← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 115

Sashe 101

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jira Aliyyah take ya fita ta nufi Layla da ta bata baya. "Kul ki tsaya akan kalamanki kada ki sake ki tako inda nake ko kuma na baki kyautar da ba'a tab'a baki irinta ba." "Mum!!" Sanah ta fasa ihu, Wanda ba kome ba ne sai juya kafaffunta da aka yi yana kallon sama fuskarta na kasa. "Nuri na!" "Na'am Mamyna!" "Cigaba da shan juice inki!" Ta juya ga Aliyyah. "Ai nasan ba gwaiba ya kawo ku ba, fitina ya kawo ku. Ko shi Maina bai da ikon dakatar da ni balle ke wacce bata san darajar kanta ba. Zuwa yanzu ya dace ki san darajar kanki da darajar da Mijinki yake baki. " "Ki kyale min Y'ata tunda baki haifa ba tukun baki san darajarsu ba. Balle har ki san zafinsu abin da kika sani miji ya zuba miki wutsiyar shi. Ban da ma Namiji da wahalar da kai me zai yi da g**dinki! Shi da babbar mace ma ta kasa mishi!" "Omo!" Layla ta rufe kunnen Nuri tana zare idanu bayan ta ga zuwan Maina bakin kofar. "Idan zaki yi zancen kishi ki daina sake manyan magana zaki lalata tarbiyyar da kika jima kina ginawa ne, ko Sultan dina?" Ranshi yayi masifar b'aci jin irin kalmar da Aliyyah take fa a a gaban Yaranta, "Me ya faru?" "Rashin kunya zata min na rataye ta, domin ina tsoron kada su min laifi nayi magana kace ban san zafin haihuwa ba. Koda yake ko baka gaya min ba matarka ta yanko maganar da zai lalata goben Yaranta." Ta juya tare da tafa hannunta sai ga shi an sauke Sanah. Fashewa da kuka yarinyar tayi. "Kana gani!" Wani dukar table din kitchen din yayi sai da suka ja da baya. "Daga yau kada na kara ganin waninku ya shiga harkokin Layla!" "Lallai baka son zaman lafiya a cikin gidan nan!" "Kika ce haka? Tow wallahi duk abin da ya faru da ku babu abin da ya dame ni!" Daga haka ya cigaba da aikinsa yana gamawa ya zuba musu ya wuce da na Layla dakin ya samu tana kwance. Tashinta yayi ya zuba mata abincin ta ci sosai. Sannan yaja hannunta zuwa ban aki wanka suka yi cike da so da kauna. Kafin suka fito waje yana jin wani nishadi. Daga nan ya bar gidan, kwanciya Layla tayi har ta fara barci aka tab'ata bude idanu tayi cikin natsuwa . "Ba fa barci zaki yi ba. Yanzu zaki fara abin da ya kawo ki." "Kamar ya? Kuma wacece ke?" Murmushi matar tayi mata, sannan ta ce mata. "Zaki san wacce ni, amma ba yanzu ba Tirsila ce ta kiraki don haka ke kuma ki amsa kiran da fara aiki akan Hamidah domin tana shirin bautar da Mijinki bayan ta gama cin moriyar Ubanshi kada ki bari haka ya faru." "Taya zan yi haka?" "Zaki iya ki fara!" Daga haka matar ta b'ace. Tashi tayi ta rufe kofar sannan ta nufi bangon dakin ta dafa, tare da motsa bakinta idanunta rufe, sai gata a dakin Queen Hamidah, wacce take parlour tana shirya sharri ita da Tirsila. "Na kirata tun jiya ban san me ya hana bayyanarta ba amma tabbas zata zo domin na kirata." "Hmm kina ganin zata zo? Ita nake son kamawa tunda na fahimci Maina ya shiga hannuna." "Kalya ki saka rundunar marasa jin magana su zame minsu!" "An gama Uwar dakina." Haka kuwa ka ayi, suna cikin tattaunawa suka ji an rufe su da wani irin bugu daga sama har kasa. ayi hakuri kun ji ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` #Mai_Dambu LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________69 Zuwa yanzu fitinar Layla kamar kara mata kaimi ake, domin wani irin azabar ishirwa fa a take ji, haka kawai ta saka su Hamidah suka yi laushi bayan an musu azazzaben dukar da ko da iyayensu suna raye basu tab'a musu ba, sai da jikinsu yayi tsami don azaba, sannan ta koma dakinta ta zauna tana haki yanxu komi kashin b'acin rai saka ta haki yake balle kuma tayi wani jijjiga me karfi. Haka yasa tun da ta dawo ta kwanta tana nishi, sai dai bayan ta kwanta har barci ya fara aukarta sai ta fara kamar mafarki kamar ido biyu wai ga Aliyyah da Sanah sun dauko abu zasu buga mata, a barcin ko mafarki ne ta kare kanta tare da fa in. "Kalya kafe su!" Ai kuwa suka kafe a wurin, ita ta zata barci ne ko mafarki ne ta cigaba da barcinta, har tana juyawa ta kalle su a mafarkin nan kuwa a zahiri ne domin kuwa sun biyo ta ne daukar fansa don Aliyyah tayi alkawarin ba zata tab'a barin Layla ta zauna ba, sai dai ita kanta bata san yadda zata yi da Layla ba. Kusan awa uku suna tsaye a wurin har sun kasa motsawa ga idanunsu na motsawa amma gangan jikinsu ya gagara motsi, a haka Maina ya shigo ya gansu Aliyyah dauke da wani katako sai Sanah da take dauke da bulala. Kallo daya ya musu ya dauke kai tabbas ban da yana da uzuri da ya sallame Aliyyah amma yanzu bata gabanshi. Malik da Auta ne a gabanshi sai Queen Hamidah. Wuce su yayi ya zauna a bakin gadon yana shafa kan Layla. "Tashi please!" Ya fada yana shafa kanta. Bude idanu tayi tana fa in. "Sultan my cowboy!" "Wa annan zaki kyale!" Ya dan juya ka an. "Su waye?" Ta fada tana mikewa daga kwance. Ta leka su dauke da kayan aiki. "Waw dama da gaske ne ba mafarki nayi ba?" Ta fada tana kallon Maina, "Amma kasan rayuwata tana cikin hatsari a gidanka ko?" "Yes i know, amma ki bar min kome a hannuna." Girgiza kai tayi tana murmushi ta ce mishi. "Idan na kyale su gobe ma haka zasu kara min!" Rike hannunta yayi cikin rarrashi ya ce mata. "Please Layla!" Zare hannunta tayi tana fa in. "Sai dai kayi hakuri;" zuwa yanzu ta koyi wani shegen taurin kai. Don haka ta dauke kai tana fa in. ""Kayi hakuri!" Tayi wani alama da hannunta take suka fara motsa, sai dai Sanah faduwa tayi ita tana wani irin girgiza. "Layla!" Aliyyah ta kira sunanta da arfi. "Meye?" Tambaye ta. "Ina ga idan ma barki da wannan aikin ya isa ya saka ki manta da ina nan!" Damke hannunta Maina yayi, wani irin zare idanu tayi ta ce mishi. "Ka daskare!" Ai kuwa ya fara daskarewa. dakyar ya saka hannunshi a gefen fuskarta. "Ki tuna ina sonki!" "Layla kada kiyi haka yana sonki!" "Tow sai me Kalya!" Cire hannunta tayi a fuskarshi tana juya mishi baya, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ta sake shi,"Layla!" "Ka tafi bana son magana!" "Ki!" "Nace ka tafi!" Ta mike tana me wuce ban aki, ta rufe kofar ban dakin da karfi tare da fashewa da kuka ta zauna a wurin haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba, zuwa yanzu yasan yana cikin tsaka me wuya, ga Layla ga Sanah ga kuma Hamidah. Haka ya tashi jikin shi a mace kasancewar sanyin ya fara ratsa shi, ya nufi bangaren Aliyyah da ta ja Yarta suka fita, koda ya shiga ya samu Nuri da Banafsha suna barci, gabanshi ne ya kara faduwa ina Aliyyah ta kai Sanah? Da sauri ya fita zuwa waje anan ya hango suna nufar bangaren Hamidah. Da wani irin gudu ya nufi bangaren amma ina sun shiga parlour babu kowa sake shiga tayi ta hango Hamidah a kwance tana nishi wani irin ihu ya fasa da ya ja hankalin kowa zuwa cikin parlour. Har shi Maina da ya iso a lokacin. "Me ya faru?" Ya tambayi masu tsaron kofar. "Ranka ya dade bamu sani ba , mu ma ihun Gimbiya ya ja hankalin mu." Tashin hankali wanda ba a saka mishi rana. Ai akan lokaci suka nufi asibiti da su baki aya. Sanaya jin shiru yasa ta zuwa masarautar bata ga tirsila ba. Koda ta ji abin da aka gaya mata. "Ina bangaren Maina ya e?" Aka mata jagora har zuwa bangaren. Layla tana zaune a tsakiyar Yara ta ji sallamarta. Bata d'ago kai ba ta ce mata. "Barka da zuwa Sanaya, ya kwana biyu?" "Ba shi ya kawo ni ba, me yasa?" "Yana da kyau ki nime alfarma ko? Sannan ki hadiye kowacce kalma da zata fito bakinki domin dai ba zan lamunci kazaman tambaya ya fito daga bakinki ba. Yarana suna jinki." Duk wannan maganar da Layla take bata kalli Sanaya ba kanta yana kasa. "Layla ki d'ago kai ki kalle ni!" "Tab ba zan kalle ki ba, balle har na ji tausayinki domin babu wanda ya isa dakatar dani!" Zubewa Sanaya tayi akan gwiwarta hawaye na zuba mata. "Ki yafewa Tirsila nasan tayi kuskure!" Sai a sannan ta d'ago idanunta da suka yi jajjur ta ce mata. "Na gaya miki, ki tafi ki nemi izinin ganina kada kuma ki kara zuwa min da zancen Tirsila!" Kuka ta fashe da shi tana me rarrafawa gaban Layla. "Kiyi hakuri nasan an miki laifi sai dai." "Tashi ki tafi kin ga na dauke hankalinsu ne daga gare mu tashi ki je kawai!" "Layla!" Girgiza kai tayi tana nuna mata hanya. "Layla nasan me suke shiryawa idan kika yafe mata zan lalata kome!" "Na rigaki sani domin sun tashi mataccenn ruhi domin ya ga bayana!" "Eh haka ne amma ko yafe mana!" " zan yi nazarin haka!" Da Sanaya ta isheta ta ce. "Kalya ki fita da ita!" Cak Kalya ta dauki Sanaya tayi waje da ita. "Amma Layla!" Dauke kai tayi, sai bayan tafiyar Sanaya taji zuciyarta tayi sanyi domin zuwa yanzu Maina ne a gefenta bayan nan babu sai yanzu da Sanaya ta bayyana kanta. A can asibitin kuwa sai da Queen Hamidah ta samu targade a hannunta, Tirsila ce dai da sauki domin tana farkawa tayi wasu yan dabarun tsafi tuni tayi ta aman jinin da Aljanu suka tara mata. Sannan ta koma ta kwanta. Queen Hamidah ce bata farka ba amma taci uban duka. - Sanah kuwa bata ma san waye akanta ba, don haka abin yayiwa Maina yawa, don haka da ya samu Hamidah ta fada wannan matsalar sai
Chapter 101 · 0% Book details