← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 115

Sashe 48

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka ji ba dadi ga link nan _________________26 D'aga kai sama Sanaya tayi taga abin ya tawo ta ce. "Queen!" Tare da rungumarta suka fadi can abin y fadi can tare da tarwatsewa a gefe can,hankalin mutanen ya tashi. Aka yo kan Queen Hamidah da Sanaya, ran Layla ya b'aci amma sai ta danne fushinta tana kallonsu, Maina da Ammar suka sauka kasar cikin tashin hankali, dakyar Sanaya ta fito tana kallon wurin a hankali ta zubawa Layla idanu tabbas taji alamar magic spells, cikin mamaki take kara kallon Layla da itama kallon Sanaya take har ta sauko tare da b'acewa ta cikin mutane, Sanaya tayi ta bin ta a can waje ta hangota tana tafiya tare da juyi tana rawa. Kamar walkiya haka ta sha gaban Layla tare da cewa. "Layla kina raye dama?" Kallon gefe da gefe tayi ta ce mata. "Ni kike?" "Layla kin manta ni ne?" "Hala na manta da ke." Ta rab'a gefenta zata wuce ta riko ta. "Layla me kika aikata a can? Dama ke kike bibiyar lamarin Hamidah?" Wani irin juyi tayi tare da tsayawa a kan yatsun kafarta tana wani juyi kamar Ballerina. Sai da tayi rawa sosai sannan ta kalli Sanaya. "Kina tsammanin ban san ke ce kika turawa Hamidah kwaron tsafi ba." "Kina mamaki ne?" Inji Layla, ta cigaba da cewa. "Ban yi kome ba, ban gama kome ba ni na shigo Baihak ne domin na ruguza farincikin Malik da Uwarshi, yanzu ma waye ya san me yake faruwa a cikin hall din?" Ta fa a tana dariya. Rike hannunta Sanaya tayi. "Kiyi hakuri ki daina wannan fadar, ki yafe masu babu amfanin yakin da baka san farkonsa da karshensa ba." Ha e hannunta tayi tare da juya shi kamar wata macijiya tayi tana fa in. "Ba zan hakura ba, karshen wannan fadar mutuwa ce kuma rugus za ayi don haka babu ruwanki." "Taya kika shigo Baihak Layla?" Wani kallo tayi mata, tana hango Maina da Ammar da suke fito da Queen Hamidah da take fisge fisge, kamar tayi hauka. "Layla kiyi hakuri wannan fadar ba naki bane." "Kin tambaye ni taya na shigo Baihak? D'aga hannu tayi ta nuna mata Maina da suke rike da Hamidah. "Zan bawa Malik kyautar abin da ba zai manta da shi ba, sannan zan tabbatar da na kwace kome daga gare su sannan na aikata abin da nake so. Sannan zan bar su kema idan kika nemu dakatar dani akan Tirsila sai na kashe ki!" Juyawa tayi tana tafiya hawaye ne yake zuba a idanunta da sauri Sanaya ta sha gabanta. "Ba zan tab'a barin ki aikata abin da kike buri ba,zan tabbatar na dakatar dake kuma dan..". Ba ta kulata ba ta nufi angaren Ummimi da yake cike da yan biki, tun kafin ta isa ta ji ana ta hayaniya, dawowa dan barandar da zai kaika bangaren tayi ta tsaya tana hango Sanaya zata bar gidan, "Ba zan yafe miki ba, na kyale ki ne amma fansata gaskiya ce." Ta fa a tana cizon bakinta domin yau ba karamin bakinciki tayi na rashin nasarar da bata yi ba, haka ta cigaba da tsayuwa har wurin sha daya na dare tana tsaye, daga nesa ya hango ta domin yanzu suka fito bangaren Hamidah da ta samu barci, ya sha mamaki da ya ganta a tsaye a wurin. Kamar zai mata magana sai ya share har ya kusan gota inda yake ya tsaya tare da cewa. "Are you waiting for someone ne?" Juyawa tayi a hankali tana me sunkuyar da kai, kallon gashin kanta yayi da suke arin mikewa tsaye. Lokaci guda kayan jikinta ya koma jajjur ta d'ago kai tana kallonshi. "Papa!" Ta juya muryan Nuri darling, tana kallonshi. "Papa!" Zuba mata idanu yayi kafin ya kwashe da dariya, tana tafiya akan yatsar kafarta. Wani irin murda jikinta take kamar ba kasusuwa a jikinta, a hankali ta juya tana kallon shi ta fara arin hawa bango kamar su wata gizo-gizon ta fara hawa ri eta yayi ta wani fasa kara saida ilahirin kingdom din ya amsa. A fusace ta juya kanshi tare da kanainaye shi ya zama ta makale shi kamar zata shige jikinshi. "Haka Salahudeen yayi min, ga dauke ni to the secret chamber. We make most great moment!" Ta fada a daidai kunnenshi. Yakinceta yake son yi amma ta makale shi kamar zata shige mishi, ya rasa yadda zai cireta a jikinshi. Bai san yadda akayi ba daga shi har ita tsintar kansu suka yi a part dinsa ta dirko tana dariya, tare da lashe bakinta, juyawa yayi ya rufe kofar tare da jingina a jikin kofar, da gudu kamar walkiya ta tawo ya saka hannu daya ya tare kanta, domin ya fahimci aljanar jikinta so take ya illata shi, a hankali ya shiga tofa mata addu'a kafin yayi nisa ta kwace kanta tare da faduwa a kasa tana birgima da ihu tana yaga kayan jikinta sai da ta cire kome ya dauke kanshi ya nufi dakinshi, juyawar da zai yi ya hangota saman rufin dakin, daukar bargon yayi kamar me yin wani shiri na musamman, kamar yasan target dinta shi zata fadowa yayi maza ya tareta, tare da buga ta da kasa ya murde a cikin bargo ya daureta tam, kasancewar tsirara take, yasa shi maza ya ja bedsheet gadon ta dauka ya shiga yaga shi cikin wani irin sauri, ya shiga daurawa a jikin window dakin, kafin wani lokaci ya dawo kanta ya dauketa ya daure ta a jikin window. "Papa!" Ta kira sunanshi. Banza yayi mata ta shiga wanka tare da Alola ya fito, ya saka jallabiya bayan ya kashe wutar dakin,wani abu tayi da bakinta wuta ya kama a dakin, ta fashe da dariya. Tana kanshi daga shi sai gajeren wando. "ka zata zan tafi ne? In tare da ita, Salahudeen ka raya daren nan dani zan barta har abada." Shi kuma za a gayawa kaidin aljanu? Banza yayi da ita ya gafatar da sallah shafa'i da wutir, ya jima yana addu'a, kafin ya kira Aliyyah suka sha waya da Saina da Nuri darling, sannan ya kashe wayar ya dauki pillow ya dawo Falon ya kwanta, yana zikiri har barci ya dauke shi. A can dakin kuwa farar inuwar da ta tsaya a bayan dakin ne ta ratsa bangon dakin ta shigo, d'ago kai tayi tana murmushi, "Hilda fita a jikin Layla!" "Ki fitar dani!" "Zan fitar dake ai!" "Kalya kin san babu ruwanki da ni, ni ba." Shake wuyarta tayi ai kuwa sai ga bak'ar hayaki na fita daga bakin Layla tare da tari, kamar a cikin mafarki yaji tarinta. Shafa kanta Kalya tayi tana fadin. "Kiyi hakuri, ki bi kome a hankali." Turo kofar Maina yayi ta koma jikin bango ta makale, kunna wutar dakin yayi ya ga ta koma jikin bango ta makale, kanta a sunkuye kuka ya kwace mata, tsura mata idanu yayi yana kallon yadda take kuka, a hankali ya taka tare da kunce hannunta, sannan ya bude wardrobe inshi ya dauko riga t-shirt sabo fil ya cilla mata, ya nufi kofa zai fita y ce mata. "Ki kwanta!" Har ya ja kofa ya tuna bata ci kome ba,nufar busashen kitchen dinsu na yayi ya ga ba kome tunda ba zama yake ba, fita yayi zuwa bangaren Ummimi, yaga yadda hankalin kowa yake tashe, ana nimanta. Y bude baki yayi magana bawan Allah nan ya share tare da nufar hanyar kitchen ya ha a abinci don tea ne sai soyayyen kwai, ya fito abin shi, "Bro ko ka ga Layla ba a ganta ba" "Ai!" Ya fa a yana barin parlourn yadda yayi maganar yasa Salahudeen ya cewa Ummimi. "Kunga sai da safe!" Ya bar gidan domin a daren aka kira shi. Shi kawai jikinshi ya bashi duk inda aka yi yarinyar tana tare da Maina, kuma amsar da ya bada ya ara tabbata mishi zarginsa. Lokacin da ya shiga dakin, ya samu tana nan inda ya barta. Ajiye mata abincin yayi ya na fa in. "Ni bana magana biyu." Yana fadar haka ya ajiye ya fita daga dakin, bai kuma bin ta kanta ba ya nufi parlourn ya kwanta. Kamar wacce aka kwashe kayan cikinta haka take ji, haba haba ta cinye ta saka rigar t kwanta bayan ta wanke bakinta, barci me nauyi yayi gaba da ita. Da asuban fari ya farka, y nufi masallacin masarautar, gulma da son labarin ya kara armashi Salahudeen da Ammar don tun daren jiya Salahudeen ya turawa Ammar cigiyarta da asuba nan ya gani koda ta kira shi sai ya ce mishi. "Hmm ina tunanin tana wurin shi!" A matu ar rud'e ya ce "what? Maina? Kai karya ne." Shi ne dalilin da kowannensu y bar masallacin unguwarshi ya tawo palace sallah, tunda yaga sun shigo one by one ya fahimci gulma ya kawo su, suna nan aka yi sallah asuba sai kallonshi Ammar yake yana hango yadda ya yaudare shi, tow meye nufinshi? Haka akayi sallah, Salahudeen yaki yarda su hadu da Maina, don yasan sai ya mishi fada ko kallon banza, da gayya yaki fitowa har sai da gari ya fara sha, sannan ya mike ya fita Ammar ta biyo bayanshi. "Kasungurmin munafuki,. Meye alakarka da ita?" Banza yayi mishi yana zikirin safe, sai da suka isa angarenshi ya bude kofa zai shiga Maina ya juya tare da watsa mishi kallon banza. "Idan kaso idanunka su fado kasa, sai na leka ta." "Allah ya baka sa'a!" Ya fa a yana tura kanshi, "A sanina ban tab'a boye maka kome nawa ba, asalima rayuwata babu abun da nake boye maka, ashe kai.ba haka ba ne." Tabbas Ammar yayi gaskiya sai ya tsinci kanshi da bude mishi kofar ya shiga. Shima ya bi bayanshi,a falon suka samu tana barci. Zai magana Maina ya saka hannu a bakinshi. Bin bayan Maina yayi har dakin motsa jiki. "Me yasa ka ajiyeta anan?" "Bata da lafiya, idan ta shiga mutane zata iya zama cutarwa a gare su." Ya fa a yana kwabe rigarshi, shiga kasar karfe yana d'agawa. "Tun yaushe haka ya fara?" "Tun lokacin da Hamidah ta bawa Hassanah kyautar akwatin maciji." A rud'e Ammar ya gyara zama yana jiran karin haske. Nan ya gayawa nishin ka an daga abin da ya faru, kallon Maina yake
Chapter 48 · 0% Book details