Sashe 6
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan shi bodyguard ne hannunsu dauke yake da manyan makamai,sai fadawa masu auke da tsumagiya, ga team in aikinshi da suke take mishi baya. Bude motar aka yi, sakatariyarshi wacce ta kasance mace. Ta ce. "Sir an d'aga meeting din zuwa next, domin mun samu sakon ganawa da Malik." Sai da ya shiga motar, itama ta shiga gabar motar, tana karanto mishi bayanai. Bai ce uffan ba, har suka bar babban bankin Baihak. Gidanshi da yake fin era, wayarshi da yake hannun Sakatariyarshi yayi ara dauka tayi cikin sanyin murya ta ce. "Yes gashi nan ma!" Ta juya tare da mika mishi wayar. "Queen Dowager!" Bude idanu yayi kafin ya lumshe idanunshi. Parking motarshi tayi daga Teemi da drivan suka fita waje, "Maina me yasa ba amsa gayyatatta ba?" Lumshe idanunshi yayi yana budewa. "Maina ba magana da kai nake ba ne?" Nan ma shiru yayi mata,. "Ok nasan inda zan samu amsar bakinka, ashe matarka ciki ne da ita." Nan ma shiru yayi mata, "Maina ni ka mai da yar iska?" Sai lokacin ya ware idanun shi, ya gyara zaman shi zai magana ta ce mishi. "Uwarka Khamila kayiwa." "Me kika ce?" Shiru tayi kafin ta ce. "Ok duk maganar da nayi baka ji ba ne?" "Ina kan hanya ne!" Tunda ya fadi haka tasan sarai kashe wayar zai yi, don haka ta ce mishi. "Baka ji Ayrah tayi rashin lafiya ba ne?" Kashe wyaar yayi ya mai da kanshi jikin motar yana sauke ajiyar zuciya. A wajen motar kallon agogon hannunta tayi, sannan ta bude motar ganin yadda yake kwance ta ce mishi. "zamu iya shigowa!" Da hannu ya mata alama, ta fito tana buga motar, driven suka shiga. Daukar wayar tayi ta rike tana duba kan wayar. Haisam ne ya kira ta auka. "Prince Auta!" Ta fa a. "Ina Yayana?" "Kayi hakuri ya fito a gajiye daga meeting ne, kuma daga nan gida zamu nufa domin Princess Aliyah bata da lafiya." "Ok ki ce mishi, idan ya huta ya shigo Palace don Allah, Ummimi tana son ganshin." Yana jinsu, har ta ajiye wayar tana me juyawa kad'an. Ta kalli cutie face din shi, sannan ta juya tana me sake murmushi. Yau shekaru goma kenan tana aiki da shi, ba wai don niman duniya ba, a'a sai don niman soyayyarshi. Amma ta lura Maina irin mutanen nan ne masu ra'ayin rukau. Sai da suka isa fin era estate, a hankali suka wuce unguwar da yake zaune da iyalinsa. Suna isa Teemi tana fitowa a motar ta bude mishi, a hankali ya zura kafarshi ya fito a nutse, tana gefen shi yayi gaba, ta rufe kofar motar tare da bin bayan shi dauke da briefcase din shi, yadda yake tafiya kamar ba zai taka kasa ba, yana kara haukata Teemi yake, a tsaye yake tafiyar kamar wani mashin yaki, cikakken namiji me cike da sadauki kuma jarumin maza. Yana isa bakin kofar aka bude mishi, karamin murmushi ya sake. "Welcome Papa!" Inji Yaran lokaci guda, daukar yar aramarsu yayi yana fa in. "Nuriyyata." Sannan ya juya idanun shi kan yan matan da suke tsaye cikin girmama. "Sanah, Sainah." "Na'am Papa!" Suka amsa lokaci guda, "Papa ya aiki?" "Alhamdulillahi." Ya furta yana shiga tanfatsetsen falonsu. Haurawa sama suka yi, inda akinsu yake, sai da ya fara wucewa dakin Mahaifiyar Yaran, ya sameta kwance tana shan ice cream. Bai Ajiye roban tayi tare da gyara zamanta tana fa in. "welcome back, Sultan!" Kallonta yake cikin kulawa da tausayin yadda take fama da matsanancin laulayi, "Ya jikin naki?" Ya fa a a hankali. "Lafiya my Sultan." Ajiye Nuriyya yayi yana me zuba hannu a cikin aljuhun wandonshi. "Babu matsalar ko?" "Yes sir!" "Ok Allah ya raba lafiya!" Ya fa a tare da nufar hanyar waje. "Dazun Court lady tazo duba ni." Ha iye yawu yayi kafin ya ce. "Me ta ajiye?" "Sainah ki cewa Amra ta kawo sakon nan." "Ok Maame!" Ta fita can sai gasu tare da wata maid dauke da wani tire da aka lullube shi da golden veil, yana gani zuciyarshi kamar zata buga, budewa yayi tare da rintsa idanunshi. "Waye ya gaya musu you are pregnant?" Yadda yayi maganar a fusace, yasa yaran suka makale jikin juna, kamar zasu yi kuka. "Amra wuce da su akinsu." Tattara yaran tayi bayan ta ajiye tiren, suka fita a hankali ta mike zuwa gabanshi. "Nasan ba zaka yarda ba, amma wallahi I don't know anything, nasan kafin ka fita kun ajiye ni a clinic, amma wallahi ko parent dina ban gaya musu ba." Fita yayi ya bar dakin ranshi yana konewa, yanzu ya fahimci dalilin kiranshi da Dowager Hamidah tayi, ban daki ya wuce ya budewa kanshi ruwa. Idan har wannan shi ne abin da ake bukata dole ya yanke hukuncin da ya dace da rayuwarshi sa iyalinsa. Ba zai cigaba da aukar iskancin wancan tsohuwar mayyar ba. Wannan karon wani abu ya samu cikin Aliyah wallahi sai ta girgiza Baihak Palace da mutanen cikinshi. TARYA Sai da Layla ta kwashe tsawon kwanaki bata fito ba, ranar da za ayi aka bude ta bayan Haeda ta mata wanka da madara, duk da ita kaka Jami bata so wannan abin ba, amma babu yadda ta iya. Itama Layla a angaren ta, yau zata wargaza bikin tarya shi yasa take murna. Wanka aka yi mata duk da tana mitan. "Haka kawai a tube mutumin sindir wai ana mishi wanka, salon ayi ta kallon mutun ganga ba rufi, Haeda idan na fita ba zan kuma yarda ba. Na rantse" Ta fa a tana tura baki. "Hmm!" Haeda ta ce mata, Kayan da aka ciro mata ta gani, har da zinari. "Har da sarka zan saka?" "Eh" Sai da ta shirya tsaf, aka wuce da ita dakin Kaka Jami. Murmushi Kaka tayi tana fa in. "kin yi kyau, zo nan ki zauna." Ta nuna mata wurin zama, zama tayi ta cire abin wuyarta ta saka mata. "Zai kare ki daga duk wani abin ki." Ta riko hannunta suka fita, Kyakyawar fatarta da aka auki tsawon kwanaki ana wanke shi da danyen madarar saniya. Sai wani sheki yake daga kugunta zuwa cinyonta ne rufe da wani zanin saki, saman kirjinta ma haka, an shirya mata jikinta tsaf da kayan k'awa tayi kyau, haeda tabi fuskarta da kwalliya me kyau, ta kawata mata shi yadda kowa zai kalleta as a goddess. Haka suka tafi wurin taron,Sun samu Tirsi tana wajen itama tare da Sanaya wacce taci Uban kwalliya, har inda Kaka Jami take Tirsi ta zo ta gaida ta, sanan ta gaya mata uzurin da ya hanata zuwa. Dake Kaka Jami mace ce adila tace mata."babu kome, ya Sanaya?" "Gata can" ta nuna mata ita, murmushi tayi ta ce mata. "Tayi kyau sosai, duk da Hanna da Rihanna tagwaye ne, sai nake jin kamar an kuma haihuwarsu ne bayan shafe karni hu u. A hankali Tirsi ta kalli Yaran, sun yi kama da juna, yanayinsu daya, sai abin ya matukar dakar zuciyarta. Domin kuwa bata ta a kawowa haka ba, sai da suka yi shigar al'ada. "Mafarkina a sake haihuwar Hanna da Rihanna, sai gashi addara ta saka an haife su a mabanbanta duniya, kuma suna raye a wuri guda. Nayi fatan su zama wasu ababen da Uwargijiya zata yi alfahari da su. " Inji Kaka Jami, bakin Tirsi ne yayi nauyi ta kasa magana, da shirinta tazo nan. Don haka ba zata bari maganar Jamimah yar uwarta yayi tasiri a kanta ba. Suna tsaye aka nemi Layla aka rasa, ba a ganta ba, kuma za a fara addu'a. Ita kuwa Madam Layla can ta bi Abokanta Tata Yu'isan Ambi, suka wuce tare da zama. "Layla ina kika shiga ne?" "Kaka Jami ta rufe ni." "Layla me ta dace muyi?" "So nake kamar yadda kaka Jami ta rufe ni, a tarwatsa taron nan." "Lalala so kike a kashe mu?" "Zaku iya mana, ku kawo kunnenku " Ta rad'a musu dariya suka saka tare da tafawa. "Idan aka yi haka ne za ayi a gaba?" "Zan yi sauran kawai Tata ka kira aljani Tunbala shi zai mana aikin nan!" "Tow an gama" ya fa a bayan ya mike, "Zubarbara Tunbala tunbaba!" Sai ga hayaki kore ya bayyana. Cikin takaici aljanin ya ce. "shugabana me zan maka?" "Wancan bakin akuyar zaka shiga jikinshi, ks tarwatsa tsaron TARYA." Kallon Layla yayi kafin ya ce. "Zaka tab'e idan ka bi na wancan Shaidaniyar." Sannan ya juya yabi iska. "Tata me ya ce?" Ta tambaye shi? Ta tafi, tafawa suka yi suka wuce cikin Majami'an. Kamar da gaske suka shiga addu'a, aka fara da su, kuka da ihu take kai zaka rantse da Allah tayi don bakinciki. "Emeeeeeeeeeee!" Baki aya majami'an ya dauka da kukan akuya, sake kukan akuyan.aka yi ta suka juya. "Uwargijiya ka tsare mu," inji Malamin majami'a. Tsalle akuyan da aka sadaukarwa da shi suka ga yake yana fa in. "laa na mutu na na dawo." "Da gaske ka mutu ka dawo?" "Ga zahiri!" Kafin kace me an shiga gudu sa ture ture ana gudu, kafin su isa kofar an rufe. "Yau rawan na mutu na dawo zan muku," Ai kuwa mutane suka shiga ihu dakyar aka bude kofar duk suka fita, Layla ta samu ta fito, inda aka Ajiye mutumumin Uwargijiya, suka je tare da saka hannu suka kwashe gwala-gwalan uwar gijiyan, tasa Tata da Yu'isan da Ambi, suka gudu ita kuma ta tsaya a gaban Uwargijiyar. Lokacin da mutane hankalinsu ya dawo kan Uwargijiya, suka tawo wurinta. "Ku dakata!" Ta fa a tana juyawa bayan ta wanke fuskarta da jinin akuyan. Cak suka tsaya. Zama tayi ta tankwashe kafarta, kafin ta fara nishi. "Hmmmmmm! Hmmmm!! Hmmmmmm!!!" Idanunta a rufe, can ta bude baki ta ce musu. "Yaku Jama'an Wagaduwada!" Yadda ta kira sunan zai tabbatar maka gaske ba ita ba ce. A wurinsu. "Ku taka rawa sau uku nice nan, manzaniyar Wada!" Ai kuwa suka shiga juyo da rawa. Sake baki tayi tana kallon yadda malaman Majami'an suke rawa da tulelen tumbi, kamar an bawa kwado dakon kaya. " Kai Malamin majami'a wannan rawan da kake Uwar gijiya zata tsine maka albarka, maza sauya rawan nan!" Aikuwa ya shiga juyo kamar an mulmula kwallon giginya akan faranti. "Tirsi ki cire kiyayya da hassada, kina gaban Wagaduwada ce,