← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 115

Sashe 55

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yasa ta fahimci yau Maina ya sauya. Wannan daren yana cikin daren alkhairi a rayuwar aurensu, alhamdulillahi kawai take fada aranta. Ba dadi kan mijinka ya fifita wata mace sama da kai. Washi gari Sainah da Layla suka shirya Aliyah na ganinta ta hade rai. "Ina kwana ranki ya da e!" Banza tayi mata sai da ya ajiye kofin shayin. "Baby baki ji bane?" "Oho lafiya!" Ta fada tana dauke kai. Ta wuce can. Knocking aka yi ya ce. "Yes!" Ammar ne tare da Prince Auta, "ina logging inta?" Kallon Layla Maina yayi sannan ya ce mata. "Kayanki!" Komawa dakin tayi jikinta har yana rawa, kallonshi Aliyyah tayi tana son magana amma yaki bata fuska. Juyawa tayi ga Ammar "Daddyn Riyyah ya su kawata suke?" "Tana lafiya!" Ta matsa tare da ja mishi kujera ya zauna, yana kallon Maina da ya fahimci kome yana tafiya dai-dai. Tea ta zuba mishi ya fara sha. Kafin Layla ta fito da kayanta, sau daya ya dauke kai bai kuma kallonta ba, haka suka fita tare da Auta, "Didina!" Nuri darling ta fa a tana ihu, amma haka ta bar gidan. Daukar Nuriyya yayi ya sakata a kafadarshi, "Fafa don Allah ta dawo!" Murmushi yayi ya ce mata. "zata dawo!" Sainah da idanunta yake cike da kwalla ta ce mishi. "But why Papa? Layla tana da kirki Layla ta bada rayuwarta domin mu and now ta." "Ke!" "Aliyyah ta buga mata tsawa. Komawa akinsu tayi ta rufe kofarta. "Madam sha'anin yara sai da hakuri, musamman idan suka samu sa'arsu!" "Layla ba sa'arsu ba ce, yarinyar da ta balaga no need ta cigaba da zama domin ina gyara tarbiyyar Yarana tana rusa min ne." Maina bai ce musu kala ba har har suka gama suka nufi office. "Yanxu ina ka sa ya kaita?" Hankalinshi yana kan hanya ya ce mishi. "Zai wuce da ita airport zai bata kome Hukumar makarantarsu zasu zo su d'auketa." "Maina ka bi Aliyyah a hankali please kada abin da take yi ya dame ka, wallahi tayi kokari fa ace a kawo yarinyar da zata." "Ba zaka fahimci me yasa ba, Ni nake renon yarana tsakanin Aliyah da yara ta haifa min su ni ne akan hidimarsu saboda ina son su shaku da ni bana son yadda na rasa soyayyar Mahaifi Yarana su rasa nawa, yarinyar na da kuke ganin laifinta." Shiru yayi yana kallon hanya. "Kai bana son bura Uba ina zaka kai mu?" Daidai lokacin da yayi parking a airport in, fita yayi ya dauki abin da zai dauka sannan ya bar Ammar a wurin. Ganin haka ba zai mishi ba ya fito yana d'aga murya yana auna mishi shirgegen Ash'aria. Lokacin da suka isa tana tsaye ita da Auta sai share hawayen da yake bi mata take, juyawa tayi tana kallon Maina domin tun daga shigarwashi taji al'amun ana kallonta, sunkuyar da kai tayi tana kallon kasa. Dafa kafadarshi Ammar yayi ya ce mishi. "Dan kutumar uba, kwaila ce naga kirjinta daya da kadangariya!" Ture hannunsa yayi tare da nufar inda take, ya mikawa Auta kome da komenta. "Hukumar makarantarku zata zo daukarki and kiyi karatu babu wasa ban da kawaye kuma banda wasa da maza!" Ya fa a yana muzurai kamar zai cinye ta. Kanta tayi kasa da shi hawaye na zuba mata. "Papa!" Yadda ta kira sunanshi sai da tsigar jikinshi ya mike. Ya zuba mata oil eyes inshi, masu digon zaiba ya ce mata. "Hmmm you !" Girgiza kai tai sannan ta cire abu aljhunta ta mika mishi. "A sakawa Nuri darling ahannunta!" Sannan ta koma kan kujera tana shashekar kuka. "Papa please kada ka bari ta hadu da Malik!" Yada tayi maganar ya kara tabbatar mishi ba iya matsalar Aljnu ne da ita ba a'a akwai abin da take tsaye a kan family dinsa, haka aka fara cewa pasinjojin US su fara shiri ya riko hannunta ya wuce da ita har inda zasu shiga jirgin, ya kaita wurin sit dinta ta zauna ya daura mata belt sannan ya zuba mata idanu. Yana kallon yadda fuskarta yayi jajjur. "You need something?" Girgiza tayi kafin ta ce. "Duk inda nake samun farinciki sai na rasa, da farko ban san wacce ni ba, na taso cikin soyayyarta, na rasata yau na samu soyayyar gaskiya a wurin Nuriyya itama na rasata!" Yadda take kuka yasa shi ciro hanky ya mika mata. "Idan kika daina kuka zan kawota idan baki daina kuka ba, ba zaki kara ganinmu ba" cak kukan ya tsaya mata ta ce. "Na daina kukan!" Cire sweater coat dinsa yayi ya rab'a mata akan kafarta. "Zasu baki dressing na irin namu, kada na kara ganinki da wannan bingilelen skirt din kin ji ko!" Ya fa a yana zare idanunshi. "Tow!" Sannan ya juya har ya isa bakin kofar ya ce mata. "Ban da kuka kina jina." Gyada masa kai tayi, ya fita tana wurin har aka tashi suka bar kasar, suna airport in, kallonshi Auta yayi ya ce mishi. "Zan je wurin hajja wani watan naje ta bani Yarta nan!" Tsuke baki Maina yayi Ammar yana kallon su har suka bar airport in. A can gidan kuwa waya Aliyya take da Jasy take gaya mata abin da tayi, shiru Jasy tayi sannan ta ce mata.."har Ayrah ce zata dauraki a kan keken bera ki hau?kin bani mamaki ko aure Maina yq ce zai yi idan nice ba zan damu ba, balle kinsan irin crisis din da ake a familynshi domin ya haifi Namiji, wai ke meye matsalarki da Layla ne?" "Yarinyar ta cika kyau ne, kyanta yayi yawa!" "Kina tsammanin pushing Layla da kika yi away xai rabaki da da namiji ne? Kinga ko bai yi aure ba zai kawo miki Concubine wacce zata haifa mishi namiji, kuma wallahi daga ranar ta haifi namiji bar ganin yana son Yaranki dole zai juya baya na wani lokaci, kai ko aure yace zai yi in nice zan ce masa ga Layla ita ce Yaranki suke so suka shaku dasu." "Amma ai Sanah bata sonta ni gaskiya ba zan yarda ya auro min ita ba, yarinyar da a haife ya haifeta kut never " "Ok amma kin ce shi kenan, Allah ya bamu lafiya!" "Amin!" Suka katse wyaar kowa ranshi babu dad'i,. tun wannan lokacin Maina ya sauya har suka bar garin bai tab'a kai su sunga Ayrah ba wacce aka cire mata d'a namiji babu lafiya, Iyayenta sun zo daga nan suka juya Baihak. Tana zuwa ta samu labarin Suhana, wannan abin ya mata ciwo gashi babu wanda ya gaya mata inda Maina suke da iyalinsa. Tayi kuka a boye tayi kuka a sarari tayi nadamar amincewa ta zama concubines din Malik, ga Maina da yake kula da ita. Haka ta cigaba da samun kulawa bayan sati uku aka sheka suna irin ta alfarma da alfahari, babu inda ba saka bikin sunan ba, Ig, TikTok, Facebook, YouTube har Snapchat an daura sunan Prince Jawad AbdulMutallab Hatim 6th Prince, wannan abin yayiwa Ayrah dadi d'anta yana cikin masu jiran gado. Layla kuwa hukumar school din suka zo aka d'auketa zuwa makarantar, tun anan ta fahimci makarantar yana cikin manyan makarantar yaran masu kudi na musamman a kasar, a akinsu su uku ne. Dukkansu fararen fata ne, daya yar kasar habasha ce amma babanta ba Amurike ne, daya kuma yar kasar Pakistan ce uwarta hindu ce, va laifi sun karbeta da karamci sannan suka bata lokacinsu, tana shiryawa suka fita, yan team dinsu. "Sunana Radiyyah Aswad Babana dan Pakistan mamana yar kasar nan ne," "sunana Ashley Joe Babana dan nan ne Mamana yar Ethiopia ce, wancan Tina William, Wannan kuma Deenah Mujahid Jikas! Babanta yana nan us." Idanunta ne ya tsaya akan Deenah ta mika mata hannu. "Layla Muhammad Hatim!" Ta fa a tana sunkuyar da kai. "Feel free, dukkanmu nan kawaye ne babu ruwan mu da rigima da tashin hankali. " "Radiyyah Aswad dole Layla ta dawo room B." Inji Deenah Mujahid Jikas, "D'auketa mana banda iskanci kin dauke mana tina ban damu ba yanzu ki dauke mana Layla." "Shi kenan!" Ta fada a marairaice. "Sai ki tafi dakinsu!" Ai kuwa suka fara ihu, zata iya cewa wannan shine karo na uku da ta kuma samun kyakkyawan alaka da wasu. Haka suka cigaba da zama, tare kuma suna nuna mata abinda bata gane ba. Musamman Deenah ta ja Layla a jiki, kasancewar Uwarta baturiya ne kuma Ubanta dan Najeriya ne daga Jahar Gombe. Kuma abin burgewa Yarinyar bata da girman. Kai kamar ba yar Babban gida ba. Sai ga Layla ta mike kafa tana ta walwala da farinciki. Kowannensu a yaran yana da abin da yake so, kamar Deenah pioneer take koya, Radiyyah kuma wasan ninkaya na ruwa take koya, Ashley kuwa tana class din da ake koyar da Ballerina. Tina William, kuma tana hidimar .... [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu *Wannan shafin na kune Pretty, Mom Sayyid, Ammin Soha, Ummu Muhammad, Maman Hajiya hmm! Dubun godiya da fatan alkhairi ana fafatawa ko _____________________30 Dream! Tafiya yake a tare da yasan inda yake jefa kafarshi ba, domin babu wani yalwataccen haske. Tuntube yayi da abu kamar an jingiza shi ya fa a cikin ruwa, mika mishi hannu tayi. "Fito!" Ta fa a tana mika mishi hannu, kin riko hannunta yayi ya kama abu zai fito yaji an rike kafarshi, sake yunkuri yayi amma yaji an rike kafarshi sosai. "ba ni hannunka!" Ta kuma fa a a karo na biyu. Gani yayi kamar zai iya fita domin a yadda yake ganinta ba zata iya fitar da shi ba, ji yayi an ja shi can asar ruwan tayi maza tana me rike hannunshi dakyar ta janyo shi. Yana fitowa tayi tafiyarta ya nime ta sama da kasa, hango kofa yayi da haske ya nufi wurin yana bude kofar zare idanu yayi wanda yayi daidai da bu e idanunshi. Sakamakon karar alarm da ya saka karfe uku saura. Tashi yayi zaune yana kallon inda ya kwana, ba a dakinshi ya kwanta ba tunda ya shigo dakinsu Sainah yayi musu Addu'a, Nuri darling tana kananun rikici ya kwanta a kusa da ita. Tun da suka dawo Washington DC, ya lura da jikinta yana yawan rikice mata, don ma ya
Chapter 55 · 0% Book details