Sashe 20
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* ___________________ Ita kanta Aliyyah tasan ishirwa yake kashewa, amma batun kauna babu shi a duniyar shi, ita abin da ta fahimta idan aka cire hakkin aure ita bata cire maganar aure tow bata tunanin akwai wani abu da yake da shi da ita, hiran shi da yaransa ne shi ba mutum ne me yawan kwaranniya ba, asalima ko da Ammar yake magana zai yi wahala aji muryan shi, domin kamar munafiki haka yake kome na shi sanyi sanyi, sai iya gasa mutum da ruwan sanyi, ga shi wannan dabi'ar har ta rab'eta. Ko da ace yaransu suna gida zai yi wahala kaji suna ihu ko hayaniya, kamar yadda yake haka ya sakawa Yaranshi tarbiya. Sannan duk wanda suke tare dasu, daga Nanny Amrah zuwa Kuku da drive kowa a nutse suke, haka yasa ko a makaranta ne su din daban ne, domin kowa yasan sun fito daga gida me girma da daraja, ko Prince Haisam haka yake, zama da Maina ya koya mishi wani irin nutsuwa, koda yake nono daya suka sha dole su zama masu nutsuwa da kamala. Washigari babu makaranta saboda ranar yara da ake yi, yana shirin office Aliyyah tana kwance. Kallonshi tayi cikin sanyin murya ta ce mishi. "Prince!" Ta madubin dakin ya d'ago kai ya kalleta. "Hm!" "Ina son ko za a kara mana masu hidima ne?" "Akan me?" Tashi tayi zaune, tana tattara gashin kanta. "Wacce zata na kula da Nur!" "Amra fA?" Sosa kanta tayi ta ce mishi. "Mun yi chat da Bahi tace za a mata aure ne." Ta fa a tana mikewa ta nufe shi, tana gyara mishi zaman links din rigarshi. Sai yanzu ya tuna Haisam ya gaya mishi za ayiwa yarinyar aure. "Waye zata aura?" "Wani ne a can Baihak." "Shi kenan! Kuyi magana da Bahi!" "Tow!" Saka jacket din suit din yayi ya bar gidan, bayan ya shiga dakin yaran ya sumbaci goshinsu. Wanka tayi agurguje ta fito daga dakin, ta umarci Amra ta gyara dakin kwanansu, sannan ta wuce dakinta. Wayarta ta dauko cikin kaguwa, takira Bahi sun jima suna magana kafin suka yi sallama. Tare da mata alkawarin an samu bayi an mata za a tura musu. Sannan ta gaya mata ban da me rawan kai, ban da kyakkyawar budurwa a nimo mummuna da sau daya zai kalleta. Sai dai yadda akewa yan mata dauki dai-dai a cikin Masarautar yaja iyayen hakura da barin yan matansu, suka shiga fita daga masarautar ta ashin asa. Wani kofa ne can ashin asa. ..... Sai da ya gama taron, sannan ya dauki wayar domin yaga kiran Dr Abbas. "Hm!" "Sir matar nan, ta farfa o amma bata gane kome tsawon shekaru nan da take coma." "Alhamdulillahi, ina da ba i zan kiraka an jima!" Ya fa a a sanyayye, yana jin tausayinta tsawon shekaru nan ace sai an maka kome, duk wanda bai godewa Allah ba zai godewa azabar Allah. Komawa yayi suka gama abin da zasu yi sannan ya koma office din shi, daga nan ya kira Abbas sun jima a wya suna magana shi tsakaninsu eh to hm, daga nan maganar kamar me tsoron yayi wata furuci a kama shi, dafe kanshi yayi kafin ya ce . "Alright xan yiwa Ammar magana, thank you." Ya kashe wayar. Turawa Ammar sako yayi, ai kuwa sai ga kiran fir yaki dauka, can Ammar yaji haushi ya turo mishi sakon manya-manyan Asharia. Murmushi yayi tare da share sakon kamar bai gani ba, Haka alamura suka cigaba da tafiya, cikin ikon Allah ya dauke kanshi daga abubuwan da Malik da Baihak suke, kamar bai san suna nan ba, ana haka Bahi ta tawo wurin shi cikin kuka da takaici, tunda ta zauna tana labarta mishi rashin mutunci da malik da Kakarsu da Ayrah sukewa Ummimi, ya dauke kai kamar bai damu ba, amma cikin zuciyarshi zafi yake. So yake ya jijjiga Malik da Mamarsa, don ya fara gajiya da abin da yake mata, kuma ance dan kuka, shi ya zama dan kuka kenan tunda gashi saboda da shi Ummimi take fuskarta wulakanci. Bai ce musu kome ba, sai dai a zaman shi na nan, shima ya samu kwararrun marasa kirki da suka shiga har fadar suka dauke Queen Hamidah, ba fada ba zagi babu sako babu wani gargadi. Suka d'auketa for the only 48hrs hankalin al'umma ya tashi, kuma ya tashi na fada ma, idan ka ga Malik sai ka rantse da Allah babu mutuwa domin ya birkice ya tashi hankalin kowa. Kiraye-kirayen waya yake can aka miki mishi waya, kallon security din yayi kafin ya amsa yana son tambayarshi waye akan Layi amma halin da yake ciki babu dama. Amsa yayi ya saka a kunne. "Assalamu alaikum, Malik ka kwantar da hankalinka, ga Queen a tare da mutane na. Duk da bana nan idanuna da ke lissafina suna kan Mahaifiyata, ka rage takurawa Ummimi domin ga ban san me zuciyata zata aikata ba. Uwa ba wasa ba ce, wannan shine kashedina da ita Queen Hamidah fitinarta ya tsaya a kaina da sauranmu amma ban da Ummimi. Tana waje a d'auketa, wannan shine karo na biyu da muka yi haka a kula" Shiru tayi ya kashe wayar, zuciyarshi tana tukiki wato shi har ya haifi dan da zai mishi wannan diban albarka, sai dai me yasa Maina yake mishi haka ne? Me yasa Maina yayi bala'in rena shi ne. Mika wayar yayi ca fusace ya ce ku duba tana can kofar fada. Ana futa kuwa aka same ta cikin buhu, wannan abin ya mishi ciwo Uwarshi Maina zai wulakanta, falon Khamilah ya nufa, tana zaune cikin damuwa domin tunda court lady ta gaya mata an sace Queen Hamidah hankalinta yake tashe taje wurin Malik aka ce yana fada, kuma ya haramtawa kowacce mace zuwa fada. Yana shiga babu sallama balle iso ya tsaya a kanta. "Tsakaninki da Allah Maina jini na ne?" Wannan maganar yazo mata bazata, Mikewa tayi tana kallon shi a rikice, "My King wannan maganar tayi muni ta fito daga bakinka." "Eh shi yasa na tambaye ki, jini na ne? Taya jini na zai aikata haka? Uwata yasa aka dauka saboda ke." Zubewa tayi akan kafarta. "Na cancanci a yanke min hukuncin kisa ma, ka gafarce mu daga ni har Maina." "Zan bada Umarni duk inda aka ga Maina a kashe min shi." Dafe kirjinta tayi numfashinta yana barazanar daukewa, ta zube a gabanshi tana bashi hakuri da dukkan zuciyarta. Tana yi jini na d'igowa ta hancinta. Haka ya juya ya bar bangarenta domin idan ya cigaba da ganinta zuciyarshi zata karaya, yana fita Court lady tazo ta d'ago, ta zube a jikinta yana nishi. "Maina baya ji, Jakadiya sauran basu daura min ciwon zuciya ba, Maina zai daura min ciwon zuciya." "Kiyi hakuri shi bai don ya kuntatta miki ba, yayi ne don ya kawo karshen abin da ake miki." " Ai ba yau aka fara ba, kuma ba yau za a daina ba, don Allah ya daina." Queen Hamidah sai da ta kwashe sama da kwana uku tana kwance kafin ta dawo hayacinta, yasan Uwarshi da munmunar zuciya zata iya cutar da Maina ko wani na shi,don haka sai da ya samu ta nutsu tsawon sati biyu ta gaya mata abin da ya faru. She shock Maina ne yasa aka kidnapping inta? Baya kasar amma har ya tsara yayi kome, haka yasa ta zubawa Malik idanu tana murmushi. "Idan har yana son Uwarshi dole sai yarda da duk abinda kake so, kada ka sassauta mata, ka fara a gaban Uban kowa sai Maina ya dawo ya amshi auren macen da nake so." Tun daga wannan lokacin Ummimi ta shiga amsar maganin ciwon zuciya, domin Malik da Uwarshi sun sakata a gaba da fitina, tayi juyin duniyar nan Maina yazo infact ma kin bata amsa yayi, a haka aka samu shekaru biyu. A bangaren shirin kawar da abinda zai kawo karshen masarautar suna kan shiri sosai, haka yasa baki daya suke shirin kota kwana, domin sun ci alwashin ganin bayan wanda ya kawo musu cikas, ba zasu tab'a barin wannan abin ya wuce a haka ba. Wani lokaci addara aba ce da take zane cikin halittar Mutum, sannan al'amari ne da yake wanzajen lamari ne, haka rayuwa da mutuwa babu wanda yasan yaushe zai mutu yaushe zai rayu, har wani shekaru mutuwa zata zo mishi. Wannan lamari ne da tun fil azal yana rubuce. A cikin shekaru biyu da suka wuce, an ta samu matsala da Tirsila da Kaka Jami saboda Layla, rigimar da ta K unno Kai saboda kawai kudirinta, a ranar shagalin ranar mutuwar Uwargijiya da haihuwarta. A ranar ko waje Kaka Jami bata fita ba,domin yau rana ce da take ji kamar tayi bankwana da Layla sakamakon sakon da aia turo mata na lallai ta fitar da Layla daga garin Wagaduwada. Amma ta kasa domin son da takewa yarinyar bata jin zata iya nisa da ita, haka yasa ta kasa samun nutsuwa, tun da fadar rauhanan suka bata tabbacin kome zai faru, a shekarun rayuwar Layla take jin like zata iya sauya addaran Layla sai dai duk yadda taso abin ya ci tura,haka ta zubawa al'amarin. Ana can ana ta biki, amma Layla tana nan tare da Kakarta itama yau ji take kamar ba zata iya nisan kwana idan babu Kakarta, kuka take tana jin kamar idan ta matsa ba zasu sake haduwa ba kenan har abada. Mikewa kaka Jami tayi ta ja hannunta, ta nufi wani kofa da babu wanda ya san da shi, sai ita ta kira Haeda, fitowa tayi tana kallonsu. "Zo ku tafi kada ku juyo ku tafi, sannan ki kula da ita ga wannan." Ta zuba musu sulallar zinari, a aljuhunsu, na Layla daban na Haeda daban, tare ta turasu suka fita, cikin kofar da yake kad'awa da mugun guguwa. Suna fita wani irin kara me karfin tsiya tare da wuta ya tashi a gidan kaka Jami, ita kanta kaka sai da