← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 115

Sashe 4

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayi karanci ba." "Amma me yasa kika samar min da marasa tarbiyya?" Cikin tsannanin kad'uwa da tashin hankali. "Laifina ne na kasancewa tsayuwa akan Yaranta, shi yasa tarbiyyar ya samu na kasu, ayi min afwa." "Afwa? Tow muje ki bata hakuri idan kuma ta ki amincewa ba zan lamunci b'acin ran Mahaifiyata ba." Daga haka ya mike, babu musu ta bi bayanshi. Don ya wulantatta a gaban bayi da barori, ya wuce da ita ta babbar kofa, tana bin shi tana kuka yadda zaka san ya shirya hakan. Abraham da yake tsaye tare da karfin maza, suna kokuwa ya ga tana bin bayan Mahaifinsu, takaici ya cika shi. Cikin wani irin gudu ua falfala tare da shan gabanta. "Ba zaki bishi kina kuka ba." A fusace King AbdulMutallab ya juya yana kallon Abraham." "Kai!" Juyawa yayi yana kallonshi. "Muje ki shirya ki je can amma ba zaki a haka ana miki kallon kaskanci ba." "Abraham ina wasa da kai ne." "Wai meye nayi da nayi wasa da kai? Gaya min haka zan cigaba da ganin kana wulakanta kowa sobada wancan witch woman din? Muje Maman Maina." Ya tasata a gaba. Duk da yana jin haushin saboda ita aka haife shi a dan baiwa but baya ganin dacewa a saka mace irinta a gaban jama'a tana kuka. "Guard ku kama min dan iska." Haka Security da Dogarai suka kama shi, shi kuma ya wuce da Princess Khamilah, tare da jin a ranshi ba a haifi wanda ya isa ya hana shi yadda yayi niyya ba, har apartment din Queen Hamidah ya kai Princess Khamilah, ta zube a gaba Queen Hamidah. "Don Allah kiyi hakuri, wallahi ban san haka zai faru ba." "Kin san ina son Maina ya haifi Namiji? Zan yi hakuri amma sai kin saka shi ya kara aure idan ma ba zai kara ba, ya tabbatar ya ajiye Kwarkwarah." "In sha Allah, zan saka shi yayi matukar zaki huce." Wannan maganar ya batawa Queen Hamidah rai, wato yanzu ta kara yarda da cewa Maina Uwarshi ke daure mishi gindi,. Cikin hasala ta ce mata. "Kuma wallahi idan bai yi yadda muke so ba, bakinciki da b'acin rai shi ne zaki gani." "Na amince!" "Yan iskan Yara marasa tarbiyya, har nan suka zo suka tsinka min mutuncina." (Dama ba shine dake ba Dowager Hamidah) tozarci da cin mutuncin da suka yiwa Ummimi Allah ya ka ai ya sani, amma bata ce uffan ba sai kuka koda ta koma bangarenta, concubine Hidayah ta samu ta coge mata. "Bana ciki da munafunci, zaki saka a rufe min d'a dayan da na mallaka zaki janyo mishi masifa." "Kiyi hakuri, zai fito an jima!" Inji Princess Khamilah. "Dalla yi min shiru keda baki da bambanci, da baiwa." "Eh bata da bambanci da baiwa, shi yasa bakinciki yake damunki har abada Ummimi ita ce next queen Dowager. " Inji Bahiyyah da ta fito tana had'e rai, masifar Bahiyyah ya wuce tunanin mutane, domin idan ta fara ko King AbdulMutallab ne a gabanta baya sawa tayi shiru. Ita dai Khamilah ta haifi yara ne, amma babu wanda ya dauko tsoronta da ruwan cikinta, dukkansu kamar wasu mayunwartan zakuna, tow ai dole su zama mafadata, tunda yadda aka mai da mahaifiyarsu kamar wata sauna kowa yana da damar cin mutuncinta, ya kwana lafiya. "Ke har kina da bakin magana? Gaya min me zai saka ba zan yi magana ba, kin san yadda nake " "Idan kin yi zuciya kiyi aure mana" "Dariya tayi sannan ta ce mata. " "Ai lokaci ne, idan kin isa ki bawa d'anki sarautar Baihak." Wannan maganar tayiwa Concubine Hidayah ciwo. "Ke!" "Kasa da murya ko na saka a karannuka su fitar min dake waje." Ta fada a fusace, da sauri ta fita. "Zaku gani wallahi zaku gani." Juyawar da zata yi, suka yi karo da Haisam. "Me zasu gani?" "Bani hanya na wuce!" "An sake miki d'anki, kada na kuma ganin kafarki a nan bangaren." "Kai.." yadda ya zuba mata idanun shi masu kama da ta mage, yasa tayi hanyar waje. Ya shiga cikin gidan, "Ummi zan bi Ya Maina Scotland kema ki shirya mu tafi!" "Kamar ya zai tafi?" "Eh zai tafi mana, farauta rayuwarshi ake duk da bai gaya min ba, amma wannan shine bari na uku da Aliyah tayi." "Kuma ba zata yi b'ari don Allah ba, sai a daurawa wasu can? Don Allah kace kada ya tafi kira min shi a waya." "Kina sonmu kike zaune ake wulakanta ki, har ga Allah wannan ba yi ba ne Ummimi kawai ki bar shi ya tafi."inji Bahiyyah, ta fa a tana barin wurin, "Haisam zan je naga Aliyah." "Ba Aliyah ke muhimmanci ba, Ya Maina ya dace ki fara gani, muje na kai ki." Tun da suka bar masarautar, kuwa gidan shi suka wuce, yaje yayi wanka ya sauya kayanshi tsaf sannan ya shiga dakin Yaran suka shiga hada kayansu. Yana gama hada kayan yaran, ya wuce abin dakin Aliyah itama ya hada mata kayanta, aka shiga fita da shi yana kara jin ba zai kuma dawowa Baihak ba, domin ba zai dauki renin hankalin da aka mishi ba, yana cikin had'a wasu takardun Princess Khamilah ta shigo office din shi da yake cikin gidan. "Tafiya zaka yi Maina?" "Taya zan zauna a cigaba da kashe min Yarana da matata take dauke dasu? Na sha gaya miki akwai abu a cikin masarautar nan baki yarda ba, Ummimi yau na bude baki na gaya miki, ba zan zauna ba ina son matata kuma ina son Yarana." "Tow Maina ina hakuri ne domin ku." Tunda ya fadi haka bai kuma cewa cikanki ba, haka ya masifar d'aga mata hankali. Ita kanta tasan ba zai kuma magana ba, sai dai a yadda ta lura da Maina zuwa yanzu kyamar mahaifinshi da Baihak ya kara cika ranshi. Idan ta tilasta shi bata mishi adalci ba, shima yana wannan yunkurin ne domin Yaranshi da Matarshi ashe kuwa dole ta mara mishi baya. "Allah ya kiyayye hanya ya baka abin da ka fita nima, ya shirya maka gabanka da bayanka. Idan ka tafi zamu yi magana da kai ta waya." "Shi kenan!" Wayar shi da tayi kara, ya dauka a hankali ya ce. "Ok" daga nan suka fito, wucewa suka yi zuwa airport bayan an turo Aliyah a gadon marasa lafiya, suka wuce da ita cikin private jet din, rungume juna suka yi, da yan uwanshi. "Dan iska, ka bani tsoro na sha jin labarin jarumai amma kai dodonsu ne kai." Murmushi yayi yana fa in. "Tow namamajo!" Ha e rai Ammar yayi yana fa in. "eh nafi karfin mace daya, sai dai biyar na gaya maka, dan iska Dan daudu, Aliyah tana hakuri ga namiji har namiji amma dan iska bai da amfani!" Kallon Yaran d suke d'agawa Princess Khamilah hannu Maina yayi cikin basarwa da iya caka magana ya ce mishi. "Hala wa ancan toddlers din, a ruwan gidana ta sha." "Kut wallahi baka da mutunci! Waye ya sani." Da haka suka yi sallama. Wadaguwada. A gaban Malamin majami'a suke, ita da Yan koranta. Tata da Yu'isan da Ambi, ita kuma tana karanto yadda zata tsara Malamin majami'a. Shiru tayi tasan a duniya babu abinda zai saka Malamin majami'a yarda da kudirinta. Don haka ta mike ta fara tsalle tana faduwa, tana ihu can ta fara shure-shure. Ai kuwa hankalin Malamin majami'a ya tashi. Mikewa yana fa in Uwargijiya ki kawo min auki, yadda ya tashi zai nufeta Yu'isan ya wurga mishi bawon ayaba, ai kuwa da tsantsi ya kwashesa ji kake kummmmmm,ya zube can da sharbeben tumbi. Tashi tayi tana murmushi. "Yau dai kome yazo da sauki." "Ina fa sauki wancan me ciki uwa na tsohon kwado!" "Tow me zamu auka!" Inji Tata, girgiza kai tayi tana kallon gunkin Wagaduwada. "Muje yau ba zamu dauki kome ba." Fita tayi tana jin wani nishadi a ranta, samun dandazon yan mata tayi sun tsaya suna fa a, anyi rabon fadar yaki karewa, juywa tayi ta wuce wani hanya ta kamo koren maciji, sai da tazo wurinsu. Ta shafa kanshi. "Bance ka ciji kowa ba, kawai ka fasa min taronsu." A hankali ta ajiye shi, da wani bala'in gudu ya nufi yan matan, ya kuwa wuce ta tsakanin kafarsu, ya shiga tsakiyar masu damben ya mike tsaye , sai ya kalli wannan ya kalli wannan can ya fasa kanshi........ #Tuesday #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu FREE BOOK 11/6/2024 08:03pm ___________________2 "Wayyo ku cire min kaikayi ba zan kuma ba." Ta fa a tana ihu da dukkannin muryanta. "Ba me cire miki tunda hatsabibancinki har yanzu bai gaya miki gaskiya ba." Inji Tirsi da ta zuba mata rankwashi. "Wayyo dakwalwata, wayyo kaikayi." Ihun da take yasa Tsohuwa Jamimah ta fito daga dakin Ibada, ta hango yadda Layla take birgima da ihu, nuna mata sandar tsafinta tayi, kamar daukewar ruwan sama haka kaikayin ya tsaya cak. Ware idanu tayi wuli-wuli, tana kallon yadda ta wargaza falon mikewa tayi tana kai hannunta baya. "Hmmm Wagaduwada ta huci zuciyarki!" Ta fa a a aramin murya. Yadda tayi ta saka hannu a cikinta tare da sunkuyar da kai. Kasa asa tayi da idanu tana kallon Sanaya da Tirsi da suka zuba mata idanu. "Haeda !" Da sauri wata mata da ba zata wuce shekaru talatin da bakwai a duniya ta fito, daga wani daki. "Wuce da ita kada ta kuma fitowa sai ranar TARYA" "An gama ranki shi da e !" Inji Haeda. Da sauri Layla ta d'ago kai. "Kaka Jami wannan ba adalci ba ne, wannan son kai ne." Inji Layla tana kuk da ihu. "Na rantse da Wagaduwada ba zan kuma ba, ni dai ku kyale ni." Ta fa a tana ihu, domin tasan matu ar aka sakata isolation tabbas ba zata kuma ganin koda hasken rana ne, ba zata kuma ganin koda hasken wata bare rana. "Kaka Jami ba zan kuma, Tirsi ku ce kada ta rufe ni." Haka haeda ta shige da ita dakin, sai lokacin tsohuwa Jamimah ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tana lumshe idanu. "Yar uwa lamarin yarinyan nan" "Tirsi!" "Kiyi hakuri amma gaskiya daya ne, kuma dole ne na gaya miki." "Tirsi me kike son nayi?" Ta fa a
Chapter 4 · 0% Book details