← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 115

Sashe 87

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana murmushi. Wani murmushi Layla tayi tare da cewa. "Laaaa Ifraz!" Da wani murya me shegen dadi da kuwa. Cak Maina ya tsaya tare da juyawa ai kuwa ta d'age gown dinta zata zuba da gudu, shi kanshi bai san ya falfala a guje ba, ya rikota. "Kina da hankali kuwa?" "Sultan kwaya nawa ake son hankali mutum ya mallaka? Zara zaran yatsunta ta cire ta fara mishi lissafi, tuni ya manta da Aliyyah ya riko hannunta. "Ni wallahi sai na je wurin Ifraz " suka yi ta drama, zuwan su Ammar da Salahudeen yasa shi sassauta riketa. "Muje!" "Wurin Ifraz?" "Ke mahaukaciyar ina ce?" "Ni ai mahaukaciyarka ce!" Ta fada tana washe hakori. Haka suka bar Aliyyah a wurin, wani irin sanyi jikin Layla yayi ta ce mishi. "Mum ba ta kira ka ba." "Oho haka ne! Muje tare!" Wai gudun kada ta tafi wurin Ifraz don ya lura Layla mahaukaciyar gaske ce, a bakin kofar parlour ta tsaya. Tana jin muryan Aliyyah tana kuka da cewa tunda ya koma wurin Layla ya tafi, dama ashe yayi musu kayan iri guda. Kai masifa da bala'i, kafin ta ce mishi. "Kada ka manta baki da yace baya sonka har abada bayan kaunarka." Haka ya ara tab'a shi koda suka fito ya sauya kaya, amma abin mamaki bai ga Layla ba, sai nimanta yake har bangaren Ummimi yana zuwa ya samu kayan da yake jikinta ta sauya izuwa irin nashi. "Ke a ina kika samu kayan nan!" "Ba kai ka turo Mum da kayan ba? Kace ta bani nawa!" Shiru yayi tabbas ya bawa Aliyyah ta ajiye tunda Layla bata da lafiya. Ashe ta kawo mata kuma ba haka ba ne. Garin ha a sharrinta take gayawa Matar Salahudeen da Ammar don sune kawayenta, anan Jasy ta ji don haka kamar an matse bakinta ta gayawa Layla tun jiya da yamma, ita kuma Layla ta saka Kalya ta juya siffar Aliyyah ta kawo mata akan idanun kowa. Murmushi tayi ta ce mishi "saka min abin wuya na!" Wanda Ummimi ta bata ne, ta saka ba karamin kyau tayi ba, don kada su fita da wuri tayi ta jan shi da rigima har ta gama. Koda suka fito su Aliyyah sun yi nisa. Hannunsu rike da juna suke tafiya. Duk wanda ya kwana da sanin tarihin Baihak yasan babu irin wannan romance din, amma abin mamaki shine ganin Maina a gaban jama'a yana rike da hannun Matarshi. Kafin a je wurin dabar sai da suka tsaya Babban hall. Anan Layla ta haska kowa. Duk wanda ya ganta sai ta burge shi, manyan mutane da sarakuna dayawa fatan ina ma da ansu maza suka same ta. Haka ya gabatar da ita, wani irin yanayi taji ya matsa daga wurin ta koma sama tana kallon yadda Aliyyah ta koma jikinshi. Idanun Queen Hamidah akan Aliyyah. Har aka gama da a fita Maina ya fara niman Layla a can ya ganta tsaye gaban wani mutum. Tana bashi labari da sauri ya wuce hanya ya haura saman koda ya isa ya samu Layla ita aya tana murmushi. Kamar zai fasa ihu ganin ita aya ne. "Ina dan iskan yake!" Dariya tayi tana gyara mishi riga. Cak ya auketa don gani yake idan ba haka ba zata iya hango dan iskan. Har filin daba. A can kuwa Aliyyah ce da Queen Hamidah. "Hmm! Ke wani irin shishigewa Maina kike yi ne?" Shiru tayi kafin ta cewa Queen Hamidah. "Tow meye laifina da yake nuna yafi son Layla akaina? Kome Layla kome Layla kowa Layla don na haifi Yara mata sai na zama shara?'" Murmushi Queen Hamidah tayi tana fa in. "Indai wannan ne xan samo miki yadda zaki koma gare shi, yanzu ina son ki min wani alfarma ki lura idan Layla tana da ciki ki gaya min!" Cikin wani irin zafin kishi ta ce a ranta. _So ake shima cikin tun kafin yazo a fara banbanta mu!_ "tow xan gaya miki!" Ita a tunanin za ayiwaa Layla wani abin arziki ne yasa taki fada. "Ki tabbatar kin gaya min! Zan baki babban kyauta wanda Maina ba zai manta da ke ba!" Gyada kai tayi bakinta ta bu e zata yi magana sai ga Maina da Layla......! ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` In sha Allah zan yi kokarin na dinga baku page 2 a rana domin mu kammala akan lokaci [9/18, 4:32 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu __________56 Kamar wacce aka ingiza bakinta idanunta yana kan Maina da Layla. "Tana da ciki, kiyi hakuri!" Ta fada a kufule, domin ranta ya gama b'aci. "Allah miki albarka, zaki ga sakamako mai kyau." Daga haka ta cigaba da tsayuwa har suka iso wurin. "Amarya!" "Na'am Queen Hamidah!" Ya fada tana kokarin sauka daga daukar da yayi mata. "Sultan muje na raka ka, ka hau doki." "Ba shi da kafa ko shi makaho ne?" Inji Queen Hamidah, "Ba mamaki haka wasu suke bukata, amma a gare ni bana fatan ya rasa ko daya domin ba zan lamunci haka ba!" Dafa Maina tayi tana murmushi, "Macen da ta ce bata sonka." Juyawa Layla tayi tana fa in. "Ai duk cikin kauna ne waye zai ga zankadedden saurayi irin Sultan Muhammad Hatim ya ce baya so, ni dai ya cika min kome bana bukatar ari." Inji Layla tana murmushi. Shi kuwa Maina jin kalamanta yasa kanshi ya wani zama kato, sannan ta kara sussuta shi da da cewa Saurayi zankadedden. Gyada kai yake kamar kadangaren gobara. "Muje Babyna ka hau doki ina son magana da su dukka!" Haka ta raka shi, har inda zai hau dokin. Tana zuwa ya sama bayan dokin ta zuba mishi mari take ya zube a kasa yana nishi. Shigowa da wani doki aka yi, "Me yasa?" "Wannan ai ba lafiya ce da shi ba, wannan kuma ita ce mai lafiya!" Ta nufi jikin dokin tana shafawa tana murmushi. "Idan wani abu ya samu Yarima na, zan dau mataki." Girgiza jiki dokin yayi. "Sultan ka hau." Haka ya hau ta rike shi tana murmushi. "Kariya da tsaron Allah suna tare da kai, mutane na suna gefe da gefenka! Amma ka sani rigimar bata kare ba, tunda ka min hukunci akan laifin da ban aikata ba ma rantse ba zan yafe ba." Ta fada tana murmushi. "Na fasa fitar!" "Ai kuma bakin alkalami ya bushe, maza asassss!" Ta kora dokin tana murmushi juyawa wurinsu Aliyyah tayi tana fa in. "Kun gaji da jira ko?" Ta isa gabansu. "Wai uban waye ya baki kayan nan kike sakawa?" D'aga kafadarta tayi tana fa in. "Waye ya gaya miki ina niman izinin wani uban ne? Kayana ne da kika rike kuma kika kawo min ki tambaya ki ji da kyau!" "Queen Hamidah kin ga abin da suke min!" Kallon kurilla Queen Hamidah tai Layka kafin ta ce. "Waye ya tsaya miki?" "Mijina!" Ya fada tana murmushi tare da maida kanta wawuya. "Mijinki?" Queen Hamidah ta kuma tambayarta. "Eh shi mana, kuma ai ya gaya min cewa kowa ya tambaye ni nace shi ne! Domin shi zimmar gari ne." "Me yasa kike son raba su!" Ta kalli Aliyyah, "Ni kuma? Ni me zai saka na raba auren da ya shekara dari, ai sai dai ita ce bata son zaman lafiya, amma ni ai me mata biyayya ce." Kallon Aliyyah Queen Hamidah tayi tana . "Kika ce tana miki rashin arziki." Kafin Aliyyah tayi magana Layla ta fashe da kuka. Har da durkusawa. "Mum ki yafe min idan nayi mijina daidai ba, indai akan Papa ne na yafe miki daga nan har ranar mutuwata bana son na kara ganinshi xan tafi garin mu na cigaba da zama. Queen Hamidah ki saka baki na yafe mata mijin idan ya dawo ku saka shi ya sake ni kun ji" "Kul ki sake cewa ya sake ki, ba a saki a masarautar nan. Akwai abin da nake son ku sani tashi tsaye!" Ta fada tana me tafiya suna bin bayanta, kallon Layla Aliyyah take cikin mamaki yarinyar nan zata iya kashe mutum. "Aliyyah a matsayinki na Babba ya dace ki ja Layla a jiki da alamu kina masifar kishinta gashi ita bata iya zazzafa kalamai akanki don haka daga yau kada na kara jin wani ya ha'inci wani sannan. Ga yarinyar da nake so zan hada ta da Maina." Ya nuna musu Sanayah da ta ci Uban kwalliya. Gaban Aliyyah ne ya fadi tana kallon Sanayah,.kafin ta juya tana kallon Layla domin yanayinsu kusan daya ne. "Laaa kai amma matar Sultan kyakkyawar gaske ce, Queen me kike so muyi mata domin ni dai nayi mubaya'a." Aliyyah da abin bai mata ba hade rai tayi tana fa in. "Shi haka tabbata da aure-aure?" "Eh bayan ya aurota zai hada har da kwarakwara." "Godiya Sultan yake Queen!" Duk da cewa Layla tasan ko mutuwa tayi Sanaya ba zata tab'a auren Maina ba, don haka tafi kowa murnan haka. Wurin zama suka nufa , har Sanaya ta iso suka kalli juna da Layla. Kafin suka gaisa koda Sanayah ta gaida Aliyyah banza da ita tayi, ita kuwa Layla jefi-jefi tana jan Sanaya da hira, guguwa ce me karfin gaske ta taso sosai a filin sukuwar, kurawa juna idanu Sanaya da Layla suka yi. Guguwar tana tashi tayi kan Maina ta nad'e shi da sojinsa. Ihu Aliyyah tayi tana kiran sunan Maina, yayinda Layla ta dauki goran ruwa ta fara sha a hankalin. Tana murmushi mikewa Queen Hamidah tayi ta nufi bayan Aliyyah da take ihu. "Me yasa ba zaki gaya musu babu abinda zai same shi?" "Ki gaya musu cewa ni matsafiya ce?" Layla ta wurga mata amsar. "Layla me yasa kika tsane ni!" Buga table din tayi tana huci. "Idan akwai wanda na tsana a iyakar rayuwata ke da kakarki!" "Amma Layla ni meye laifina?" "Naji ance zaki auri Maina ko? Ki shirya kishi ko ya i ." Wani irin abu Sanaya ta ji a hankali ta ce. "Har abada ba zan tab'a hada miji dake ba, sannan ina nan shirye na bada rayuwata dominki!" Mikewa Layla tayi tana motsa bakinta a hankali, guguwar ta lafa sai ga Maina lafiyarshi lau. "Na san kece kika bashi
Chapter 87 · 0% Book details