← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 115

Sashe 5

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana kallon Sanaya da take tsaye. "Tun haihuwarsu ya dace ki gaya min makomar addaranta!" Ta juya Sanaya. " Na ce ban ga kome a addaran a kansu ba." Kurawa Sanaya idanu tayi tana jin wani abu me d'aci yana ratsa zuciyarta. "Tabbas yar uwa, kina boye min wani abu. addaran Sanaya ce zama abu biyu lokaci" "Idan kuma ba haka ba ne fa?" Tsohuwa Jamimah ta daka mata tsawa. "Wannan ya zama kashedina dake na arshe." "Amma kuwa wannan son kai ne!" Tirsi ta fada da karfi. "Ni ce nake son kan?" "Tabbas rayuwar nan akwai son kai, tun daga shudewar abilarmu, har yau babu wanda ya k yanke hukuncin rad'awa dan shi suna sai ke, nasan kina kokarin boye min wani abu, tun bakar dare bayyanar." "Tirsi ni kike gayawa magana!" Inji Kaka Jami, cikin bakinciki da takaici Tirsi ta ce mata. "Kin san Sanaya an haifeta ta hanya me tsarki, iyayen Sanaya sadaukarwa suka yi ga Uwargijiya. Sannan albarka yana lullube ga yaran da aka haifa bayan an sadaukar da rayukan iyayensu, tun ranar da aka haifeta baki gaya min kome akan addaranta ba, ni cikinmu aya zuriar wancan yarinyar da kika fifita saboda duniya suka bar duniyarmu. Nayi imani da cewa Uwargijiya ba zata yafe miki ba, kuma zan bi dare da rana, zafi da sanyi, sai na binciko abin da kike boyewa akan Sanaya da Layla " ta juya ta bar gidan tana zubda hawayen bakinciki da b'acin rai. Bin bayanta Sanaya tayi bayan ta kalli Kaka Jami, sannan ta juya ta fita tana jin wani irin haushin Layla domin duk lokacin da Kaka Jami da Kaka Tirsi suka yi fa a, akan Layla ce. Tun fil azal tayi ta kaf-kaf da lamarin sadaukarwan nan, gashi nan ta rasa iyayen Yarinyar da babu ruwanta don zuriyarta su rike tsawon rai na tsawon zamani biyar. Sai ta mayar da Sanaya abin alfahari, sai ta sa al'umma sun kaunaceta shi yasa take kara tsundumata harkan ibada da ilimin Bokanci da tsafi koda zata mutu ba zata tab'a sarewa ba, alle a kai ga ta fa Ajiyar zuciya kaka Jami tayi tana jin muryan Layla har lokacin ihu take, kuma ta sani ba zata tab'a daina ihun nan ba. Sai dai killace Layla kamar shi zai saka ta shiga hankalinta, har zuwa ranar bikin TARYA, bikin tarya shagali ne da akewa Uwargijiya duk bayan shekara biyar, tun ana gobe bikin xa a wanke majami'an, sannan a gyara shi, za a tsananta tsaro da ibada a kwanakin ana yawan addu'a da hadaya. Sannan malaman Majami'an da sauran manyan gari, za su shiga gaba wurin sadaukar da dabbobi awakai. Fari da baki, akwai za a debi jinin a kawowa Kaka Jami tayi addu'a a kai, sannan a bi kusurwan Wagaduwada ana zuba jinin dabbobin, bakar akuya tana daukar ranar bakinciki ga al'ummar garin. Farar akuya tana nufin ranar da aka haifi Wagaduwada. Idan an gama xa'a koma majami'a ayi shagalin bikin tare da saka yan mata da yara rawa a gaban jama'a tare da shigar Wagaduwada da kuma yanayin ya in da aka yi. Daga nan za'a saka mutane zuwa yiwa Wagaduwada addu'a da rokon farinciki ga kan farin akuya. Ana yi wannan bikin duk shekara, sai dai a wannan karon malaman Majami'an da kansu, suka bukaci Layla tayi shigar Wagaduwada wanda haka bai wa Tirsi dadi, domin kai tsaye kaka Jami ta ce musu. "A'a ga Sanaya, ita ce ta dace domin ita ce Tirsi take son zama yanayin Wagaduwada." "Ranki shi da e. An haifi Sanaya a ranar mutuwar Uwargijiya. Ita kuma Layla an haifeta ne a a ranar zagayowar haihuwar Uwargijiya. Haka ya tabbata ma." "Malamin majami'a, a dakatar da saka sunan Layla a duk sha'anin wada." Ta fada tana juyawa, ta bar majami'an da kallon Mamakin abin Tirsi take bin ta, ta jima da sanin haka. Ranar TARYA ba shi ne ranar da aka haifi Sanaya, amma taki biyayya hakan don ta bayyana a wayewan ranar haihuwar Wagaduwada duk wanda aka haifa a wanann dare mai albarka. Yana kasancewar me albarka. Sannan tun bayan mutuwar Hanna da Rihanna, abisa bincike da aka yi aka tabbatar da zaa yi yarinyar da zata samu darajar mutane uku da suka sadaukar da rayuwarsu, Wada, Hanna da Rihanna. Wannan yasa babban burin abilar shine a haifi me baiwa uku. Haka yasa duk wani yaro ko Yarinya da za a haifa, Kaka Jami ake kawowa ta kalle shi ta kuma duba addaran, sai da ba a samu wani me irin wannan baiwar ba. Lokaci da aka haife dake Tirsi tana da matukar son abin duniya, haka yasa tayi ta bincike ta hango cewa idan har ta sake ba zata tab'a samun damar wata ana a cikin kabilar Wada ba, sannan zata kare ayiwa yar uwarta bauta ne, duk da Jamimah tayi arin toshe wasu abubuwan amma ina, haka yasa aka gari Maman Sanaya da Baban sanaya sun sadaukar da rayuwarsu ga Wada. Duk iyayen da suka yo haka, tabbas suna bukatar Yarsu ta zama waliyiya. Har zuwa mutuwarsu Tirsi bata yi nadama ba, sai dai Kaka Jami ta gaya mata. Tana kusanta kanta ga halaka amma bata ji ba, domin kaka jami bata da d'a sai dai renon marayu. Izuwa yanzu Layla ita ce yarinyar da bata ji maganar kowa, ga jan rigima kamar wata yar bala'i. Sannan duk fitinarta yana karewa ne akan kayan mutane, domin abokanta suna ce mata basu ci abinci ba, zata shiga sane da sata wa mutane. Wannan yana daga cikin abinda yake mata dad'i, sannan a garin ma iyayen Yara sun hana Yaransu mu'amala da ita, domin gani suke ita tsinuwa ce a gare su. ---- Cikin kuka da gajiya ta ce. "Haeda zan yi fitsari!" Juyawa haeda tayi ta ce mata. "Shiga ban daki." "Ni dai ban zan yi ba a ciki ba." "Tow cigaba da zama" "Haeda zan sha ruwa." "Gashi nan kusa da ke!" "Ni ki zo ki bani!" Banza tayi da ita, ai kuwa ta fashe da kukan shagwab'a. "Ni dai ku kyale ni! Zan tafi wasa na ne. Wayyo Uwargijiya ki kawo min auki." Turo kofar dakin Kaka Jami tayi, ta hangota zaune. "Sannu da shigowa!" Inji Haeda ta fada tana mikewa. "Yawwa Haeda." Shigowa bakin gadon Kaka Jami tayi. Ta zauna tana kallon Layla da take kuka kuma taki kallon kakan. "Jeki Haeda!" "Tow ranki shi da e!" Ta fita daga dakin. Kallon kofar kaka Jami tayi ta nuna sandar tsafinta, a hankali kofar dakin aka gine shi da wasu irin duwatsun tsaro na tsafi. Kallon gabanta tayi ta sake nuna sanda wata kofa ce ta bude, a hankali ta riko hannun Layla suka fita zuwa wani lambu. Wanda yake cike da wasu mutane masu sanye da fararen kaya. Sai gaida Kaka Jami suke, har suka isa gaban wata mata. "Jamimah yarinyar ta girma!" Zubewa kaka Jami tayi tana fa in. "Godiya nake shugabana." Da wutsiyar idanu take kallon ilahirin lambun. "Layla gaishe su." Hannunta ta kai tare da zubewa kasa ta ce. "Ina Godiya Shugaban Kaka Jami." Mangareta kaka Jami tayi ta fa i. "Kaka!" "Shiiii!" Murmushi farar rauhaniyar tayi. "Duk da kasancewarta bil adama, sai dai har yanzu bakar inuwar Hilda tana bibiyarta." D'agowa Kaka Jami tayi tana kallon Layla. "Shugabana, Hilda fa!" "Kwarai da gaske!" A rud'e bakin Kaka Jami yana rawa ta ce mata. "Ina tsoron." Hilda ba zata iya shigar ta ba, sai dai ki san yadda zaki dakatar da Tirsi domin kuwa dole kome zai faru. Domin abin da ya faru shekaru dari hudu da wani abu zai kuma faruwa. Na gaya miki dole kiyi shiru akan kaddaransu. Haihuwar masu yanayin Hanna da Rihanna ba karamin sha'ani ba ne, a binciken da muka yi mun samu zuri'ar Hanna suna nan a raye, Hilda tana tare da ita, Rihanna ce babu labarin zuriarta. Hakan yasa na gaya miki tun black moon, na ce miki duba addaran kowa ya kare, amma abin da ya faru zai sake faruwa. Abu daya xan gaya miki, koda zaki mutu ki tabbatar kin rufe kofar jikin Layla. Dabi'arta sak da Rihanna tare da Bulma, don haka rufe kofar zai tasirantu ne ta hanyar binne abubuwa masu muhimmanci da idan suka fito zai iya kawo karshen rayuwarta." "Shugabata." "Layla tayi mu Sharaka da Uwargijiya. Ai sai dai kiyi hakuri domin kuwa Laylarki Uwargijiya ce da kanta, kada ki damu ba zata iya kome ba, domin jikinta babu kwarin daukar hasken Uwargijiya." "Ban san yadda zan rufe kofarta ba." "Mayen bumma tarwatsiwatsa!" Inji farar matar ta watsawa Layla wani irin koren ruwa, take ta yanki jiki ta fadi a wurin. "An gama babu abinda zai faru! Zasu d'auketa."sauka daga kujeran matar tayi tare da nufar Layla da take kwance, ta tab'a kanta, a hankali tana karantar Layla din. Da sauri ta cire hannunta, wanda yake fitar da hayaki. "Mayen barba!" Ta kuma rufe idanunta. Da sauri ta cire hannunta. "Jamimah! Layla shekarunta sha biyu ko?" "Eh shugabata." Hannun da baya hayaki ta saka a bakinta, tare da zubda hawayen. "Taya muka yi sake?" A rud'e kaka Jami ta ce. "Shugabata wani abu ya faru ne?" "Zai faru dai! Ki nisanta Layla da Wagaduwada, domin jini zai zuba a sanadinta. Amma ba ita ke da hakkin zubda shi ba. Saura wasu lokuta na rayuwarta zasu cika shine hakan zai faru, ku tafi!" Rauhaniyar ta fa a, juyawa kaka Jami tayi maza ta dauki sandarta, wasu daga cikin hadimar fadar rauhanan suka futa da su, tana tsaye, sai ga Tirsi da Sanaya. Zubewa suka yi cikin tsananin biyayya. "Shugabata, nazo da kuka na ne, Jamimah taki gaya min kome akan Sanaya." "Kina sane ba zan ci amana ba, mu magana daya muke yi. Ki maida jikarki!" Ta fa a tana takowa gaban Sanaya, ta dafe kanta, lumshe idanun tayi tana cirewa ta kara kallonta. "Meye burinki Tirsi da zaki dafar da zuciyarta? Me yasa kika ginata cikin kiyayya da hassada? Kina sane da hakan kike bibiyar lamarin yar uwarki. Zaki samu biyan bukata amma zaki yi danasanin lokacin da bai da amfani kunhela kun lala!" Ta nuna musu hanya." Baihak. A yadda yake tafiya cike yake da gajiya, domin tun karfe sha daya suka shiga meeting, sai shida da wani abu suka fito.
Chapter 5 · 0% Book details