amshi kaddaranta ce." Murmushi Sheikh Bin Musa alkandariya yayi ya ce. "Idan kace sun janye ta daga duniyar mu zan amince, amma kace min kada mu bada rayuwarmu kasan haka ma ba zai yiwu ba." Sannan Amir ya amshi karatun Nuhu yana gefe, tunda ya fadi ana bukatar sadaukarwa yasa Maina ya shiga tashin hankali yana jin kamar ya zauce. Haka ya fita ya gaya musu halin da ake ciki. Wannan tashin hankali ya firgita kowa. Queen Hamidah da ta kasa zama a cikin masarautar gidan Tirsila ta nufa, tunda ta isa Tirsila take girka bala'i da masifa tana wurgawa Layla da take ganinta cikin wani bakin duhu, haka ba karamin dad'i yayi musu, "haka zata kasance bana son ta mutu ina son ta ji kamshin mutuwa har na tsawon kwanaki arba'in yadda ko ta farka da yatsa daya zan karasata." Ta fada tana murmushin mugunta. Tunda Maina ya fadi abin da yake faruwa, aka rasa me magana a cikinsu. Can dare suka watse, Har Maina da Malik ya saka shi gaba ya tafi ga iyalinsa. Auta ne ya fito tare da nufar bangaren Malik yana shiga ya samu su Sheikh suna ta abu aya. Zubewa yayi akan gwiwarshi ya ce mishi. "An samu Rauhanin da za tafi na shirya.... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/8, 3:57 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________73 Kura mishi idanun Sheikh Bin Musa alkandariya yayi na wani wasu dakika kafin ya sauke numfashi ya ce mishi. "Kana tsammanin zan yarda ayi sadaukarwa ne,ayar Allah ya isa bama bukatar wani abu." "Sayyid ka fahimci abinda nake nufi." "Na jima da sanin haka! Tana da mahaifi sannan ga Mijinta waye kai a gareta? Kai ba kowa ba ne facce dan uwan Mijinta don haka na sallame ka!" Ba tare da sanin Maina yana bakin kofar ba, suke maganar abin ya bashi mamaki da yadda Auta zai bada rayuwarshi saboda Layla. Wacce irin so Auta yakewa Layla haka? Komawa yayi ya boya yana jin kamar ya fashe da kuka. Yana tsaye a inda ya boya Auta yazo ya wuce shi, bai sake ya fito ba sai da ya daina jin takun auta sannan ya fito daga maboyanshi. Ya nufi dakin ya zauna yana kallon Layla da ake ta mata karatu. Bai sake yayi maganar abin da ya ji ba, amma tabbas yaji a ranshi ba zai yarda Auta ya mishi riga malam masallaci ba, kai ko mutuwa yayi baya fatan Auta ya auri Layla balle har haka ya faru. Har asuba yayi suka
Chapter 105 · 0% Book details